AGOLA LITTAFIN NABILA
RABI’U ZANGO
LAKABI: NABILAT LADI
LAMBAR WAYA: 08028525263
BOOK 2: SERIES 2
Parking yayi adede wani karamin gida, inda
yakasance masauki agareshi aduk lokacin dayazo sakkoto, fita yayi suma suka,
fito, tsayawa sukayi suna kallonshi, ahankali yace bansan ina zan kaiku ba,
kuma gashi dare yayi, duk da kunce infitar daku wajen gari, agaskiya bazan iya
kaiku ba, saboda dare yayi kuma gashi ku mata ne, idan harkun yarda dani
kushigo ciki ku kwana idan Allah ya kaimu gobe semusan abinyi, domin nima ba,a
garin nan nake ba, wani aiki yakawoni yau, kuma nagama gobe zankoma kaduna acan
nake da iyalina.
Kallonshi babbar ciki tayi nawani lokaci
sannan tace bakomai munyarda da kai. Bude masu gidan yayi bayan sunshiga yakoma
yakwaso kayan cikin motar daya siyo, yashigo ya kulle gidan, zaune suke afalo,
shima zama yayi sannan yace. Ga dukkan alamu kuna dauke da yunwa, sede abinci
beda yawa kaza ce da lemu nasiyo se biredi, kucinye kawai gobe idan nafita
nasamo mana abinda zamu karya dashi, matar tace mungode sosai, amma yanzu
abinda kedamuna bamuyi sallar magriba da isha,i ba, murmushi yayi yajinjina
irin addini na wannan matar, daganinsu kasan suna tare da yunwa, amma duk da
haka take maganar sallah.
Dakinshi ya nuna masu
yace akwai bandaki aciki idan sungama ga abin sallah nan, bayan sunshiga shi
kuma yazauna afalo yana tunaninsu, yakosa sugama abinda sukeyi ya tambayesu
labarinsu.
Babbar matar takalli yarinyar dasuke tare, da
alama diyarta ce saboda tsanin kamar dasukeyi, tace kishiga ciki kiyi wanka
sannan kiyo alwala, zama tayi tajirata, har tagama tafito sanye da kayan data
cire, daukar hijabinta tayi ta kabbara sallah,ita kuma uwar tashiga domin yin
wanka.
Motsi yaji yasashi saurin
dagowa, ganinsu yayi sunfito tsaf dasu, anan take ya iya hango kyawun dake tare
dasu, duk da akwai alamun walaha atare dasu hakan be hana kyawunsu fitowa ba,
musamman dasukayi wanka suka fita daga cikin dattin dasuke, duk da basu canja
kaya ba.
Abinci yadauko masu yamika masu lemu da ruwa
harda biredin, murmushi babbar tayi tace da alama kaima bakaci komai ba, kuma
gashi kabamu duka, kadebi kazar semu hada biredin, yace a,a kude kuci ku koshi
tace Allah bazamu iya cinyewa ba, bata jira abinda zece ba, ta deba mashi kazar
dan tana da girma ta mika mashi da biredin, amsa yayi yana mata godiya,
murmushi kawai tayi takoma kusa da diyarta suka fara cin tasu, shide ci kawai
yakeyi amma hankalinshi yana kan wannan matar, addu,a kawai yakeyi acikin
ranshi Allah yasa bata da miji, dan tunda tafito yaji wani irin yanayi akanta.
Bayan sungama takwashe kayan tasa aleda ta
kaisu cikin dustbin tasaka, kalon diyarta tayi taga tana gyangyadi, Alh, yace
yan mata bacci kikeji kije ki kwanta, murmushi tayi tace to Dady, sosai yaji
dadin yanda takirashi da dady, tashi tayi tamasu seda safe tashige daki, matar
tace Alhaji kai kuma a ina zaka kwana? Murmushi yayi yace bakomai anan ma ya
isheni, zama tayi akasa tayi kasa da kanta tana wasa da yatsunta.
Shima kasa yasauko dan nesa da ita kadan, yace
duk da bansan sunanku ba, daga ke har diyarki kiyi hakuri kifadamun labarinku
dan bazan iyayin bacci ba idan har banji dalilin dayasa akeso akasheku ba. Idan
har babu damuwa inasonjin labarinku, dan Allah.
