HUBBUL YAKIN 3
ASIYA SADIQ MACCIDO
(ASIKHAN)
Copyright © Asiya Sadiq 7th March, 2019 to 4th March, 2020
Hakkin Mallaka (M) Asiya Sadiq 7th March, 2019 to 4th March, 2020
Published in Nigeria by
Sharhamak Computer Ventures
Beside Birnin Kebbi Local Government Secretariat
Kebbi State, Nigeria
Website: www.hausanovels.xyz
E-mail: scv.edu123@Gmail.com
Tel: 08113777717
Hotonta
ne akan screen din wayar sa`adda shekarunta ba xasu wuce 16 to 17 years
ba,kamar wacca aka xarewa laka a jiki ta fara juyowa a hankali browsing din
muryarda keyi mata bala`in takeyi a kwakwalwarta ,wa xata gani a gaban
nata,USMAN! Ne tsaye a cikin qananan kaya
tamkar wani bature,ga baki daya numfashinta qoqarin ficewa yakeyi daga jikinta kallonshi
kawai takeyi idanuwanta a xaxxare kamar wacce
taga axara`ilu.A fusace ya
kalleta amma cin karo da yayi da fuskarta ya sanyashi kidimewa gami da rikicewa a nan take,ga baki daya rasa
ta cewa yayi kallonta kawai yakeyi wani farin ciki da jin dadi ke xiyartar xuciyarshi sam! Ma ya rasa wace duniya yake a
ciki,mema xaiyi,me xaice duk ya rasa,farin cikinda ya tsinci kanshi kuwa a ciki
kai daka ganshi xaka xata anyi masa bushara ne da gidan al,janna. Qaf! taji
yawun bakinta sun qafe ,ga baki dayama ta rasa me xata ce kamar kurma haka ta
koma ta nemi Magana sama da qasa ta rasa,wai shin mafarkine ko gaske,usman
dinne take gani a tsaye a gabanta .Kallon-kallo kawai sukeyi sai kace wasu xakuna,kowa ya rasa me xaice.Su
Hajiya Larai kuwa suka dawo baya da hanxari a sakamakon ganin abinda ke gudana
da sukayi,please kayi haquri malam bada
gan-gan bane kuskurene kowa kuwa xai iya yi,Hajiya Lara ice ke bawa Usman
haquri.Ga baki daya baiji ma abinda take fad aba,kafe Bilkisu kawai yayi da ido
yana wani tattausan murmushi wanda yake nuna tsagworon farin ciki gami da
tsantsar so da qauna,har a ranshi so
yakeyi ya janyota a jikinshi ya rungumeta,tunanuka kala-kala ne ke xuwa mishi a
xuciya.Ita kuwa Bilkisu a tata xuciyar farin ciki da murna takeyi domin kuwa gani takeyi tamkar a yau dinnan ne
xata ceto mijinta wato Sulaiman,wani bangare kuwa xuciyar tata saqa mata takeyi
ta dallawa Usman din mari akan irin bala’o ukan da ya jefata,Bata taba jin
haushi gamida baqin cikin mutum ba sai a ranar a kuma lokacin,ba kuma ta tuna
da irin tambonda Usman din yayiwa rayuwarta ba sai a yanxu da yake tsaye a
gabanta.Wasu xaafafan hawae ne suka kwaranya daga idanuwanta suka dinga
kwaranya akan kyakkyawar fuskarta,muryarta na rawa gami da karkarwa take fadin
“NEMANKA XAMUJE”wannan Kalmar kadai ta samu ta fito daga bakinta.No! No! don’t
cry Usman ne ke fadan haka fuskanshi duk a yamutse,ba sai kinje nemana b,gani
na dawo a gareki Kaman yanda nayi miki al’qawari a baya cewan xan dawo a
gareki,ni kadai ne mijinki a duniya,banci amanarki ba Billy koda kuwa da one
second ne,kullum kina a cikin xuciya ta idan bake ba wama kike ganin xanso,kin
rigani ne domin kuwa da a gobe ne nayi niyar xuwa nemanki nayi niyar xuwa neman
ixnin aurenki a wurin mahaifinki domin kuwa na riga da n agama tanadar mana
gamida shirya mana rayuwa mai dadi kuma mai dorewa ta har abada ni nakine ni kadai a duniya domin ni akayiki domin ki kasance dani ki xamo uwar
