...MABUDIN WAHALA






























Sharahbil M. Sani
E-mail:sharhamak@yahoo.com
sharha089@gmail.com
08103139272

Copyright © 2010 Sharahbil Muhammad Sani
Hakkin Mallakar © 2010 Sharahbil Muhammad Sani
An fara bugawa November, 2010
Hijri Dhq, 1431/27































GODIYA
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah (S.W.A) mai kowa mai komai wanda ya sanya soyayya a tsakanin jinsi biyu na kowa ce halitta, Allah ka dada tsira ga shugabammu Annabi Muhammad (S.A.W) da alayensa da sahabbansa da duk wanda ya yi riko ga tafarki na gaskiya alqur'ani har izuwa ranar sakamako.

*****       *****       *****
SADAUKARWA
Ga Mahaifana ina rokon Allah ya kare ku daga sharrin masusharri, da kuma mahasada. Daga karshe ina rokon Allah (S.W.T) da ya jikan dukkan wadan da suka riga mu gidan gaskiya tin daga lokacin baban mu annabin mu Adam (A.S) har ya zuwa ranar sakamako, mukuma idan har ta mu ta zo Allah ya sa mucika da imani, ameen.



















DOKA
Ba'ayarda wani ko wata ya yi umfani da wannan littafi ko wani sashe daga cikin wannan littafi ta ko wace sigar sai tare da izinin marubucin wannan littafi Sharahbil M. Sani Makera, aki yaye. 

*****       *****       *****

FADAKARWA
Wannan littafin ba'ayi shi don cin zarafin wani ko wata ba, idan har ya yi dai-dai da irin halin da wani ya ke aciki ayi hakuri, wannan kagaggen rubutu ne, daga mai kaunar ku a kullum Sharahbil Muhammad Sani Makera

*****       *****       *****
JINJINA
Gareka Malam Kasim da fatar Allah ya bada nasara ya kuma kara taimaku a cikin a yukkan ka, ameen. Ina mai jinjina a gare ki ‘yaya ta Saratu M. Sani Marubu ciyar Littafin Rashin Sani, Allah ya kara basira, ameen.        
Jinjina ta agareku abokai na Uzairu Bello Gohe, Nazir Muh'd, fata na Allah ya kara kulla soyayya a tsakani, ameen summa ameen. Jinjina ta a gare ku Masoya wa’anda dana sani da kuma wa’anda ban sani ba ina mai fatan alfahari a koda yaushe Allah ya bar mu'atare ya kuma kara kulla soyayya a tsakanin mu, ameen.
KADUNA STATE
Alhaji hakan sam bai dace ba, har ace lokacin fitar da hakken Allah ya yi ka kasa fiatar da wannan hakken, wanda yake tsakanin ka ne da Ubangijin da ya halittakane, matar Alhaji Musa ce ke wannan jawabin a gareshe.
        Alhaji Musa ya ce “ke Hajiya Salima ya ka mata idan har zaki yi magana kisan irin wanda ki ke yi, domin baki isa har kice zaki azani a hanya ba, don baki da isashshen hankali har ni zaki zo kina gaya man irin wannan magan ganun, to wallahi kishiga taitayin ki ni na ke auren ki bake ce kike aure na ba, kina jina? Don haka ina mai kara sanar dake da cewa idan har wannan maganar ta sake fitowa abakin ki to shine zai iya zamowa sanadiyar rabuwar auren mu nagaji da irin wannan zancen, bara na tambeki, ke ce ki ke nema man kudin da nake da su? wannan ma ai rainin hankali ne.
Rufe bakin sa ke da wuya hajiya salima ta ke cewa “Alhaji ina mai sanar da kai dukiya lallai bani ce na baka ba, Ubangiji Allah shine ya baka, kuma shine ya umurci dukkan wanda ya baiwa hali da ya fitar da zakka, ma'ana yabaiwa talakawa wadan da bai hore wa ba wani kason daga cikin dukiyar sa.
        Fadan wannan Alhaji ya fusata, a fusace ya ke cewa “lallai ke nuna man cewa ke kin isa, to tinda harke isa, nayi miki saki uku, naso ace za'aiya haura ukun, wallahi da zan haura hakan, kuma   kada ki yarda na dawo a gidan nan na sameki aciki, domin ina kyautata zaton bana ubanki ba ne.
        Hajiya salima sam bata ce masa uffam ba, nan ta ke ta shiga daki ta dakko mayafinta, ta saka kamun ta fita ta ke cewa “Alhamdulillah Allah ina mai godiya a gareka, da kafitar dani daga a cikin wannan la'antaccen gidan” cikin fushi Alhaji Musa ya ke cewa “gidan na wane la'antaccen,? “Eh! mana ai wannan gidan zaman sa ba'abinda ya ke haifarwa dan adam sai la'anta da tsinuwar mala'iku, ba anan kadai ta tsaya ba hajiya salima ta sa ke da cewa “Musa! ka yi gudun ranar da Ubangiji Madaukakin Sarki zaiyi nashi ikon zuwa a gareka, kana gani ne kamar bayan da za'ayi dukiyan na ka  kare ne? ko kuma ka na ganin kaine ka baiwa kanka dukiyar? Lallai ka yi wauta, ina mai sanar da kai cewa wallahi duk wanda Allah ya baiwa dukiya, Allah zai yi masa bin cike daga cikin dukiyar da ya bashi, lallai shi Ubangiji mai hakurine ga duk izgilin da bayinsa su ke yi masa, ina mai kara sanar da kai da cewa, shi Allah yakan azirtar da wanda ya so, kuma ya hanawa wanda ya so, idan kuma har ya ga dama ya karbewa wanda ya baiwa.
        Lallai ka yi kuskure mai girma duk wani abinda ka tara bazai yi tasiri agareka ba a ranar da ubangijin ka zai yi bincike akanka. A fusace Alhaji Musa ya taso da karfi daniyar kaimata mari, cikin zaugawa ta ce ke cewa “me zaka yi wallahi idan har ka tabani sai ka gane cewa kai ba kowa bane, ka sakeni ai ba kada iko dani a halin yanzu” Alhaji Musa ya ce “Wallahi keyi arziki” wani dogon tsaki taja, ta ce “ai dama Allah ya halittani da arzikina, ba a gidan ka nasame shiba” Alhaji Musa ya ce kije dukkan kayan da kika zo dasu ki kwashe su gabadaya.
Hajiya Salima ta ke cewa “dame nazo? ai ni kaga wadannan da kagani ajikina sune na zo da su, me zanyi da kayan matsiyaci? Alhaji Musa sam ya kasa ya ce komai.
Hajiya Salima ta fita zuwa gidan su, ta bar Alhaji Musa a tsaye ya na faman sabbato ya na cewa “yau kaji man wani zance idan harba ta raina ni ba ya zata dameni da wani zancen kawai, waini na bada zakka naki na bada, haka kawai zan dauki dukiya na baiwa wani katon banza wanda baisan irin wahalar da nasha ba har na sami wadannan dukiyar ba, shi talakan kada ya tashi ya nema ya zauna ya na jawa kansa, ai kuma   bani na ce kar ya nema ba, ni kuma   don ina gara sai na dauki dukiya na baiwa wani katon banza, kai amma wannan ma rainin hankaline.
Alhaji ya fito ya shiga motar sa deraba ke tuka motar.
Kyakkyawar yarinya ce ke tafiya, yarinyar wacce ta ci sunan ta Samira tana sanye da tufafi abin ban sha'awa yarinyar ta rufe dukkan jikin ta da gyale, domin har a kasa ya ke, tana sanye da takalma ta gwanin ban sha'awa duk da ya ke (plat) ne, da kagan ta kaga wacce ta san addini, yarinyar ta na tafiya a kan hanya ne, direban Alhaji ya kawo dai-dai ga wannan yarinyar, direban ke kokarin wuce wa, nan ta ke Alhaji ya hange ta, cikin hanzari ya ke cewa direban ya tsaya ba musu direban ya tsaya Alhaji Musa ya saukar da glass din motar yana cewa “yarinya don Allah salamu alaikum, jin hakan Samira ta karba zato ta ke bakone zaiyi tambaya ne, tadan tsaya domin ta ji irin zance da ya zo dashi.
