ADDU’A
DAGA AL-QUR’ANI DA HADISI
FASSARAR HAUSA










شَرْحَبِيلُ بِنْ مُحَمَّدْ ثَنيْ
SHARAHBIL MUHAMMAD SANI
www.craspost.xyz
E-mail: scv.edu123@gmail.com
Tel: 08113777717


ADDU’A DAGA AL-QUR’AN
1.      "Ya Ubangijinmu! Ka bamu mai kyau acikin duniya da mai kyau a cikin lahira, kuma Ka tsare mana azabar wuta!" (2/201)

2.      "Ya Ubangijinmu! Ka zaba  hakuri a kanmu, kuma ka tabbatar da duga duganmu, kuma Ka taimake mu a kan mutanen nan kafirai." (2/250)

3. “Ya Ubangijinmu! Ka da ka kama mu, idan munyi mantuwa, ko kuma munyi kuskure.
Ya Ubangijinmu! Kuma kada ka aza nauyi a kanmu, kamar yadda ka aza shi a kan wadanda suke a gabaninmu.
Ya Ubangijinmu! Kada Ka sanyamu daukar abin da babu iko garemu da shi. Kuma ka yafe daga garemu, kuma Ka gafarta mana, kuma Kayi jinkai garemu. Kaine majibincimmu, sa boda haka ka taimakemu a kan mutanen nan kafirai".

4. "Ya Ubangijinmu! Kada ka karkatar da zukatanmu bayan har ka shiryar damu, kuma ka bamu rahama daga gunka. Lalle ne, Kai, Kai ne mai yawan kyauta."

5. "Ya Ubangijinmu! Lalle ne mu, mun yi Imani, sai Ka gafarta mana zunubanmu, kuma ka tsare mu daga azabar wuta."

6. "Ya Ubangijinmu! Ka bani zuriyya mai kyau daga gunka. Lalle ne Kai mai jin addu’a ne."

7. "Ya Ubangijinmu! Mun yi Imani da abin da Ka saukar, kuma mun bi manzonka, sai Ka rubutamu tare da masu shaida."

8. "Ya Ubangijinmu! Ka gafarta mana zunubanmu, kuma ka tabbatar da duga duganmu, kuma ka taimakemu a kan mutanen nan kafirai."

9. "Ya Ubangijinmu! Ba ka halitta wannan akan banza ba, tsarki ya tabbatar maka, Ka saboda haka Ka tsare mu daga azabar wuta.
"Ya Ubangijinmu! Lalle ne kai, wanda ka shigar a cikin wuta, to, hakika, ka tozarta shi, kuma babu wasu mataimaka ga azzalumai.
"Ya Ubangijinmu! Lalle ne mu munji mai kira yana kira zuwa ga imani cewa, kuyi Imani da Ubangijinku. Sai mukayi Imani.
"Ya Ubangijinmu! Saboda haka ka gafarta mana zunubanmu, kuma ka kankare miyagun ayyuka daga garemu, kuma ka karbi rayuwarmu tare da mutanen kirki.
"Ya Ubangijinmu! Ka bamu abin da kayi mana alkawari a kan manzanninKa, kuma kada ka tsoratamu a ranar kiyama, lalle ne kai, ba ka sabawar alkawari.”

10. "Ya Ubangijinmu! Mun zalunci kanmu, kuma idan baka gafarta mana ba, kuma kayyi mana rahama, hakika, muna kasan cewa daga masu hasara.”

11. "Ya Ubangijinmu! Ka da ka sanya mu tare da mutane azzalumai.”

12. "Ya Ubangijinmu! Ka zuba hakuri a kammu, kuma ka kashemu muna musulmai.”

13. “Ma’Ishina Allah ne. Babu abin bautawa face shi, a gare shi nake dogara, kuma shi ne Ubangijin Al’arshi mai girma.”

14. "Ya Ubangijinmu! Kada ka sanya mu fitina ga mutane azzalumai. Kuma ka kubutar da mu domin rahamarka, daga mutane kafirai.

15. "Ya Ubangijinmu! Lalle ne ni, Ina neman tsari daga gareka da In tambayeka abin da ba nida wani Ilmi a kansa. Idan baka gafarta mini ba, kuma kayi mini rahama, zazn kasance daga masu hasara."

16. "Ya Ubangijinmu! Ka sanya ni mai tsayar da Sallah. Kuma daga zuriyata.
"Ya Ubangijinmu! Kuma ka karbi addu’ata."

17. "Ya Ubangijinmu! Ka yi gafara gareni, kuma ga mahaifana, kuma da muminai, a ranar da hisabi yake tsayawa."

18. "Ya Ubangijinmu! Ka shigar da ni shigar gaskiya, kuma ka fitar da ni fitar gaskiya, kuma ka sanya mini daga gunka, wani karfi mai taimako."

19. "Ya Ubangijinmu! Ka bamu wata rahama daga gare ka, kuma ka saukake mana (samun) shiriya daga al’amarinmu."

20. "Ya Ubangijinmu! Ka buda mini kirjina.
Kuma ka saukake mini al’amarina
Kuma ka warware mini wani kulli daga harshena
Su fahimci maganata”

21. "Ya Ubangijinmu! Ka kara mini Ilmi.”

22. Babu abin bautawa face Kai, tsarki ya tabbata a gareka. Lalle ni, na kasance daga azzalumai.

23. "Ya Ubangijinmu! Kada ka barni makadaici alhali kuwa kai ne mafi alherin masu gado."