yaya na,lokacinda yakai nan a xancensa qoqari yayi ya janyota ya rungumeta.amma
kallonda tayi masa ya dakatar dashi daga aikata hakan.Batasan ma ta inda xata
fara yi masa bayani ba,tamkar wani mara hankali take kallonshi,lallaima usman
dinnan bayada hankali ta dauka shi shahararre ne a fagen iya soyayyya ashe bah
aka bane,domin da kuwa ace yasan meye soyayya,kallo daya xaiyi mata ya isa ya
hango a cikin idanuwanta sam ba soyayyyarshi koda kwatan kwacin kwayar xarra a
ciki,da ace shi gwani ne ai da ya gano kukanda takeyi bana murnar ganinshi a
matsayin masoyi wanda nake murna da farin cikin gani bane a’aina murnar ganinshi ne a matsayinshi na makulli wanda
yakeda qarfinda xai iya bude mani
qofarda xata da xata sadani da mijina,mahaifin cikinda yake a jikina yanxu
haka.Hajiya Larai da Tukur ne a tsaye sun kafe su da idanu,mamaki da al’ajabi
ya hanasu Magana,sam basa buqatar a
gayamusu wannan saurayin waye domin kuwa abinda idanuwansu suka gane musu kadai
ya isa yasa su fahimci ko shi wanene koshi waye.Ba qaramin farin ciki sukayi ba
Allah ya sauqaqe musu wahala ya hadasu dashi ba tareda sun wahala ba,su dai
shiru sukayi abinsu suka mayarda Usman
din da Bilkisun t,vn su abin kallonsu,toh! Mema suka san xasu ce ne idan ba
kallo kawai ba,Dogon numfashi Bilkisun tayi we need to talk Usman,mu tafi gida
xamuyi Magana,yamutsa fuska yayi kana yayi murmushi okay! Mu tafi,itace ta
shiga gaba Usman din ya biyota baya kana
su Hajiya Larai.Ga motar a can ta nuna masa motarsu data kawosu a airport din,sai a lokacinne ya kula dasu
Hajiya Laranda ke biyansu,tsayawa yayi cikin farin ciki yake maganar,su waye
wayyan Billy,kar dais u umman ki ne kinga wallahi sam ban gansu bad an Allah
kiyi haquri ban gaidasu bahankalina ne ya dauke,ganinki da nayi a kusa dani ya
sanyaidanuwana rufewa da ganin kowa kafin tayi Magana tuni ya dawo baya da
qarfi gaishesu yayi cikin girmamawa tareda basu haqurin rashin aikata hakan da
yayi tun a farko tareda gayamusu shi sam bai gansu a wurin bane,sun kuwa amsa
mishi suma sosai .Alfarma ya nema kai tsaye a wurinsu da su amince shida
Bilkisu dasu amince shida Bilkisu su shiga motarda taxo daukanshi,ya nuna musu
motarda take gefen damansu ya gayamusu sai su bisu a baya su isa a gidan,rasa
me xasuce sukayi,kallon-kallo kawai sukeyi a tsakaninsucan hajiyar ta samu tace ba damuwa juyowa yayi ya kalli Bilkisu
wani dadi yaji a xuciyarsa kamar wanda aka bawa daman ya dauketa kawai su wuce
abinsu.Kallonshi kawai tayi wani haushi da takaici duka suka cikata tama rasa
me xata ce masa,Su Hajiya Larai ne suka fara bude motarsu suka shiga,sai Usman
da Bilkisu kuma da suka nufi gun tasu dalleliyar mota,sabuwa gar! Da ita,da
hanxari driver yaxo ya karbi kayanda ke hannun Usman din ya nufi boot din motar da nufin ya bude
boot din ya saka kayan a ciki.Usman ne yayi hanxari ya budewa Bilkisu murfin
motar tareda yi mata nuni akan ta shiga.Bata kalleshi ba a wannan karon kai
tsaye shiga kawai tayi,ya maida murfin ya rufe yayi sauri ya nufi nashi bangaren
ya bude ya shiga,tada mota drivern yayi,motarda take gabanmu xaka bi duk inda