Alhaji ke cewa “don Allah yarinya ya sunan ki?” ba tare da ta bashi amsar tambayar sa ba ta ke cewa “me kuma   za'kayi da sunan nawa?” Alhajin ya mayar mata da amsar ta da cewa kamar ya me zanyi da sunanki, idan har bazan yi wani abin da sunan naki ba, ai bazan tambeki ba. Samira ke ce masa “sunana Samira, Samira ta bashi amsar dukkan tambayar da ya yi ma ta Alhaji Musa ya cewa direban ya ja mota su tafi direban ya ja motar suka tafi. Samira dai ta bashi amsar tambayoyin da ya yi ma ta ba tare da sanin meye asalin dalilin yi ma ta wadannan tambayoyin ba, Samira ta juya ta tafi abinta.
Direban ya kawo dai-dai kofar gidan da isar sa ya faka motar da sauri ya fito ya bodewa Alhaji kofar motar Alhaji Musa ya fito da fitowar sa ya tunkari shiga a cikin gidan kamun ya shiga ya yi sallama Assalamu alaikum mahaifiyar Samira ce ta amsa masa, ameen Hajiya Sakina ta fito dumin ganin wake sallama, fitowar hajiya sakina, tagan mutun a cikin gidan duk da ya ke sam bata waye da shi ba, Hajiya Sakina ta yi masa maraba ta ke cewa “barka da zuwa shigo mana cikin fara'a ta ke cewa “ga wuri ka zauna ta dauko tabarma ta shimfida masa Alhaji Musa ya zauna ita kuma ta nemi kujera ta zauna, domin jin irin wacce ya zo da ita, bayan gaisawa nadan lokaci, Alhaji Musa ya sanar da ita sunan sa, yana mai cewa “sunana Alhaji Musa da kuma   dalilin shigowar sa,  “wata yarinya na gani ta nuna man nan ne gidan su ni kuma sai naga ya dace na zo tun yanzu na sanar da Mahaifanta… jin hakan Hajiya Sakina ta fahimci inda maganar sa zata dosa ga abin da Hajiya Sakina ta ke wace “kasanar da mahaifanta me? to bara in sanar da kai yarinya tana da wanda zata aura, amma ka bani mamaki tsofai-tsofai da kai har zaka zo ka iya furta wannan zancen, baka jin kunya? yau naga tsoho da budurwar zuciya, kai! amma kayi tsofan banza, don Allah bai halittaka da alkunya ba sai ka shigo har cikin gidan.
Wallahi ni na dauki cewa kakan Abban Malam ne ya dawo domin tin yana saurayinsa ya bar gida bashi ba labarinsa, ta sake da cewa “To wallahi kayi sauri kabar gidan nan, tinda sauran mutunci, ai wannan rainin hankali ne da kuma rashin tinani. Ganin wannan cin mutuncin da Hajiya Sakina ta ke masa, Alhaji Musa ya tashi ya kama hanyar fita sai ya dawo ya zaro kudi dauri biyu na dubu daya-daya yana mai cewa “Hajiya kiyi hakuri wannan kuskure ne, insha'allahu zankiyaye, amma ga wannan ayi hakuri, Alhaji Musa ya bata wadannan ma kuddan kudi, nan ta ke ta sauko tana cewa “ai ba kaine kayi kuskure ba, nice nayi babban kuskure, don Allah kayi hakuri nayi wannan ne cikin rashin sani, Hajiya Sakina ta sake da cewa “lallai kaine wanda ya kaine wanda ya kama ta abaiwa Aminci.
Alhaji sam bai sake cewa uffan ba, amma sai dai azuciyar sa yake cewa “lallai kwadayi mabudin wahala, alhaji ya hau hanyar sa ya fita, Hajiya Sakina ta bishi domin taraka shi tana mai cewa Allah ya kiya ye kaji dan halal, idan Samira ta zo zan sanar da ita yanda mu kayi da kai. Alhaji Musa dai sam bai sake cewa uffanba, yabarta tana faman surutai. Sam yaki da ya ce komai, da isar sa direban ya bude masa kofa alhaji ya shiga motar nan take direban ya yi ribas ya fita acikin gidan, ita kuma Hajiya Sakina ta tsaya a kyawren gidan tana mamaki ta dan jima a tsaye can Hajiya Sakina ta ke cewa “dayar dan Allah Samira sai ta auri wannan mutumin, a'ah kaji man mutum, ni na haushi da faman fada amma shi kaga alhairin da ya saka man dashi, nan ta ke ya azirta ni, ta ci gaba da cewa “lallai kan sai inyi zance kara komawa hajji tin ba'a fara samun miskila a wannan harakar ba.
        Hajiya Sakina ta juya zuwa a cikin gida dashigar ta ta ajiye kudi a kan tabarmar, Hajiya Sakina ta mike a tsaye ta dinga gwabzar rawa tana cewa, “Allah ya yi ruwa tsiya ta wanke, ta dai ci gaba da zantuna irin nata, tana acikin wannan yanayin ne Mal. Manir ya dawo daga kasuwa da shigowar sa ya ke cewa “Assalamu alaikum, a firgice ya ke fadan cewa “hajiya lafiya” haka Hajiya Sakina ta dauki kudi ta dinga zuba mar aka, Mal. Manir kuma ya ga wannan abin ya yi yawa tana ta watsa kudin amma kamar ba zasu kare ba, shima ya bita yana bankar rawa can! Mal. Manir ya tsaya cikin fara'a ya ke cewa “wa ya kawo man wadannan kudin? abin da ya tambiye Hajiya Sakina kenan, jin ya ce hakan hajiya Sakinat ta tsaya ta na mai cewa “kamar ya wa ya kawo maka kudi”? ta kuma   sake da cewa “wa ka ajiye wanda zai kawo maka kudi”?. Jin wa'annan magan ganun Malam Manir ya ke cewa “to ai wannan tambaya ne, ko ban da incin yin tambaya kuma? Hajiya Sakina ta zauna ta ce da mijinta “Malam zauna yanzi ka sha labari da gaugawa Mal. Manir ya zauna Hajiya Sakina ta kwashe labari duka ta bashi hakan yasa dukkan jikin Malam ya yi sanyi, Mal. Manir ya ke cewa “Hajiya ki na ganin wannan abin bazai zamu illa agaremu ba? kamin ya sa ke dura wata maganar ta sharbe shi da cewa “wace illa malam”? ai wannan bazan cen illa a cikin sa, haba malam, ai again na da muba da 'yar mu ga wanda ya ke yanzin ne ya ke kokarin tasowa ai gwanda mubada ita ga wanda yake ya taso, kada ma ka yi tinanin wani illa acikin wannan al'amarin.
Malam Manir ya ke cewa “Hajiya ki tinafa ke san zancen wannan yaron Mukhtar  alkawari ne, idan har muka kauda wannan ina ganin ai baza abauke mu da mutinci ba, kuma za'a dauke mu dacci jan banza, gaba daya mutincimmu zai zibe a idon mutane, ke ga hakan sam bai dace ba, ace gudan ni limamin unguwar nan hakan ya kasan ce da ni.
Alhaji saurara kaji yanzin nan ai hakan ake yayi kuma shine ake tunkaho dashi, idan yarinya ta sami masu son ta za'a dubi wanda yafi tsoka abashi, idan kalura Malam Siddi 'yar sa, Larai tana da masu son ta da ya wa da ya tashi yi ma ta auren, wanda ya zo daga baya shi ya aurar ma ta da shi, idan ka lura to ai yafi kudi a cikin su.
Hakan tayi ta yi masa har ta ciwo kansa ya yarda a aurar da ita ga Alhaji Musa.
Ganin hakan Hajiya taji dadi, har ta ke cewa “duk da ya ke baice nabaka ba, amma ga dauri daya karika”, Malam ya yi murmushi ya ce wallahi ke kyauta dalilin da ya sa ki ke kara burgeni ke nan da tini nay miki kishiya amma ke ga ganin kina yi man hakan na kasa da na kara wata matar, Hajiya Sakina tayi dariya ta ce “Malam ai dole ne nayi ma, idan har banyi ma ba, to wazan yiwa?