Hawayen dake idonta ta goge tace tabbas Alhaji
ka cancanci kaji labarinmu, domin katemakemu kuma nayarda da kai.
Nide sunana HAJARA amma anfi
kirana da HAJJO kasancewar mudin fulanine, Wannan kuma diyata ce sunanta FALAK,
kuma ita kadai Allah yabani, mijina Allah yayi mashi rasuwa yau wata 5 kenan.
Ajiyar zuciya yayi aranshi yana fadin Alhamdulillah.
Asalin labarin HAJJO...............
Ita kadai Allah yabama iyayenta,
kuma su fulanin daji ne, basu da taka maiman garin zama, ako da yaushe suna.
Canza gurin zama daga wannan guri zuwa wannan, tun bayan auren Baffanta da
Innarta suka bar garinsu wanda yake acikin niger, dan sunkasance fulanin niger,
haka suka rika yawo gari gari tare da Shanunsu, duk inda sukaje sukan kafa
bukkarsu agurin suzauna har zuwa wani lokaci, idan sun gama sesu tashi zuwa
wani gari, acikin haka har suka haifi Hajjo, wanda sunan innar Baffantane aka
samata.
Lokacin da Hajjo tayi girma har takai sheakara
10 alokacin suka yada Zango acikin garin gusau, acan bayan gari suka kafa
bukkarsu tare da wasu yan uwansu fulani dasuka hadu ahanya, koda sukaje gurin
sunsami fulani dayawa agurin, anan Baffa yaji dadi, dan tunda suke yawo basu
taba haduwa da fulani dayawa kamar wannan ba, anan suka zauna suka cigaba da
kiwonsu, inda Inna yakeyin fura da nono tana dora ma Hajjo tana bin sauran
sa,anninta zuwa cikin gari sukai talla.
Baffa dakanshi yayi
sha,awar saka Hajjo makarantar boko kasancewar yaga wasu daga cikin yaran
gurinsu suna zuwa, ahaka wani abokinshi jauro yayi mashi jagora zuwa makarantar
da diyarshi take, shima yasaka Hajjo.
Haka rayuwarsu tacigaba da
tafiya gwanin dadi, su Hajjo suna zuwa makaranta, ranar da babu karatu kuma
sutafi cikin gari talla.
Ahaka harsuka gama primary alokacin Hajjo tana
da shekara 16, kyawunta yakara fitowa sosai, kowa sonta yakeyi, watarana
suntafi kasuwa ita da kawayenta domin aranar kasuwa takeci, sunje kai talla
Tunda sukaje kasuwar ta lura
dawani yanata kallonta, ahaka harsuka saida suka siyi abinda zasu siya suna
shirin tafiya gida. Sallama taji anyi mata, amsawa tayi tare da juyawa domin
ganin me mata sallama, wannan wanda tagani yana kallonta shine de tare da
abokinshi.
Sannunku yanmata yace yana kallonta fuskarshi
dauke da murmushi, bayan sun gaisa yake tambayarta sunanta, tace Hajjo,
murmushi yayi yace Hajara kenan, amma sunan akwai dadi, ni sunana Bashir, kuma
ni dan sakkoto ne, ina zuwa nan duk ranar kasuwa, amma Allah betaba jadamu ba,
se yau, murmushi tayi tace zanwuce abokan tafiyana suna kirana kada dare yayi,
kallon abokinshi yayi yace to abokina nima tafiya zanyi dan banason dare yayi
saboda barayin hanya, dan Allah kabisu Hajjo kaganemun gidansu idan nadawo sati
mezuwa kwana zanyi seka rakani. Godiya yayi masu sukayi sallama.
Tundaga wannan lokacin soyayya tashiga
tsakanin Bashir da Hajjo, har iyayenta sun san dashi, Baffane yace ma
Hajjo idan Bashir yazo yanason ganinshi.