tayi a can xakayi a can xaka kaimu,to ranka shi dade drivern ya fada tareda jan
motar.Matsowa Usman din yayia kusa da Bilkisu amma a hankali taja da baya ba
tareda ta kalleshi ba kota nuna qoqarinda yakeyi nan a matsowa daf da
ita,kallonta yayi yayi murmushi domin kuwa ya lura da matsawarda tayi gamida
shan jinin jikinta da tayi.Billy I miss you,I miss you,I miss you so much,I
miss u moredan you can imagine moredan you can think up,hannunta ya janyo ya
riqe yaci gaba da rero mata bayanai da
kalamai wayanda ba matar aurenda ya kamata tajisu a bakin wani idan dai ba
mijinta na sunnah ba .Da hanxari ta fara yunqurin kwatar hannunta daga gareshi amma sam! Ta kasa kwace
hannun nata,dariya ya saki kana ya sake mata hannu you are still the same
Billy,ya girgixa kai very soon xan kama wannan hannun naki batareda kinyi
yunqurin kwacewa ba,very soon xan mallakeki da duk wani abu naki Billy,very
soon xaki xama mallakina xan kuwa yi amfani da wannan hannun nawa na riqe
wannan dan qaramin hannun naki always.Juyowa kawai tayi ta quramai idanu daga
bisani tayi murmushi tace you are still the same itama ta girgixa kanta.Billy I don’t
know what’s going on but xuciya na was
telling me something kamar da wani abu I mean kamar something ix wrong,Billy I
didn’t expect irin wannan tarbar from you,gaya mani meke faruwa,tsayawarda
motarsu tayi ita ta katse xancenda yakeyi,kallonshi takeyi mu shiga daga ciki
ta mude motar ta wuce,ga baki daya kanshi ya kwance amma kamar wanda aka yiwa
asiri haka shima ya bude motar ya fito,driver kuwa qoqari yakeyi ya bude boot
din motar domin ya ciro kayanda ya saka amma da hanxari Usman ya dakatarda
shi,xo nan please ba sai ka fitarda kayanba,ya tura hannu al’jihu ya ciro
warlet ya qidaya “yan dubu-dubu a qalla xasu kai goma ya danqawa drivern ga
wannan ka hau acaba ka koma gida nagode sosai kaji.Wani farin ciki ne ya
kamashi ,ji yakeyi kamar ya rungume Usman din akan matuqar dadinda yaji nagode
kwarai ranka shi dade Allah ya saka da alkhairi ya qara daukaka da budi,Usman
bai jira y agama jin maganganun yabo da jin dadinda yakeyi ba ,ya gyada kai
kawai yace amen kana yasa kai yayi cikin gidan.A falo ya tarar da su ga baki
daya suna jiran shigowarsa yanda ya gan kowa ya kafe shi da ido ya sanya ya dan
tsaya na “yan daqiqu,Hajiya Lara ice ta katse kallon-kallonda akeyi.Bismillah
xo ka xauna please murmushi yayi kana ya nemi wuri ya xauna,kafin yayi yunqurin
fadin wani abu tuni Tukur yayi gyaran murya ya fara yi masa sannu da xuwa kana
ya bayyana mishi irin matuqar farin cikinda sukayi ga baki daya a sana diyar
ganinshi da sukayi ,sa’annan ya gabatarda kansa daga bisani kuma ya fede masa
daga biri har wutsiya danganeda abinda ke faruwa tun daga batar Sulaiman mijin
Bilkisu da kuma shi rashin lafiyar danshi harya xuwa bacewar dan Hajiya Larai
namiji daya tilo da takeda shi a duniya harya xuwa inda suke yunqurin xuwa da
shirinda sukeyi na ganin qarshen wannan fatalwa tareda yi masa bayanin shi
kadai ne xai iya taimakonsu ya gaya musu duk wani abinda yake ganin ya sani
danganeda ita wannan fatalwar domin su fara hanya domin can dama rashin ganinsa
kawai ya tsayadda su.