Malam ya karbi kudin daga hannin ta ya saka aljihu ya ce “Bara infita in samo mana ko dan balangu mudan mutsa baki, kesan yau watammu tara bamu sa nama abaki ba, tin ranar sallah da makotan nan namu, Alhaji Idris da ya aiko mana da layyar da ya yi. Hajiya Sakina dai murmushi ta yi ta ke cewa “to ai ka ga idan har mun aurar da samira ga wannan attajirin ai kaga dule ne ababen su canja, ya yi murmushi, hajiya sakinat ta ke cewa “Allah kiyaye sai ka dawo Malam, malam ya ce ameen sannan ya fita.
Samira ce ta dawo a inda Hajiya ta aike ta, da shigowar ta sallama ta yi, Sallamu alaikum kamin ta zaun ta ce Umma na dawo kuma wallahi Hajiya ta ce bata da kudi gaba daya kan hakan ma yau ba su yi girki ba.
Cikin fara'a mahaifiyar Samira ta ke cewa “amma baki lura a  inda ki ke a zaune ba? Samira ta ce menene? da sauri ta tashi ta mike a tsaye domin ganin me ke faruwa, daga tashin ta taga kudi zube akan tabarma, Samira ke tambaya “Umma ina ki ka samu wadannan makodan kudin a zube hakan? Umman ta bata amsa da cewa “mai sonki ne ya bani su” jin hakan Samira ta dan tsorata, ta ce “wane mai sona kuma ko Mukhtar ? domin ni Mukhtar  ne kawai na sani, Hajiya Sakina ta ce ke ki ka san wani Mukhtar , wannan wani shalele ne, abin son kowa, kina jina?, wani Alhaji ne ya zo ai ya ce ya ganki akan hanya ya kuma ce ke ki ka sanar da shi gidan nan, kuma   ya sanar dake komai.
Samira yi farat ta ce “ni ban hadu da kuwa akan hanya ba, sai wani tsoho da ya ganni ya ke tambaya ta wai ni 'yar gidan wa nake ni kuma nasanar da shi. Samira ta kwashe labari du ka ta sanar da mahaifiyar ta Hajiya Sakina ta ke cewa “to ai wannan shi ne ya zo gidan nan, kai amma mutumin ya na da kudi sosai fiye da yanda zaki yi tsammani, ta sake cewa ai har mun yanke shawara shine wanda muka ba, ma'ana shine wanda zaki aura. Cikin firgita Samira ta ce “kuka bawa? Ni wallahi bana son sa, Mukhtar  nake so dumin Mukhtar  ne amintacce acikin zuciya ta, kuma shi na baiwa dukkan mabodin kofofin zuciya ta. Nan ta ke Hajiya ta dau ke Samira da mari ni zaki gayawa irin wannan maganar don baki da kunya, duk da ya ke rudewa ne yasa Samira ta yi wannan zance jin cewa ba zata auri Mukhtar  ba, Samira ta tashi ta shige a daki a fusace, Hajiya Sakina kuma ta dora hannun ta aka ta jijjiga kai ta na mamakin yanda Samira ke irin wannan zancen agaban ta.        
***  ***  ****
Mukhtar ne ke tafiya akan hanya ya na ta re da masoyiyar sa Samira, su na tafiya ne, su na tadi irin na masoya, lallai da ka gansu kaga masoyan da suka shaku da juna sosai abin ba'a cewa komai. Mukhtar yaro ne mai kimanin Shekara a Shirin da biyar, yaro ne wanda ya ke da siffa irin ta Larabawa, idan har ka ganshi kace Balarabe ne, a lokacin ne suka isa a wani kanti wanda ake sayar da kayayyaki iri daban-daban (Botique). da isar su mutanen da ke gurin ke kallon su dominirin burgewa da suke da shi, wanda dukkan masoya sun su ace za su kai a wannan matsayi.
Da shigar su Mukhtar ne ya hango wadan su tufafi abin ban sha'awa ga dukkan macen da ta saka su, Mukhtar  ya nuna wa Samira tufafin, nan ta ke suka isa a gurin da kayan suke, ya dakko wa'anan tufafin yana nuna wa Samira, samira ta ke cewa “kai! amma ka'iya zabe ai wannan sai ya mai dani kamar bani ba”, Mukhtar ya dan yi murmushi a lokacin ne ta dan tsaya na dan lokaci ta na kallon sa dominmurmushin sa ke kara sa taji ba wani sai shi. Daga nan suka isa a sashen da ke da agogon hannu da gilasai, Samira ta zabo wani agogo wanda ya ke da bansha'awa ta baiwa Mukhtar , Mukhtar  ya karba, ta sa ke zabo wani (glass) na Ido ta baiwa Mukhtar  bayan ya karba ta ke cewa “kai amma wannan sai ya yi kyau a gareka domin na fararen mutanene wannan” Mukhtar  ya yi murmushi ya ce amma ke iya zolaya, Samira ta ce ai wannan ba zance zolaya. Daga nan suka je suka biya kudin kayan da suka saya.
Da fitar su cikin (Botique) sun dan taba tafiya domin har sunyi nisa a gurin, sai ga wata dankareriyar motar ta faka a gabansu mai kirar (Judgement day 21306), a dai-dai lokacin ne wanda ke cikin motar ya dan saukar da (glass) din motar ya ke cewa “Samira ki saurareni ko na minti daya ne. ko da Samira ta ganshi sai ta sa dogon tsaki ta juya baya ta cigaba da tafiyar ta, to koda Mukhtar   ya ga mutumen nan wanda ke a cikin motar ba yaro bane, sai ya zata wani kawun ta ne, sai ya ce Samira ana magana da ke keki ki saurara, ke san ko sako zai baki zuwa ga Abba kokuma Umma, Samira ta yi kamar Mukhtar  ba da ita ya ke magana ba.
Da Alhaji yaga babu sarki sai Allah nan ta ke ya tuka motar sa ya zarce sai gidan sa, da shigowar Alhaji a gida ya tarar da yaron sa Gali yana zaune akan kushin, Alhaji ke cewa “Gali wannan al'amarin ke bani mamaki, me yarinyar nan ke nufi ke nan, har ina ma ta magana amma yarinyar ko kallo na ta ki tayi, dan haka wallahi dole ne sai na dauki mataki akan wannan yaron Mukhtar  na rabashi da wannan yarinyar Samira har yarinyar ke nema ta raina man da hankali”.
Gali ke cewa “kasan lamarin mata yan da su ke, Alhaji idan har mai hankali ce ya za'a yi har ta tsaya ta saurari wannan yaron, kasan tinanin nasu kadanne, har a baiwa mahaifin ki manajan wadan su kamfonnan daga cikin manya manyan kampanoni, amma baza ta duba ba.
To ai shi nagani wanna yarinyar sanadiyar ta ce na sayawa mahaifin ta gida, wanda ya ce ko ni sam ban zauna acikin sa ba, badan komai ba sai kawai dan ina son ta.
Wallahi kasan cewa ko zakka bazan iya fitarwa, don kada wani ya ci a bisa dani, amma kaga rana tsaka na baiwa mahaifin ta mota na bashi gida, badan komai ba sai dan na sami nasara ga auren wanna yarinyar Samira, amma naga tana man wani kallo akan wanda sam bai wuce a gama da shi a cikin lokaci daya ba.
        Wallahi ko ta halin ya sai na auri Samira idan kuma ba haka ba mahaifan ta zan wulakantasu, in kuma hallakar da su ga baki daya domin hausaw na cewa kwadayi mabudin wahala, don haka idan ba haka ba kashe su, gaba daya a cikin fushi Alhaji Musa ke wannan zance.
***  ***  ***
Samira da Mukhtar  kuma sun isa a gida, suna zaune ne akan table a cikin wani lambun da ke acikin gidan na su Samira, suna zance irin nasu na soyayya, Samira ke cewa “Mukhtar  ka dauki wani alkawari wanda ya ke duk kan halin da nashiga idan har na tina wannan zan sami wani sarari acikin zuciya ta. Mukhtar   ke cewa “Samira ina mai sanar da ke cewa na dauki alkawari bawani abin da zai sa na daina sonki, Samira  ina mai kara sanar dake kaunar ki ce kadai azuciya ta, kuma   ke ce insha allah wacce zata zamu mata agareni.
Samira duk wani hali na kuncin da zanshiga/nashiga bazan taba mantawa da ke ba ke kadai ce na baiwa Aminci”
Samira ke ma ki gaya man abin da zaisa naji sanyi azuciya aduk lokacin da na shiga wani yanayi na halin kunci dab akin ciki a soyayya.