Zaune suke abisa tabarma, anan
Baffa yake tambayar Bashir asalinshi, Yace nide sunana Bashir, kuma ni dan
asalin sakkoto ne, iyayena sun rasu tun ina dan shekara 20, banida kowa se
kawuna, agurinshi nake kuma gida daya muke dashi, kasuwanci shine sana,ata ina
zuwa garuruwa kasuwanci, kuma a sakkoto gidana yake wanda mahaifina ya mutu
yabarmun.
Baffa yace Alhamdulillahi, anan
shima yafadamashi alabarinsu, sannan yace tunda naganka naji hankalina ya
kwanta da kai, kuma nabaka Hajjo, ko yaushe kake so adaura maku aure zaka iya
zuwa, sede inaso dan Allah karike mana Hajjo bisa gaskiya da amana, ita kadai
Allah yabamu, kuma kaga bamuda kowa anan, gashi ba gari daya zamu zauna ba,
kasan mudin makiyaya ne, inaso karike mani ita, kuma dan Allah karika kawo mana
ita duk sanda zaka zo kasuwa, kafin mutashi daga nan, duk da gaskiya bayanzu
zamu tashi ba, dan naji dadin zaman gurin nan.
Bashir yace insha Allahu Baffa zaka sameni me
riko da amanar daka bani, kuma insha Allah sati mezuwa tare da kawuna zamuzo se
adaura mana aure, banaso ku wahalar da kanku, Hajjo kadai nake so, saboda haka
kada kusiyi komai. Godiya Baffa yayi mashi sannan yatashi yakira mashi Hajjo.
Bayan sati guda Bashir yazo da kawunshi Wanda
yake kanin mahaifinshi dasuke uba daya, sunanshi Lado, amma mutanan gari suna
kiranshi da Figo. Kasancewarshi cikenken dan duniya, danshi haryanzu beyi aure
ba,sede lalata yaran gari, beda wata sana,ar data wuce shaye shaye da sata,
shine oga acikin group dinsu, dan har yara gareshi. Bashir hakuri kawai yake
dashi, tunda agida daya suke, sede shi kawu Figo adayan part din yake.
Bayan andaura aure aka shirya Hajjo cikin
dinkunan da Bashir yakawo mata, sosai tayi kyau ahaka sukayi sallama da
iyayenta suna kuka tafito, kawayenta suka rakota, harbakin mota suka kaita,
suma kukan sukeyi ahaka suka tafi, ita kada abaya Bashir da kawu agaba, Bashir
ke tuka motar. Tunda Kawu yaganta yake hadiye miyau yana murmushi aranshi yana
fadin tsuntsu daga sama gasashshe.
Bayan sunje gida ya aje kawu sukuma suka shige
gidan, gidan yayi kyau sosai, komai yasaka aciki kayan more rayuwa masu kyau
yasa mata.
Ahaka sukaji gaba da rayuwarsu cike da so da
kauna, komai najin dadi Bashir yanayi mata, sosai yake taka tsan tsan da
gidanshi, saboda kawu, dan yafikowa sanin halinshi, ko abincin da Hajjo take
bashi be bari takai mashi shine yake bashi da kanshi, idan kuma tafiya
takamashi sede yakai Hajjo gidan abokinshi Saddik ta kwana, duk yanda kawu yaso
kebewa da Hajjo Bashir yahana, idan yashigo gidan sede idan Bashir yana nan. Duk
sanda zeje gusau cin kasuwa tare da Hajjo yake zuwa, sosai Hajjo tayi kyau,
takara girma.
Bayan shekara biyu da aurensu tahaifi diyarta
me kama da ita sede Allah yayima yarinyar kyau sosai, tun tana jaririya, ranar
suna Bashir yasa mata FALAK, dan yace yana son sunan sosai.
Tunda FALAK ta girma yasata a primary, ranar
dazeje gusau tare suka tafi, kwnansu 2 sannan sukafara shirin dawowa, Inna
tadauko wasu awarwaro masu kyau guda biyu ta bama Falak, kasancewar sun mata
yawa yasa Hajjo ta amsa tasaka a hannunta, haka taji kamar karsu tafi, Baffa
yakara tunama Bashir akan rikon amanar daya bashi, haka sukayi sallama suka
tafi.
0 Comments
Post a Comment