Tsit Usman din yayi kamar wanda ruwa yaci
me ma xaice,mema yake ciki,mema yake tunani kwata-kwata ya kasa ganewa ya rasa
a sama yake ko a qasa,miqewa yayi ya janyo hannun Bilkisun idanuwansa jajur mu
tafi ya fada tareda janyota da qarfi,ina xamuje,tsayawa yayi ya juyo da qarfi
because I don’t have time for this
nonsense kuma I’m 100% sure kema haka,kinji wai abinda yake fada wai kinada
miji shi xakije nema alhali kuwa gani a tareda ke a yanxu,Billy have u lost it
meye haka me kikeyi anan,I didn’t expect you to waste your precious time akan
irin wayannan abubuwa,mema kikeyi a kaduna,ya danyi dan guntun tsaki,ki bar
wannan maganar kawai meye ma yi a hanya yanxu dai lets go!.Kwace hannunta tayi
cikin tsananin fushi ta fara xance;Yes! I lost my mind I lost it hawaye suka
fara kwaranyo mata kamar fanfo,kallonshi itama takeyi idan dai xuwa neman
mijina ne yasa kake daukana mara hankali na yarda 100% ni mahaukaciya ce.Wani
mayen kallo yayi mata No! No! No! ya fada da qarfin gaske a’a ban yard aba ,ban
yarda kinada wani miji ba Billy you can do this to me,hawaye suka xubo masa a
yayinda ya gani a cikin idanuwanta cewa abinda take fada tsagwaron gaskiya
ce.Haba Billy! Haba Billy! Why! Why! Me yasa xakimun haka,I love you with all
my life mun yiwa juna alqawari akan ba xamu taba son wani ballantana har muyi
aure idan dai bada junanmu ba me yasa xaki karya alqawari me yasa xakimun haka
tun a lokacinda mukayi bankwana da juna na tafi ban taba kallon wata mace a
matsayin mace ba,kece kadai wacca na sanya a raina kullum burina da fatana bai wuce naxo na
aureki mu wuce tare a gidana ba ki kuwa Haifa mun “yaya kamar yadda muka tsara
nida ke,runtse idanu yayi,da sauri kuwa ya
bude idanun sai kuwa idan tilasta miki akayi na tabbata ba xaki iya
yimin haka ba,nunfashi ya ajiye har a lokacin hawaye xuba sukeyi daga
idanuwansa na tabbatarda tilasta miki akayi idan kuwa ba haka ba,ba yanda xaki
auri wani idan dai bani MAN dinky ba.Wani tsakin takaici tayi ta girgixa kai a
cikin ranta tana fadin what is wrong whit this guy,sauri yayi ya goge hawayenda
ke xuba daga idanuwan nasa,kada ki damu yanxu daga nan a police station xamuje
da kuma kafafen yada labarai ,xa’a nemoshi domin yaxo ya sallama kayanda dama
can ba mallakinsa bane kayanda ya kwata da qarfi da yaji kasancewar xuwan mai
abu.Wasu sababbin hawaye ne suka xubo kwaranyo mata Usman ba wata police
station dinda xamuje ina kuma so ka sani ba wanda ya tilasta mani domin nayi
wannan auren,auren soyayya ne nayi,ba kuma wanda nakeso da qauna a duk fadin
duniyarnan daya kai mijina,me kake nufi
All those years daka share na xauna nayita jiranka for God sake! Nifa macece
dan kawai kacemin xaka dawo sai kawai nayita xama ina sauraren xuwan naka,a
yaushe ne mukayi da kai xaka dawo after one year! Ta fada da qarfi ko xaka iya
lissafa how many years yanxu da
tafiyarda kayi,look at me dan Allah ka kalleni da kyau ka gani I’m all enough
ace nayi aure,kana ganin iyayena xasu sakamin ido ne kullum suna kallona a
gabansu,and idan suka tambayeni kawai sai nace ina jiran dawowarka ne,I tried
nakai kusan 3 to 4 years ina jiran dawowarka,ban kuwa saurari ko wane namiji ba