Samira ke cewa “Mukhtar a koda yaushe kaine wanda zuciya ta baiwa kauna, kaine nake so akowane irin hali na shiga Mukhtar har abada ina mai sanar da kai ko mutuwa bazai sa nadai na kaunar ka ba, idan har ba kai ba nadauki alkawarin cewa bazan aurin kowane da namiji ba.

Mukhtar badan saurari ko wane da namiji ba sai kai. Mukhtar kaine wanda zuciya ta bodewa kofar Aminci”
Hajiya ce ta same su a lokacin da suke wannan zance hajiya ta ke cewa “lallai zuciya a yan zin nan ne ta rufe kofar Aminci” ta sa ke da cewa “amma kai wai shin bara in tambeka, amma uban ka Alhaji Kabir ya yi zama a gareji ku? don da anga fuskar ka anga mara mutinci, mara tarbiya, alamun ka kana shaye-shaye, “To wallahi idan har baka da masaniya to kasani, yarinya tana da mijin aure ba irin ka ba, wanda ya yi gadon tsiya tin a guri kakanni, kuma na baka 'yan mintina ka tashi ka fita a gidan nan tinda ba gidan uban ka bane. Mukhtar  ya tashi ya kama hanya zuwa fita, Samira ta rike hannin sa tana mai cewa “Mukhtar  ina zaka je dan Allah kada ka barni” Hajiya Sakina da sauri ta bige hannin Samira tana mai cewa “kaji man rashin hankali yarinya ke ne man ta mayar da magana ta maganar kawai, Hajiya ta jawo Samira, Samira ke ko karin ta je gun Mukhtar .
        Mukhtar  ya fita ya bar Samira acikin tsananin damuwa, duk da ya ke baya neman wani abin da zai ta ba Samira, bale damuwar ta, ba tare da jin dadi ba, Mukhtar  ya bar gidan su Samira, dalilin wa'annan kalaman da Mahaifiyar Samira ta gaya masa.
        Ya isa a gida ba, tare da ya na mai jin kansa kamar yanda ya ke ba, Mukhtar  ya zauna acikin wani babbam falon da ke a cikin gidan nasu, ya na tuna wa'annan miyagon kalaman da Hajiya ta gaya masa.
        Mahaifiyar Mukhtar  ce ta shigo a cikin falon, sai faman kiran kiran sa ke Mukhtar , Mukhtar , Mukhtar  sam Mukhtar  baiji kiran da mahaifiyar sa ta ke masa ba. Hajiya Karima ta iso kusa ga dan ta Mukhtar  ta na cewa “lafiya Mukhtar  a lokacin ne Mukhtar  ya lura da mahaifiyar sa ke mishi magana, Mukhtar  ke cewa “lafiya kalau wallahi, mahaifiyar ta ce “inafa lafiya nagan ka bayan da na saba ganin ka ba”, ba komai Mom “to idan dai har ba za ka gayaman ba bari in kyaleka, idan dinge ya fashe ai aji wari, murmushi ya yi, ita kuma Mom din sa ta hau a sama, ta bar Mukhtar   anan cikin falon.
***  ***  ***
        Alhaji Musa ne ya zo agurin Samira, Samira ta fito cikin bacin rai da fito wanta Samira ta tsaya a gaban sa amma ta juya masa baya me ya kawo ka kuma  bakin maye kanka zaka ci wallahi.
        Fadin wannan maganar Alhaji Musa abin ya bashi mamaki, ya kasa da ya yi shuru, Alhaji Musa ya ce “Samira ko ke san abin da kika fada kowa?” Eh mana sai me akwai wani magana? Samira ta ke cewa “Musa ina mai sanar da kai cewa wannan abin da kake bazai taba sa inji ina sonka acikin zuciya ta ba, Musa ina mai sanar da kai wallahi a rayuwa ban da wanda nake ki kamar ka, sam ni kudin ka bazai sa na aure ka ba, idan don ka sami nasarar aurena ne ka bawa mahaifina gida to wallahi ka yi abanza, ina mai rantse maka da Allah ko kai kadai karage a fadin wannan duniya wallahi bazan aure ka ba, Samira ta yi tsaki ta juya da ta koma acikin gida Alhaji Musa ya rika gyalen ta Samira! Samira!! Sa… nan ta ke Samira ta dalla masa mari tas! ta kuma tofa masa yawu a fuskar sa, ta barshi acikin wani tsananin bakin ciki, lallai hakan ya matukar bata wa Alhaji Musa rayuwa, abin da sam ba wani talikin da taba yi masa hakan. 
        Alhaji Musa ya isa agidan, da isar sa maigadi ya bode masa (gate) Alhaji ya shiga acikin gida masu aikin gida su ka tasu cikin gaugawa nan ta ke suka bude masa kofar motar sa ya fito “sannu da dawowa” Alhaji sam bai ji abin da suke fada ba, ya shiga acikin babban falon da ya ke shakatawa, da isar sa ya tarar da babban yaron sa Gali, Gali yaron Alhaji ne amma ida ka gan su kamar abukin sa, Alhaji Musa ya zauna a kujera ya dura hannayensa a ka, Alhaji Musa ke cewa “Bazai yu ba ace wani can banza marar asali, wanda bai ta ka kara ya karya ba har ace zai rinjaye mu, wannan maganar banza ce, kamun Alhaji ya dora wani zance Gali ya ke cewa “Alhaji kada ka damu wannan ba ko mai ba ne, dominni ban dauke shi wa ni doguwar matsala ba.
Kamar ya baka dau ke shi matsala ba? Ai kuwa wannan ya wuce zamu wa matsala, “To Alhaji ga wata yar shawara wacce zan bayar. Alhaji ke cewa “wacce shawara kuma duk abin da zaka ce ni nariga na yi tinani ba zai yu ba”, “ka dai tsaya ka saurareni Alhaji” “To ina jin ka”.
Yaron Alhaji Gali ya ce Alhaji shawarar ita ce ka na ganin baza'a hada shi da haya (killers) 'yan Fashi da su hallakashi ina jin kamar wannan ne ka dai maganin wannan matsalar. Alhaji ya yi shiru na tsawon lokaci, jim kadan, sai Alhaji ya ce “to maji wannan, idan har an salwan tarda rayuwar sa ai so ya nanan, wallahi ni a gani na ba wani hanya wacce zai sa wannan yarinyar ta soni, Gali ke cewa “Alhaji sam wannan ba shi bane, abin tinanin ba, abin da zaka yi la'akari da shi shine, idan har kasa aka yi masa wannan, shi zai sa ka sami damma na ciwo kanta, da kuma sauka kawa agurin iyayen ta, idan har ya mutu dole za'a aurar da ita agareka ba, domin iyayen ta baza su zauna da ita acikin gida ba. “Eh! In ji Gali amma ai ma'iya samun nasara idan har muka samu hadin kan iyayen ta ko ta so ko kar ta so wannan ya zama tilas agare ta sai tayi, Alhaji ya ce “eh! Hakanne fa, amma akwai ka da zurfin tunani wallahi, Gali dalilin hakan na ke son ka fiye da dukkan yara na.
Bayan kamala dukkan shawarwarin da su kayi Alhaji ya ke cewa “ai wannan ba abin wasa ba ne ka yi sauri ka je ka kira wa'annan mutanen domin wannan aikin ina son ayi shi tin a yau, ba na son ya kwana a doron kasa.
Nan da nan Gali ya fita dominya cika umurnin da alhaji ya bashi, ma'ana ya zo da wa'annan miyagun mutanen.
Da fitar sa bai dauki wani tsawon lokaci ba, nan ta ke Gali ya dawo tare da haya killers, da shigar sa ya tarar da Alhaji ya na mai cewa “to Alhaji ga su nan na zo da su, Alhaji ya ke cewa “lallai Gali ka yi ko kari, domin ka cika aikin ka, duk da ya ke Alhaji ya na sama, 'yan fashin gaba daya a tsaye su ka yi sun jera wani layi ka ce sadaka za'a ba su.
Nan ta ke sai babban ya ce “Alhaji menene matsalar ka yanzinnan zamu ya ye ka daga cikin ta ha! ha!! ha!!!.
