AGOLA LITTAFIN NABILA RABI’U ZANGO
LAKABI: NABILAT LADI
LAMBAR WAYA: 08028525263

Agarin Kaduna, a unguwar Sarki, awani katon gida, nashiga domin dauko maku labarin cikin gidan. Alhaji Abba Bala, hamshakin me kudine, yanada mata daya da ya,ya biyu mata, Sunan matarshi Hajiya Zarah, takasance yar garin zariya, diyace agurin Malam Garba da matarshi Asabe, kishiyar mamanta, ce, tana kiranta da inna, Asabe takasance mace me kissa, hakan yasa take zaune da Zarah tamkar ita ta haifeta, babu wanda yasan dalilinta nayin haka, talakawa ne acikin danginsu kaf Zarah ce kadai tayi sa,ar auran me kudi, dalilin haduwarsu kuwa lokacin da Alhaji Abba yaje zariya acikin unguwarsu Zarah, yaziyarci wani abokinshi, ahanyarshi ta dawowa yahadu da Zarah tadawo daga aiken da Innarta tayi mata, lokaci guda yaji yakamu da sonta, ahaka. Bayan sungaisa yanemi data nuna mashi gidansu, yayi mata godiya yatafi.

Tundaga ranar soyayya tashiga tsakaninsu, kai tsaye yanemi izinin aurenta agurin mahaifinta, babu bata lokaci ya amshi bukatarshi.
Zarah Allah yayi mata son kudi, babu abinda ta tsana irin talaka, duk da Allah yayita acikinsu amma bata son su, ko taron danginsu akeyi bata shiga, hatta da iyayenta hakuri sukeyi da ita, tasha yin mafarkin ta auri me kudi, segashi Allah ya amsa mata addu,arta tasamu me kudin, 
   Zarah bata damu da ilimin addini ba, ko sallah bata damu dayiba, amma tunda suka hadu da Alh, Abba taboye duk wani halinta marar kyau, shi kuma duk farin ciki ya isheshi yasamu diyar gidan mutunci, duk da azahiri iyayenta suna da mutunci amma bata gado suba.

Ahaka akayi aurensu, aka kaita kaduna cikin unguwar sarki akaton gidanta, haka suka cigaba da rayuwarsu cike da so da kauna, hankalinta ya kwanta, arzikin mijinta se karuwa yakeyi, hutu ya zauna mata tuni fatarta, ta murje tayi kyau sosai, tuni ta manta da iyayenta da danginta, tunda akayi bikin bata zuwa garinsu sosai, sede idan mijinta ya matsa mata, shima sede suje tare kuma bazata kwana ba, ko bikin dangine bata cika zuwa ba,  idan ma yabata kudin gudummuwa ko kwatar abunda yabada bata basu, gashi Allah yayi mata rowa.

Ahaka ta haifa mashi diyarta ta farko me suna Hauwa,u sunan mahaifiyarshice yasa dan duk iyayenshi sunrasu, dama shi kadai suka haifa, sede danginshi, hakan yasa aka sama diyarshi sunan mamanshi, ana kiranta da JIDDAH.

Bayan sunanta ne Alhaji Abba yabama Zarah kudi masu yawa yace tafara bussiness, kuma shine yayi mata jagora zuwa dubai domin fara kasuwanci, daga haka harta fara zuwa ita kadai, ahaka ne tahadu da wata mata me suna Hajiya Karima, itama babbar yar kasuwace, halinsu ne yazo daya dan danan suka kulla kawance, itama anan kaduna take. Kawancensu sukeyi sosai, Karima takara nuna ma Zarah duniya anan idonta yakara budewa takara koyon duk wata kissa, sede ita karima bata bin bokaye sede duk wata kissa ta iyata, shiyasa Zarah take zaune da mijinta lafiya, tana yimashi biyayya, saboda yana sakar mata duniya, ita kuma babu abinda takeso kamar kudi, tun bayan haihuwar Jidda taso tayi planing amma Karima tahana ta, acewarta tabari tahaifi namiji.