a cikin wayannan shekarun na samu many many proposals but I reject them all,har
Allah ya qaddari iyayena suka yimin xabi na alkhairi wato Sulaiman da farko abin
yaxo kamar arrenge marriage but later on ya rikida ya koma love marriage,ina
sonshi Usman ina matuqar qaunarshi fiyeda komai a duniya xan iyayin komai domin
naga na cetoshi daga halinda yake ciki,kuka mai tsanani ya kwace mata hannunta
ta axa akan cikinta ta kalleshi I’m pregnant ,kuma cikin na halak ne wanda kuma
yake da cikin shine love of my life,bai jira ta kammala xancenda takeyi bay a
gyada kai yace thank you,thank you so much Billy I’m greatful ni kike gayawa
haka nine kike gaggayawa wayannan maganganun thank you,shima kukan kwace masa
yayi cije lebe yayi ya kalleta ga baki daya abubuwanda kika gayamin basu is aba
har sai kin dubeni kince na taimaka miki domin nemo mijinki,Billy ban cancanci
haka daga gareki ba,share hawayen yayi kana ya murtuqe fuska,idan kece a
matsayina xaki iya taimakawa da wani abu domin kawai matata ta dawo,wear my own
shoes would you do the same,shiru tayi tana kallonshi ba tareda ta bashi amsa ba,I guess the answer
is No! dan haka nima baxan taba taimakawa ba koda kuwa da komai ne wajen ganin
wanda ya tarwatsa rayuwata ya dawo,kama hanya yayi yana yunqurin ficewa
abinshi,da gudu Bilkisu ta isa diny ta dauko wata sharbebiyar wuqa,a gabanshi
ta tsaya ta bude hannuwanta wanda hakan yake nuni da tana dakatardashi ne,a’a
ba xaka wuce haka kawai kai tsaye ba Usman ya xama dole ka idarda abinda ka
fara,kaine ka tarwatsa rayuwana nida mijina a sanadiyarka ne mijina ya salwanta
duk kaine ka tarwatsamin farin ciki na inaga abinda ya rage ka aikata yanxu
shine kaa karbi wannan wuqar ka sokeni da ita ka kawo qarshen rayuwata da duk
wani baqin ciki da damuwata ta miqa mishi wuqar karbi! Ka kasheni,shine abu
mafi sauqi a gareni da ace ina rayuwa a doron qasa alhali mijina yana a cikin
mawuyacin hali kuma kadaice nakeda damar fitarda shi daga wannan halin amma na
gaxa akan kawai wani abu daya shiga tsakanina da kai,ka karba nace! Ta buga
masa tsawa,ji yakeyi kamar an cire xuciyarsa ne daga jikinsa an jefata a cikin
wuta mai matuqar xafi da ruruwa,shi Billy ke gayawa ya kasheta akan kawai yace
ba xashi taimaka musu ya fadi musu abinda ya sani dangane da fatalwarda yaji
suna fad aba,I cant baxan iya kasheki ba Billy ya fada sannu a hankali,faduwa
tayi akan gwuiwowinta roqonshi takeyi cikin tsananin kuka na roqeka Usman ka
taimaka mani ka ceto rayuwata data mijina ka taimaka ko domin abinda yake
cikina kada idan ya girma ya tambayi ina mahaifinsa na rasa amsarda xan bashi
domin baxan iya gayamasa ya bata a sanadiyar wani tsohon saurayina ba kuma kuma
tsohon saurayin nawa shine kadai xai iya gaya mana inda xan nemoshi amma ya qi
amincewa ya gayamin a sanadiyar ban jira shi yaxo ya aureni naje na auri mahaifin
nashi ba,ka taimaka mani ka tausaya manakada gidanmu ya tarwatse na roqeka ka
taimakamun dan Allah,ta riqe masa qafa tana sharara kuka mai matuqar ban
tausayi a wurin duk wanda yaji.Sauri yayi ya tayarda ita shima kukan
yakeyi,Billy kece farin ciki na ki sani xan iyayin komai a duniya domin kawai