Alhajin ya ke cewa “abin da na ke so shi ne, ina son ku hallaka man da wani dan iskan yaro wanda ke so ya ga ya kada ni, lallai ni nasan karyar sa, ya ce har zai ja dani, ina so ne kura bashi da rayuwar sa, bana so na sa ke jin duriyar sa a cikin wannan duniya”. Nan da nan shugaba da ga cikin wa'annan haya killers ya yi wa ni dan murmushin ke ta ya na mai cewa “Alhaji jingar mu shi ne million hamsin”, Alhajin ya bude bakin sa yana mai cewa “sam sam wannan ba matsala ba ne, ku cika aikin ku ka da ku damu, ya dakko kudi naira million arba'in ya ba su, “ga wannan ku fara aikin” fadan Alhaji ke nan.
Da fitar su Gali ya nuna masu hanyar da ya yawaita biyowa idan har ya dawo da ga makaranta.
A dai-dai lokacin ne Mukhtar ya fito da ga makaranta ya na cikin motar sa shi ka dai ba ya tare da kowa nan ta ke su ka yi planning na yanda za su hallakar dashi.
A dai dai lokacin ne Mukhtar ya yi kusa da hanyar da makiyan sa su ke, Mukhtar ya shiga faduwar ga ba, a cikin zuciyar sa ya ke cewa “Kai wannan al'amarin ya ba ni mamaki, wannan faduwar gaba inajin da walakin”, da ya ke a duk lokacin da su ka ta su da ga makaranta ba shikadai ya ke dawo waba, ya kan taso ne tare da abokan sa, saboda hakan Mukhtar sam bai dauki wannan wani abin ba. duk da ya ke zuciyar sa ta radar masa da cewa hanyar ke da matsala.
Kamar ya gan su ne, nan ta ke ya yi rivers dominya chanja hanya, juyawar sa ke da wuya ya dinga jin harbi, ba, ba, a jikin motar sa, a lokacin Mukhtar  ya kara ta ke motar sa, amma ina harbin har ya kai a bagiren da suka fasa masa tayoyin mota, ba tare da wani bata lokacin ba, motar ta dinga jujjuyawa da shi har sai da ta kai shi a cikin wani babban rami wanda a ganin su duk wani mahalukin da ya fada acikin sa bashi ba rayuwar sa, a lokacin da ya fada a wannan ramin Allah mai ikon sa ne ga dukkan bayin sa, kuma   ya kan jaraba bawan sa ta ko wace irin hanya, duk da ya ke ya ji matsanancin rauni, Allah ya ba shi ikon fitowa, da fitowar sa motar ta buga bam! wuta ke tashi, a dai-dai lokacin ne miyagon suka leka ramin dominsu ga me ke faruwa, bayan sun duba su kaga ba shakka sun sami nasara, nan ta ke ogan na su ya yi irin dariyar sa, wacce ta ke firgita dukkan rayuwar dan adam.
Bayan wuce warsu zafin wutar ya yi wa Mukhtar ya wa, Allah sarki, Mukhtar , gashi a kwance domin yawan rauni gaba daya ba numfashin sa, Mukhtar  ya shiga wani mummunan yanayi. Amma zamu je a gidan Alhaji domin jin irin zancen da haya killers suka isar zuwa ga Alhajin.
'Yan fashin sun isa gurin Alhaji Musa domin shaida masa da sun gama masa aikin sa, Alhajin ya yi matukar murna fiye da yanda mai karantun zai zata, ya biya wa'annan mutanen kudin su ba musu.
Kwana da kwanaki Mukhtar sam ba numfashin sa, bayan mako biyu da wannan mummunan aika aikan da Alhaji Musa ya yi, rashin ganin Mukhtar Samira ta shiga wani yanayin mai tsananin munin gaske, yawan tinanin, Mukhtar  da Samira ta ke yi har ya jawo ma ta da wani ciwo mai tsanani.
Duk da haka iyayen Samira su suna shirye shiryen aurar da ita ake yi ga Alhaji Musa, lokaci sai matsowa ya ke domintun ranar da Alhaji Musa ya shirya da a hallaka Mukhtar da kwana daya ne aka sa ranar auren Alhaji Musa da Samira da ya ke Wata biyu ne aka aza ranar, wato ranar da za'a yi bikin auren Samira da Alhaji Musa.
Allah mai yanda ya so ga bawan sa, Mukhtar  na cikin wani yanayi wanda Allah subuhanahu wata'ala ya jarab ce, shi dashi, a dai dai lokacin ne numfashin sa ya ke dawowa ahankali Mukhtar   na cikin wa ni hali na neman taimakon Ubangijin sa.
Allahu Akbar, Allah mai yanda ya so ga bayinsa, wani mutum ne ke tafe dominjewayar gonar sa, ya na a cikin wa ta mutar mai kirar Jeep mutumin bashi kadai ya ke ba, ya na tare da direban sa, a lokacin ne Allah ya baiwa Mukhtar  ikon jan jikin sa zuwa a kan hanya da ya ke ramin na kusa ga hanya, da isowar su a kusa ga wannan rami sun yi kusa da su wuce Alhajin ya ga mutum a kwance jikin sa gaba daya a raunane, Alhajin ya bude bakin sa da cewa Innalillahi wa'inna'ilaihirraju'un subhanallah, cikin gaugawa ya ke ce ma direban sa, “tsaya-tsaya” ba musu direban ya tsaya.
Alhaji ya fito tare da direban sa a cikin kuzari dominceto rayuwa. Allah Sarki lallai shi ciwo ba mutuwa ba ne, lallai kuma Allah shine mai jinkayin bayin sa, nan da nan suka dauke shi suka sa shi a motar, direban ya shiga mota da sauri, ba tare da tsai tsayawa ba suka isa a asibiti, da isar su direban ya tsaya, nan ta ke a ka zo a ka dauke shi a cikin motar zuwa cikin dakin tiyata.
Alhajin a razane ya ke gaba daya domin ganin irin wannan aika aikan, tinanin sa accident ne, duk da ya ke ya hangi a wani gurin ma ajikin sa ammar harbi uku, Alhajin ya shiga da kan sa a cikin asibitin da isar sa likitocin gurin ke cewa “Dr. Umar lallai kai ne ka dace da ka yiwa wannan bawan Allah aiki”, Dr. Umar ke cewa “ba matsala” nan da nan Dr. Umar ya saka kayan aiki ba tare da wani bata lokaci ba.
Dr. Umar ya yi nisa ga aikin sa gaba daya an share dukkan jinin da ke ajikin Mukhtar an kuma yi masa aiki a duk inda ya dace, ba tare da an bata wani dogon lokaci ba, Dr. Umar ya kammala dukkan aikin da ya ke.
Lallai wannan asibitin shine asibitin da ya zamu abin alfahari, gasu da ma'aikata kwararru, na'urorin aiki irin na zamani lallai wannan asibitin ya zamu mai kula ga dukkan maralafiya (FMC).
Bayan kwana uku da yiwa Mukhtar wannan aikin, ya samu sauki har yakan iya dan jinginawa ya dan tashi.
Lafiya sai kara samuwa ta ke yi a gun Mukhtar wannan lamari ya zamu ikon Allah.
***   ***   ***
A bangaren Samira kuma jin an sa ranar da za'a daura auren ta da Alhaji Masu tinani ya yi zorfi a gareta, Samira ta shiga acikin wani yanayi abantausayawa, a dai-dai lokacin ne ta ke kwance acikin dakin ta, tinanin ta shine inane zata iya ta sami Mukhtar? a zuciya ta ke fadan hakan. Zuciyar ta ke nuna ma ta da cewa Mukhtar ya mutu domin tabbacin cewa Mukhtar bazai iya dauriya na mintina batare da ya ganta ba, a zuci ta ke cewa “a'a ina ganin dalilin Umma ce da ta nuna masa cewa ba zasu yarda da su aurar masa dani ba, shine dalili. A zuci ta ke cewa “to idan haka ne a gaskiya Mukhtar bai rike alkawari ba, nan da nan ta ji a zuciyar ta da cewa “lallai Mukhtar amintaccene domin Mukhtar ya ka sance mai Juriya, Rikon amana, da kuma   cika Alkawari na tabbatar cewa Mukhtar idan har yana da rayuwa akuwanne hali ya ke bazai iya juriyar awa daya da ga cikin (24 hours) awa ashirin da hudu ba tare da ya ganni ba”.