24. "Ya Ubangijinmu! Ina neman tsarinKa daga fizge – fizgen shaidanu.”
Kuma ina neman tsarinKa Ya Ubangijina! Domin kada su halarto ni.”

25. "Ya Ubangijinmu! Munyi Imani, sai Ka gafarta mana, kuma Ka yi mana rahama, kuma Kai ne mafi alherin masu tausayawa."

26. "Ya Ubangijinmu! Ka yi gafara kayi rahama, kuma Kai ne mafi alkhairin masu rahama."
ADDU’A DAGA HADISAI

KAFIN SHIGA MAKEWAYI
·         Da sunan Allah
Ya Allah Ina neman tsari daga sharrin aljannu maza da mata

BAYAN FITOWA MAKEWAYI
·         Gafarar Ka

IDAN ZA’A FARA ALWALA
·         Da Sunan Allah
IDAN ANKARE ALWALA
1.      Na shaida babu abin bautawa sai Allah, Shi kadai bayada abokin tarayya, kuma na shaida Annabi Muhammad bawan sane kuma manzonSa ne.
2.      Ya Allah! Ka saya ni cikin bayinKa masu tuba, kuma ka sanya ni cikin bayinKa masu tsarki.
3.      Tsarki ya tabbata ga Allah da godiyarKa. Na shaida babu abin bautawa sai Allah. Ina neman gafararKa, kuma Ina tuba gareka.
IDAN ZAKA FITA DAGA CIKIN GIDA
1.      Da sunan Allah
Na dogara ga Allah, babu karfi babu dabara sai ga Allah
2.      “Ya Allah! Ina neman tsarinKa kada nabace ko nabatar, ko nayi talallabiya ko in talallabiyar, ko nayi zalunci ko a zalunceni, ko najahiltar ko a jahilceni.
IDAN ZA’A SHIGA GIDA
·         Da sunan Allah muke shiga kuma da sunan Allah muke fita kuma ga Ubangijinmu muka dogara.
IDAN ZA’AJE MASALLACI
Ya Allah Ka sanya haske a cikin zuciyata, kuma ka sanya haske a cikin halshe na, kuma ka sanya haske a cikin jina, kuma da gani na, kuma ka sanya haske daga bayana, da gabana, kuma ka sanya haske a karkashi na, ya Allah ka bani haske.
IDAN ZA’A SHIGA MASALLACI
Ina neman tsarin Allah Maigirma, kuma fuskar sa alfarma ce, mulkinSa dadadde ne, daga shaidan tsinanne. Da sunan Allah, tsirada aminci su tabbata ga manzon Allah. Ya Allah ka bude mini kofofin rahamarKa.
IDAN ZA’A FITA MASALLACI
Da sunan Allah tsira da aminci su tabbata ga manzon Allah; Ya Allah ka tsare ni daga shedan jefaffe.
BAYAN KARE SALLAH
1.      Ina neman gafarar Allah (3)
-          Ya Allah ! Kai ne Aminci (Assalamu) kuma gareKa aminci yake, Ya ma’abuci girma da karamci kayi albarka.

2.      Babu abin bautawa sai Allah shi kadai baya da abokin tarayya. Mulki da godiya duk gareshi yake, kuma shi mai iko akan komai. Ya Allah bamai hanawa ga abinda Ka bayar kuma ba mai bayarwa ga abin da ka hana.

3.      Babu abin bautawa sai Allah Shi kadai, bashida abokin tarayya, mulki da godiya gareshi suke, kuma shi mai ikone akan komai, babu karfi babu dabara sai Allah kuma bama bautawa kowa sai shi kadai, ni’ima da falala da yabo kyakkyawa ga Allah suke, babu abin bautawa sai Allah, muna tsalkake addini koda kafirai sunki (basaso).

4.      Tsarki ya tabbatarma Allah,
Godiya ta tabbatarma Allah,
Kuma Allah maigirma (3)
-          Babu abin bautawa sai Allah Shi Kadai, ba yada abokin tarayya mulki da godiya gareshi suke, kuma shi mai ikone akan komai.


5.      Suratul Ikhlas
Suratul Falk
Suratul Nas
-          Sau uku uku bayan Sallar asuba da magariba amma sau daya bayan sauran salloli
6.      Ayatul – Kursiyyi
7.      Babu abin bautawa sai Allah shi kadai bashi da abokin tarayya, mulki da godiya gareshi suke, shi ke rayarwa kuma shike kashewa kuma shi mai ikone akan komai.
8.      Ya Allah Ina rokonKa Ilimi mai amfani da arziki mai kyau, da aiki karbabbe. (Bayan an sallame sallar Asuba)
ADDU’A BAYAN AN TASHI DA KWANA
1.      Mun wayi gari, kuma mulki ma ya wayi gari yana mai tabbata ga Allah. Dukkan yabo ya tabbata ga Allah. Babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Mulki ya tabbata gareshi, kuma shi mai iko ne akan komai. Ya Ubangijina! Ina rokonKa alkhairin da ke bayanta, kuma ina neman tsarinKa daga sharrin dake bayanta. Ya Ubangijina! Ina neman tsari da Kai daga Kasala (Lalaci) da Mummunan tsufa. Ya Ubangijina! Ina neman tsari da Kai daga azaba acikin wuta, da kuma azaba a cikin kabari.