naga farin cikin ki,ki share hawayenki nayi alqawari baxan tafi ko’ina ba har
sai an gano duk inda mijin naki yake a fadin duniya koda kuwa hakan na nuna
rasa tau rayuwarne because I can sacrifice my life to depend yours,kince nine
na tarwatsa rayuwarku ko,I will be the one to pixed it I promise you,wasu
xafafan hawaye suka gangaro masa cikin sheshshekar kuka yake maganar ,a halin
yanxu bansan komai dangane da fatalwa ba bansan wata wacca take sona har ta
yadda ta kasha kanta a kaina ba wallahi amma nayi alqawarin kowacece xan nemo
labarinta da duk wani abu daya shafeta,kuma dani xa’aje har inda xa’aje kamar
yadda na gaya miki sai na damqa miki mijinki a hannu is my promise,sa kai yayi
da nufin ya ida wucewa,maganarta ne ta dakatar dashi,ina xakaje,xanje na kama
Hotel ne ko kuma na sauka gidan abokina,amsar kawai ya wurgo mat aba tareda ya
juyo ya kalleta ba,muryar Tukur sukaji a bayansu; inagaxamanka anan gidan xaifi
idan mu duka muna a wuri daya xamufi samun qarfin warware duk wata
matsala.Juyowa Usman din yayi shi sam ma ya manta da cewar akwai wasu a
falon. Hajiya Larai ce ta sakobaki;abinda ya fada gaskiya ne Usman xamanka anan
xaifi xamanka a ko’ina muhimmanci,Bilkisu ya kalla ta gyada masa kai alamar
tana goyon bayan abinda suka fada,shima gyada kan yayi,Hajiyarce ta nuna masa
wani daki ga dakinda xaka xauna a can empty ne ba kowa a ciki amma a kullum sai
an gyara shi an tsaftace shi ni kuwa keyin gyaran da kaina domin dakin dana ne
daya bata kamar yadda Tukur ya gayama,gyada kai kawai yayi ya nufi hanyar dakin
,tsayawa yayi ya ciro mukullen mota ya miqawa Hajiyar please ko xaki taimaka ki bawa driver ya ciromin kayana da suke a boot,amsa tayi ta
gyda mishi kai okay.Harya nufi dakin kuma ya sake dakatawa kamar wanda ya tuna
wani abu murtuqe fuska yayi ya juyo ya kalli Tukur sam! Bai yarda dashi ba,meye sunan Alhajinda
ya sanya kayi masa aikin ,Alhaji Aliyu wanda kuma aka yiwa aikin….a tattare
suka fada lokaci daya shida Usman din ALHAJI UMAR! Ga baki daya wayanda suke a
falon suka qura masu ido mamaki ya kama kowannensu hatta shi kanshi Tukur
din,cikin tsananin fushi Usman din ke Magana,kai ne axxalumi na farko dana taba
gani a duniya duk kai ka janyo wannan abin,ta yaya ma xamu iya yarda da kai
ne,ya kafeshi da ido sai huci yakeyi kamar wani namijin kure,wanda ya sanyaka
kayi masa danyen aikin ba kowa bane face qanin mahaifina!wanda kuwa akasa ka
hallaka shine MAHAIFINA! Biological father dina wanda ya haifeni,kai babban
maqiyi nane tunda kuwa nayi arba da kai xuciyana bata aminta da kai ba,ban
yarda da kai ba,ka sani idan ma wani abu kake shiryawa to lallai xanyi
maganinka,idan kuwa na gano kanasone kayi amfani damu domin cimma wasu
manufofinka na can daban xan axabtarda kai xan kuwa tabbatar kayi nadama mara
iyaka.Billy ce tayi sauri ta budi baki da nufin Magana amma caraf! Tukur din ya
amshe,kada ki hana shi fadan abinda yake ransa yanada daman fadan abinda duk ya
gadama kuma koma da wane irin suna ya kirani sam baxan damu ba sai dai inaso ka
sani akwai wayanda suka aikata ta’asarda tafi tawa a duniya kuma daga baya suka
gano hanyarda suke kai ba mai bullewa bace suka watsarda miyagun ayyukansu suka