Aminci ya tabbata a gareka, Mukhtar ni Samira Insha'allahu na dauki alkawarin auren ka domin na aminta da soyayyar ka.
A wannan zance ta ke sai ta ji ana buga kwauren dakin, Samira ta tashi domin ta bude kofar koda ta duba agogo sai taga karfe goma sha biyu da rabi (12:30pm) ta buga, cikin hanzari Samira ta bude kofar, “Umma ina kwana” Samira ce ke gaida Mahaifiyar ta “Mahaifiyar ta Hajiya Sakina ke cewa “lafiya naga a yau baki yi saurin tashi daga bacci ba? gashi yanzi karfe (12:30pm) har ta buga “A'a lafiya kalau wallahi” inji Samira, Umma ta ce “Samira na san dalilin ki bai wuce tinanin Mukhtar ba, kiyi hakuri domin Mukhtar dai ya riga ya mutu kuma ba'asan inda gawar sa ta ke ba, kiyi hakuri ki amunta da Alhaji Musa mana ayi auren ku, kin ga sai kije a gidan ni'ima gidan wadata gidan da zaki ji dadin sa, ke san cewa Alhaji Masu mutun ne mai kudin gaske wanda ya mallaki dukiya fiye da yanda zaki iya tinani ke ga kuwa idan har ki ka aure shi lallai muma zamu ji dadi sosai”.
Samira ta ce “Umma a gaskiya ni bazan iya auren Alhaji Musa ba, domin tin a baya na fada ni Mukhtar   na ke so kuma ni na tabbatar cewa Insha Allahu Mukhtar   yana da ransa ba mutuwa ya yi ba, kuma   idan har Maganar kdi ne lallai nasan shi kudi Allah ne ke badashi gawan da ya so domin yi masa wata 'yar jarabawa ya ga idan har zai zamu mai godiya a gareshi.
Haka kuma idan bai baka ba shi ma lallai jarabawa ne daga Ubangiji Madaukakin Sarki, dan haka ni bazan so ku aurar dani don kudi ba, domin hausawa kance KWADAYI MABUDIN WAHALA”, Umma ta katse wa Samira hanzari, da cewa “lallai ke girma ke yi wuya ke isa yanka har zaki sani gaba kina gaya man maganganun banza, to ni zaki gayawa hakan wallahi ko ki so ko karki so auren nan kamar anyi angama, bari ma na sha'ida miki da cewa yau saura mako uku a daura auren ki da Alhaji Musa”. dajin haka Samira duk tafirgita tana mai kaskan tarda kai tana cewa “Umma ka da ku hadani aure da wanda bana so, ku tausaya wa rayuwa ta, ka da kudi ya jaku da ku aika ta mummunan al'amari, wanda daga baya zaku kasance abin kwatance a gurin jama'a, wannan sam ba mutincin ku bane, da… kai-kai-kai wuyan ki yay kauri, inji Mahaifin Samira Mal. Manir har zaki yi zaune kina ciwa uwar ki mutinci, “To Wallahi ba ki isa ba, ko ki so ko karki so, aure anyi angama, indan har baki da masaniya to na sanar da ke kinji, tashi ki ba mu wuri idan ka haifi da baka haifi halinsa ba”.
Samira ta koma a dakin ta, ta sami guri ta zauna tana nazarin wa'annan kalaman da iya yen ta suka gaya ma ta.
Tsananin son da ta ke yiwa Mukhtar sai kara kallafuwa ya ke acikin zuciyar ta, tarasa yanda zata yi da rayuwar ta, tinanin Mukhtar ya riga ya mallake dikkan rayuwar ta, abin har ya kai Samira ba ta iya chin abinci, hawan jini ke neman hallaka ta, sanadiyyar yawan tinani ciwo ke ne man kada ita.
***   ***   ***
A sashen Mukhtar bayan wata daya (One Month) lafiya ya ke kara samuwa a gareshi, Mukhtar ya shiga tinanin masoyiyar sa Samira ce wacce ta fara fadowa a zuciyar sa, a cikin wannan tinanin ya ke sai yaji shigowar Dr. Umar domin duba lafiyar sa, “Assalamu  alaikum”, Dr. Umar ne ke sallama, Mukhtar ya amsa masa da cewa “Wa'alaikumussalam sannu da zuwa”, bayan gaisawar su na dan lokaci, Dr. Umar ya nemi Mukhtar da ya bashi labarin kansa da kuma   yanda aka yi wannan mummunan hatsari ya faru dashi, ba tare da wani bata lokaci ba, Mukhtar ya bashi labarin kansa da kuma yanda ayi hakan ya faru dashi, cikin nuna tausayi Dr. Umar ya ke cewa “Subhanallah Allah ya kara tausaya mana, kuma ya yi mana kariya, Mukhtar ya ce “ameen”. Dr. Umar ke cewa “duk da ya ke naso idan har aka sallameka inje dakai a gidana kaman koda mako uku ne, dai-dai ka kara samun lafiya”, Mukhtar ya amsa masa da cewa “ba da muwa ai duk wanda ya yi maka irin wannan taimakon ba kada tamkar sa, a duk fadin duniya dan haka ban da abin da zan saka maka dashi sai dai addu'a a gareka Allah ya kare ka ga duk kan makiya, ya kuma ya tausaya ma da aminci sa, ubangiji ya yi ma ka mafi kyakkyawan sakamako, ameen”. Dr. Umar ya kasa ya ce komai ya na rike da kafadar Mukhtar, Mukhtar kuma ya na gurfane ya rika kafar Dr. Umar. bayan fita Dr. Umar Mukhtar ya kasa ya kwanta, a tsaye ya ke kansa a sama ya na mai cewa “Ya Ubangiji na ina mai godiya a gareka da ka bani lafiya, ya Allah ka tausaya man ka aminta dani, ya mahaliccina kamaidani gida ina mai aminci, aminci a gareka madaukakin sarki, Mukhtar ya koma a kan gado ya kwanta. (Bayan wata biyu)
***   ***   ***
Fannin iyayen Mukhtar kuma sun zamu abin tausayi, Mukhtar ne kadai da agare su, ba suda wani da gaba daya sai Mukhtar. A dai-dai lokacin ne mahaifiyar Mukhtar Hajiya Karima ke a zaune a kan dogowar kujerar falon, tinanin ta ina ne zata ga dan ta Mukhtar, a zuciyarta ta ke cewa “lallai ni ban yi tsammani ce war Mukhtar ya mutu ba”, ta sake tana cewa “kuma   ya kan yu Mukhtar ya mutu, amma ni jikina sam bai bani da cewa Mukhtar ba ya a durun kasa ba”.
Lallai yau ne ya cika wata biyu bansa shi a idona ba, ta daga hannin ta a sama ta na kuka, ga abin da ta ke fada “Allah ka mayar man da dana a cikin koshin lafiya, Allah idan har Mukhtar ya mutu ya zan yi da rayuwa ta, Allah ka yi tausayi na ka mayar man da da na Mukhtar, dan darajar fiyayyen daraja shugaban halitta mafi ficin manzanni Muh'd (S.A.W), ta yi dai dai da shigowar mahaifin sa, Alhaji Kabir ya na mai cewa “Sallallahu alaihi wasallam” gaba dayan su suka shafa.
Alhaji Kabir ya zauna a kan kujerar da Hajiya Karima ta ke a zaune, ya dora hannin sa a kai ya rasa me keyi masa dadi a duniya, ga tambayar da matar tasa ta ke yi masa “Alhaji ko kaji labarin dannan” amsar sa, shine “wallahi ni banji komai ba dan haka ba wani abin da zamu yi sai addu'a. “To ai ina nan ina iya kacin nawa ko karin”, Hajiya Karima ce ta fadi hakan. Alhaji Kabir ya ce “To Allah yasa mu da ce” dukkan su suka ce ameen.
***   ***   ***
Da gari ya waye ranar ce ranar da za'a daura auren Samira da Alhaji Musa mutane sai taruwa suke, gaba daya kofar digan ya cika da ilahirin jama'a, manya manyan motoci ka, ke gani su ke ta (paking) a kofar gidan. a lokacin ne Samira ta yan ke shawarar zata gudu ta bar gidan yala'alla idan aka nemi amarya ba ta, kowa zai waste, kaga taron bazai yi tasiriba. duk da ya ke lokaci ya kure, tinanin ta ya zata fita ba tare da ansanda fitan nata ba, hakan mawuyacin abune domi ya wan mutanen da suka sauka a gidan ciki da waje.