Bayan shekara biyu da haihuwar Jidda takara haihuwar diyarta mace, har kuka seda tayi, saboda bata samu namiji ba. Ranar suna yarinya taci sunan maman Zarah Saratu, ana kiranta da JALILA.
   Tun daga lokaci Karima tarakata aka tsaida haihuwar acewarta karta tsufa dawuri. Haka yara suka taso cike da kulawa, sudukansu suna da kyau, sede Jalila tafi Jidda kyau, Ahaka suka shiga makaranta, Jidda na P. 1 aka saka Jalila, haka suka cigaba da karatunsu, harsuka girma, alokacin Jidda tana da shekara 18 Jalila tanada 16, alokacin Jidda tana ss 3, Jalila tana ss 1. Halinsu kwata kwata bezo daya ba, Jidda gab daya irin halin Umminsu tadauko, Jalila kuwa irin Halin Dadynsu gareta, tunda suka gama Primary Jidda tafita daga islamiyya, Jalila ce kadai take zuwa, sede Dadynsu besan bata zuwa ba, kasan cewar aiyuka sun mashi yawa, ga tafiye tafiye dayakeyi. Ita kuma umminsu bata damu da ilimin addini ba. Tun Jidda tana ss 1 tafara kula samari, duk wanda zekirata yabata kudi to zata iya binshi duk inda yace, so dayawa Jalila tana kawo kararta amma Umminsu bata daukar maganarta abakin komai, karshema sede takoreta, ahaka harta shiga ss3 alokacin tahadu da kawaye yan duniya tuni suka maida bin maza aikinsu, sede kawarta. Ameera tafisu duniyanci, hakan yasa takaisu asibiti domin suma ayimasu planing. Tun daga lokacin suke sheke ayarsu, kudi suke samu sosai, dayake Jidda tana bama Umminsu kudi hakan yasa tarufe mata baki, takuma zama yar gaban goshinta. Kullum Jalila setayi kuka idan taga halin da yayarta tasa kanta, amma sanin kotayi magana babu wanda ze kulata yasa tayi shiru , saboda Zarah taja mata kunne akan idan har tafada ma Dadynsu wata magana akan Jidda seta tsine mata. Addu,a kawai takeyi mata, sannan ta maida hankalinta akan karatunta na boko dana islamiyya.

Alh. Abba ne yafito cikin shirinshi na tafiya sokkoto. Matarshi da yaranshi biyu, suka rakoshi har bakin mota. Alh, yace to Hajiya nizantafi akula da gida, insha Allah gobe zandawo, kallon yaranshi yayi yace ku kula da karatunku ina fatan babu wata matsala ko? Jidda tayi saurin fadin dady kayan kwalliyarmu sun kare, dariya yayi yace toga dubu 20 nan ai sun isa ko? Karba tayi tana dariya, Jalila tace dady mungode Allah yakara budi. Allah yatsare hanya, sosai yakejin dadin addu,ar da Jalila takeyi mashi aduk sanda yatashi yin tafiya, ita kuwa Jidda tuni tajuya tanufi gida tana murnar samun kudi, daga nesa take fadin dady seka dawo ayo mana tsaraba. Murmushi yayi ya girgiza kanshi yace toni zan wuce, Zarah ta rungumeshi tana fadin seka dawo mijina, Ganin haka yasa Jalila tayi mashi sallam itama ta juya, kiss yayi mata agoshinta yana kara rungumeta, anan yakara mata bandir guda na 1k yace kozata nemi wani abu kafin yadawo. Godiya tayi mashi sannan yashiga motarshi yawuce.

Dayake tafiyar batayi mashi sauri ba, kasancewar tsaye tsaye dayayi kuma dama befito gida dawuru ba, hakan yasa beshiga sokkoto dawuriba segurin karfe 8 na dare, kaitsaye yawuce gurin wadda yazo, dan agobe yakeso yakoma, shiyasa seda yaje yagama abinda yakawoshi sannan yawuce masaukinshi, misalin karfe 9: 30, dayake awajen gari masaukin nashi yake, yafito daga cikin gari tun daga nesa yaga kamar ana tsaidashi, sede beda niyar tsayawa, dan yasan halin yan, fashi babu abinda basayi inde suna son sutareka, haryawuce yaga kamar mata guda biyu ne abikin titin wadanda suke tsaidashi, gani yayi sunata waigen bayansu gashi daya daga cikinsu ta tsugunna kasa kamar tana kuka ganin yawucesu.
Cikin sauri ya taka burki yakoma baya, suna ganin ya tsaya da gudu daya takama hannun dayar suka nufi gurinshi, tambayarsu yafarayi, amma cike dasauri suka bude bayan motar suka shige. Dakyar take magana, dan Allah bawan Allah katemakemu kayi nisa damu daga gurin nan, wlh sunbiyo mu zasu kashemu...... Ai dajin haka yatada mota yafisgeta suka bar gurin, lokacin damasu binsu suka iso ko alamarsu basu gani ba, haka sukaita dube dubensu, ganin dare nayi suka juya domin komawa gurin Ogansu.

Ci gaban labarin. Danna Nan