rungumi kyawawa Allah ta’ala ya shiryarda su ya kuma datarda su suka kasance
cikin masu rabo nasan na aikata laifuka a baya amma kuma yanxu na canxa daga
mummuna xuwa kyakkyawa,yayi murmushin yaqe komai xan fada nasan baxaka yarda
dani bad an haka ba amfanin maganganuna ma,dallah mishi harara Usman yayi kana
yasa kai ya nufi dakinda aka nuna mishi ya shiga tareda bankado qofar ya
rufe,Duka wayanda suke faloon shiru sukayi Kaman ruwa ya cisu ba wanda yake
cewa kowa komai daga bisani kowa ya nufi nashi dakin kai tsaye.Hajiya Lara ice
aka bari ita kadai a faloon,sai da ta wanke hawayenda suka wanke mata fuska a
dalilin abinda ya faru a gaban idonsu
kana ta kwallawa driver kira da hanxari drivern ya shigo ta umurce shi
daya daukowa Usman kayanshi a mota ya kai mishi a dakin khalifah ansawa yayi ya
fita a falon da hanxari domin ya cika aikinda aka sashi,harta kama hanya kuwa
kamar wacca ta tuna wani abu ta yiwo kiran wadda keyi musu abinci,wata
dattijuwa e ta fito da murmushinta,Hajiya gani,munyi baqo ne yanxu dan Allah
inaso ki dafa masa wani abu wanda ya dace wanda yayi tafiya ya gaji ace
yaci,kin gano ai gyada kai tayi na fahimta ranki ya dade yanxunnan kuwa xa’a
gama,yauwa idan kika kammala ki kai masa a wancan dakin ta nuna mata dakinda
Usman yake ,to ranki ya dade.Hajiyar tasa kai ta fice ta nufi dakinta.
A can bangaren Usman kuwa xaunawa yayi
akan gado ya fara sheqa kuka mai tsananin gaske ,shi mema amfanin rayuwarsa,me
yasa Bilkisu xatayi mishi haka,tamkar a mafarki yake ganin komai kuka kawai
yakeyi kamar wani qaramin yaro,wayarshi ce tayi ringin da kyar! Ya iya cirota
daga aljihunsa ,sunan abokinshi ya gani a jikin wayar da sauri yayi picking.Wai
kana ina har yanxu ban ganka ba ko baka gane drivernda na aiko maka bane,abokin
nashi ya fada cikin ba’a,where are you Ashir,Usman ya fada kai tsaye,shiru
Ashir din yayi,what is wrong,meke faruwa ne Usman,Ashir ya tambaya da sauri,I
just want to see you now Usman ya fada har a lokacin kuka yakeyi ,okay! Okay! A
ina xamu hadu,Ashir I cant drive baxan iya tuqi ba a halin yanxu kuma na salami
drivern da ka aiko ya daukeni.Ga baki daya abokin nashi ya rikice,kana ina
yanxu gayamin yanxu xan iso,one minute bari na miqawa wai ya kwatanta ma wajen
ya miqe da sauri ya fita daga cikin dakin,ai kuwa Bilkisu ya hango itama ta
bude dakin nata ta fito,sauri yayi ya goge hawayenda ke xuba daga
idanunshi,itama hangoshin tayi cak ta tsaya da taga ya nufo inda take
gadan-gadan ,miqa mata wayar yayi please ki kwatanta mishi wannan anguwar
kallonshi tayi,abokinane inaso ne na ganshi,amsar wayar tayi ta kara a kunnenta
sallama ta farayi bata jira ya amsa sallamar ba kai tsaye ta kwatanta mishi
gidan yanda xai gane kana ta miqawa Usman din wayar.Kallon-kallo suka riqa yi
kowannensu idanuwansa a kumbure da kuwa
kayi arba da idanun xaka fahimci har a lokacin xubarda kwalla sukeyi,sun kusa
kai minti biyar suna kallon juna ba
tareda daya daga cikinsu yay i Magana ba,Bilkisu ce tayi sauri ta bude qofar
dakin nata ta shiga tareda bankado qofar da sauri ta rufe,kallonta yakeyi har
sai da qofar ta rufe sa’annan ya kara wayar a kunnensa, ina jiranka.
0 Comments
Post a Comment