***  ***  ***
Samira ta fito daga cikin dakin ta ta shigo a cikin babban falon gidan ta tarar da Mahaifiyar ta a zaune alokacin bata tare da kowa,Samira ta durkusa tana mai cewa “Umma kiji tausayina ki tausaya wa rayuwa ta, kada ku aurar dani ga Alhaji Musa kada ku hada ni da wanda bana so, Um… mari taji a bakin ta, “rabani da zancen banza, ga inda arziki ya ke inda za muci arziki muyi yanda muke so da arzki, kina neman mayar da mu baya, ki rikitar mana da lisafi, ai wannan maganar banza ki keyi, aure anriga an daura da gayau ke zamu matar Alhaji Musa, don haka ki tashi ki bani wuri, kina nema ki raina man da hankali, kimayar da mu dacchijan banza wa'anda ke sauya magana”. Samira ta shiga wani yanayi wanda ya ke da tsananin gaske, ta zamu abin tausayawa ga duk wanda ya ganta.
A lokacin ne ta ke kokarin tashi, amma ina ba dama nan ta ke ta yanki jiki ta fadi. Da ganin haka Hajiya Sakina ta yi matukar tsorata, ganin 'yar ta acikin wannan hali, nan da nan ta ratsa ihuu domin neman agaji, ita ba komai ta ke duba ba sai dai idan har Samira ta mutu yanzin shike nan wannan arzikin ya guje su, Hajiya Sakina ta kara ratsa ihuu!!! domin neman ceto.
A dai-dai lokacin ne Mahaifin Samira ya shigo a firgice gaba daya ya rude aguje da shigo warsa, ya ta rarda Samira a kwance, ya iso da sauri ya jijjiga ta, sam bai ji ta mutsa ba, Mal. Manir gaba daya ya rude yarasa yan da zaiyi, saboda tsananin rudewarsa ya katata sai a waje yana mai cewa “Samira ta mutu” muta ne, sai kururuwa ake domin aga meke faruwa, duk wanda ya shiga sai ya fito da sauri, lallai da yawan mutane hakan suke cewa, Amarya ta mutu ba zance daura aure.
Mal. Manir ya dawo gurin 'yarsa Samira idan kaganta tabbas ka ce da ita ta mutu domin ba alamar ko numfashi, kaji namiji da raki, faman kuka ya ke gaba daya matan da ke a cikin gidan kuwa ya ginda kuka, wannan auren bai yi ribaba.
Mahaifin Samira ya na son Samira fiye da yanda za ku zata, a zuciyar sa ya ke cewa, “idan har wannan guda gudar 'yar nan ta mutu sanadiyayyar wannan al'amari to yanzi ya zamuyi, lallai ni da nasan hakan zata faru da banbi zogar wannan matarba”, ya dan dubi Hajiya Sakina ya dan gyada kai ya ce “kamata mana muje da ita asibiti”, cikin tsananin rudewa Mal. Manir ya dauki 'yarsa domin zuwa asibiti,
***   ***   ***
An tafi da Samira zuwa asibitin, amma kash a dai-dai lokacin ne aka sallami Mukhtar, Mukhtar ya fito tare da Dr. Umar son shiga a mota mai kirar (end of disscotion 307), da shigar su direban ya ja motar, zance da ku har ya dungura motar sa zuwa fita, a wannan lokacin ne direban  ya dakko Samira ya kawo zuwa shiga, motocin na su kowacce sai da zoji 'yar uwarta, lallai wannan zan iya cewa da ku shine ban hannun makafi.
An shiga da Samira a cikin asibitin nan ta ke ma'aikatan asibitin suka dauki Samira a kan wani gadon marasa lafiya, an shiga da Samira a dakin kula da masara lafiya sai kuma a kayi dai-dai da dakin da Mukhtar ya kwanta ne cikin sa, da isuwar su, a dakin aka tsaiyar da iyayen ta awaje.
Cikin gaugawa aka fara binchike domin gano wane irin ciwo ne ke damu wanta har ya kai ta a hakan. Duk da ya ke numfashin nata sam bai dawo ba, binchiken Dr. ya nuna da cewa jinin ta ne ya hau, batare da bada lokaci ba likitan ya fito ya na mai duban Mahaifanta, kamun ya ce uffan cikin firgita Hajiya Sakina ta bude bakin ta da cewa “Dr. ta mutune?” Likitan ya ce “a'a tananan da ranta, amma har yanzinnan numfashin ta bai dawo ba”, Mal. Manir dai bai ce ko mai ba sai kallon likitan da kuma matar sa Hajiya Sakina da ya ke ta faman yi. Hajiya ta sake tambayar Likitan da cewa, “me ke damun ta ne?. Dr. ya ce Jinin ta ne ya hau, ya barsu a tsaye ya koma akan aikin sa, da shigar sa yaci gaba da aikin sa kamar yanda ya dace.
***   ***   ***
Mukhtar da Dr. Umar sun isa a gida, mai gadin gidan ne ke ko karin bode gate din gidan, bayan ya bode direban ya shiga da motar acikin gida ya yi parting, sauran ma'aikatan gidan kuma suka taso cikin gaugawa domin budewa Alhaji kofar motar bayan fito wansu Alhaji Umar ya rike kafadar Mukhtar dominsu shiga a cikin gida, babban falon gidan ne Dr. Umar ya shiga, da shigar suka sunyi sallama Assalamu alaikum, Amira ce ta karba Wa'alaikummussalam Abba “sannu da dawowa”, Dr. Umar ya amsa ma ta da cewa “Amira karatu ake tayi” Amira ta amsa tana mai cewa “eh! Jarabawa ne zamufara” alokacin ne ta hangu Mukhtar daga chan ta ke kura masa ido, Amira ta ga irin wanda take so.
Dr. Umar ya ke cewa Mukhtar “zauna mana, ai wannan gidan ku ne Mukhtar”, Mukhtar ya zauna, a lokacin ne Amira ta tashi dominta samu masu dan lemo. Fitar ta ke da wuya Hajiya Umaima ta sauko a sama ta na mai cewa “a'ah!!! maraba-maraba sannu ku da dawowa”, Alhaji Umar ya karba da cewa “uwar gida sarautar mata daga bacci ki ka ta shine? Hajiya Umaimat ta ce dashi “a'a na dan kwanta ne amma ba bacci naiba”.
Amira ta kawo masu laimo ta ajeye akan table da ke ajeye a tsakiyar kujeron ta kuma zuba a cikin cups irin na zamani, Dr. Umar ya dauki cup daya ya bawa Mukhtar, shi kuma dayan cup din ya dauka Mukhtar ya dan taba shan laimu sama-sama ya ajiye kofi. Wani kallo ne Amira ke masa wanda ke ratsa dukkan sassan jiki duk da ya ke tana nuns daru a wajen kallon da ta ke masa, batare da iyayen nata sun gane ba.
Amira yarin ya ce wacce Allah ya baiwa kyau idan kagan ta ka ce ba indiya ce, yarin ya ce wacce ta ke da matsakaicin tsawo, Amira yarin ya ce kamila maihakuri ga kuma sanin yakamata, yarin ya ce wacce ke da ilmin boko da kuma arbiyya, ba'anan kadai ta tsaya ba, Amira ta kasance mai yawan tausa yi a gurin wanda ya ke akasa gareta.
Amira 'ya ce wacce duk namijin da ya ganta sai ya muna kwadayin sa agare ta, 'ya ce wacce ta ke da kwar jinni a gurin Jama'a. Duk da ya ke Amira ba ita ka dai ta ke agurin iyayen ta ba, tana da 'yaya wanda yake karatun sa a Indian.
Amira tayi zaune idanuwan ta ba su dauke a fuskar Mukhtar ba, Amira ke cikin wannan yanayi tayi zorfi a tinani ta ya zata fito wa Mukhtar har ya san tana son sa. Mukhtar kuwa tin tini ya fahimci cewa Amira tana son sa, duk da ya ke Mukhtar ya yi alkawarin a kowane irin hali ya ke da kuma kowane irin yanayin rayuwa bazai manta da Samira ba hakan ya sa sam bai kula da itaba.
Mahaifiyar Amira Hajiya Umaima ke cewa “duk da ya ke na shirya maku wani shahararren (breek pass) wanda za ku ji dadin sa fiye da yanda za kuyi tsammani. Alhaji Umar ya ce “gaskiya” Hajiya Umaima ta ce “ku taso mana muje yana can na ajiye a dining table” Alhaji Umar ya dubi Mukhtar   ya ce “To tinda ta ce hakan tashi muje” Mukhtar ya dan yi murmushi ya tashi, gaba dayan su suka isa suka zauna a kujerin da ke gefe gefen dining table. Amira kuma ta dawo dai-dai kusa ga Mukhtar, badan komai ba sai dan ta dinga kallon kyakkyawar fuskar sa.
A dai-dai lokacinne suka fara cin abinci, Amira dai kallon Mukhtar ta ke yi domin ita ta kasa ta ci abincin, a zuciyar ta ta ke cewa, “Allah mai ikon sane ta kowace irin hanya, lallai Allah ya yi halittar sa ina ma ace zan zamu mata ga wanna bawanna ka! Tinanin Amira ya yi zirfi, har suka kamala cin abincin Amira bata ci ko cokali daya ba.
Duk da ya ke Hajiya Umaima ta fahimci amira, sanadiyyar irin kallon da ta ke yi wa Mukhtar.
Ganin hakan Hajiya Umaima ta shi tana mai cewa “Alhamdulillah Alhaji zan shiga a ciki”. Ganin Hajiya ta tashi Dr. Umar shima ya ce “ainima yanzin zan tashi” da wuce war Hajiya Umaima Mahaifiyar Amira Dr. Umar ya tashi amma sam shi baisan me ke faruwa ba.
Amira ke ganin Mahaifan nata gaba dayan sun fice da ga gurin, ganin hakan Amira ta kara kurawa Mukhtar ido feyi da yanda ta ke mishi a dazin, ganin hakan Mukhtar ya tashi izuwa babban falon gidan, da shigar sa ya kwanta akan doguwar kujerar falon.
Amira kuwa hakan ya bata mamaki matuka ta kasa da ta tashi a inda ta ke zaune, tarasa yanda zatayi har ya iya fahimtar fanufarta, azaune ta ke takasa da ta tashi jimkadan Amira ta tashi zuwa a dakinta domin tana sone ta dan kwanta kuta sami saukin wannan tinanin.
Kwanta wanta ke da wuya nan ta ke bacci ya shareta, jim kadan mafarki ya zo acikin bacci ta.   
***  ***  ***
Mukhtar ne ya tarar da Amira a zaune a gurin da ta ke zama domin hutawa, anan cikin lambun da ke arear gidan, lambun ya kunshi ababe masu bansha'awa za kaga plowers iri daban-daban.
        Amira ce a zaune kan kujerar dake gefen wani table wanda ya ke anan cikin lambun, a kan table din akwai wa'ansu kayan marmari iri daban-daban. Amira na dauke da madara tana sha, alokacin ne Mukhtar   ya zo dai-dai a inda ta ke ya gurfana ya na mai cewa “Amira kiyi tausayi na, Amira ki tallafi rayuwa na. Idan har baki tausaya man ba ya ki ke so ne na kasan ce? Amira sonki ne kadai a zuciya. Amira tsananin sonda zuciya ta ke miki ya sa na rasa duk kan jindadin rayuwa.
Amira idan har baki aminta da soyayya ta ba zan iya kasan cewa a cikin wani mummunan yanayi, ki tausaya man Amira, zuciya ta ka sance mai aminci”.
Mukhtar ya ka sance mai zubar da hawaye alokacin da ya ke ma ta wannan jawabi, Amira ta kalli fuskar Mukhtar, alokacin ne wani tausayi ya shige a zuciyar ta, nan ta ke hawaye suka dararu a idaniyar Amira, Amira ta ajiye madarar da ta ke sha, ta rika kafadar Mukhtar ta dakko wani kyalle a nan gefen ta, ta share masa hawayen da ke fitowa a idaniyar sa, tana mai cewa “Mukhtar kada ka damar da rayuwar ka, har a bada kaine wanda nasa a zuciya, banda wani wanda nake so kuma   nake kauna azuciya ta sai kai, tsananin sonda nake maka yasa na ka sance bana ganin ko wane da namiji sai kai.
Mukhtar idan har ban aminta da soyayyar ka ba to wazan aminta da shi? Mukhtar kai ka daine wanda zuciya ta bawa Aminci”.
Hakan sam bai sa Mukhtar ya daina fitowa da hawaye sa ba dan ganin Amira ta na fitar da hawaye a mafi kyawawan idaniya. Mukhtar   ya karbi kyallen da ta ke share masa fuskar sa ya na mai share hawayen da ke zubuwa a idaniyar Amira, ya rika kafadar Amira ya tada ita ya kuma kama hanyar zuwa a cikin gida.
A dai-dai lokacin da Amira ta tashi daga bacci a firgice tana mai daga hannayen ta a sama tana cewa “Ubangiji na ka taimake ni ka bani nasara ga duk kan ayukana ameen. Amira ta shafe hannayen ta a fuska.
***  ***  ***
A ban garen Samira kuma Samira farfado abisa tsawon lokacin da ta dauka batare da numfashi ba, a lokacin ne ta dan sami sauki har ta dan zauna akan gadon da ta ke a kwance. Samira tadan juya fuskar ta, zuwa yammacin gadon, juya wanta ke da wuya ta hangi wani (warch) wato agogon hannu wanda ya ke Mukhtar ke saye dashi, Samira ke tina lokacin da ta sanya masa wannan agogon hannu, ta yi shiru na dan lokaci ba wani ko dogon mutsi, jimkadan
Samira ke cewa “To meya kawo Mukhtar ta fadi wannan maganar a cikin jin tsoron fadan da ake Mukhtar ya mutu, zuciyar ta cewa “Bashakka Mukhtar ya mutu”, Samira ta shiga wani yanayi wanda ya ke abin tausaya wa, nan ta ke ta daga hannayen ta a sama tana mai cewa “Ya Ubangiji na ka tausaya mini ka cireni daga wannan kangin” ta sake da cewa cikin kaskantar da kai “Ya Ubangiji ka sanya mahaifana su ka sance masu duba na gaskiya, kada kudi ya rudar da su, ka bani nasara na kasance mata ga Mukhtar, Allah ni kai ne kadai wanda nake kai'wa kuka na, ya As-samad banda wanda zai iya biyan bukatuna, sai kai, banda karfi banda dabara, aga reka ne nake neman taimako na, aminci ya tabbata ga shugabam mu wanda ya fito manada gaskiya ya kuma kauwar mana da karya a tsakanin mu.
Duk kan godiya ta tabbata ga Allah subhanahu wata'ala don kai ne makagin halitta, Samira ta shafa hannayenta a fuskar ta, alokacin da ta kammala du'ain da ta ke.

***  ***  ***
Iyayen Samira ke zaune a cikin falo, Mal. Manir Mahaifin Samira ya dora hannayen sa ya dafe kansa yana mai cewa matar sa “Hajiya Sakina yanzi kina ganin wanna yarinyar idan har akayi wannan auren bazai zamu illa agare muba? Tambayar Mal. Manir izuwa ga Matar sa Hajiya Sakinat ke nan.
Hajiya Sakinat ta amsa masa da cewa “Malam kada ka damu da wannan ba wani illa da ke a kwai ga wannan al'amari” ta sake da cewa “To ai maganar aure akayi domin wanda ta ke so yazamu babu, dan haka bayanda zamuyi” “gawa kikaji cewa Mukhtar ya mutu? wannan jicejicen jama'ane kawai” Malam ya yi wannan zancen “Au ai abin da kaji mutane suna jicejice idan har akayibincike yakan yu gaskiya ne” Mal. Manir ke cewa ga wadan ne irin mutane kikaji wannan zance ba tare da ta bashi amsar sa ba Mal. Manir ya sake da cewa “ 'Ya dai ni ke da iko da ita kuma nike da ikon yi ma ta dukkan wani abin da naga ya dace, dan haka Wallahi ni na gaji da wannan zugar naki, aure kuma   za'a daura shine ga wanda ta ke so Bi'iznillah.
Mahaifiyar Samira ta ce “Malam wai kana sane da irin magan ganun da kake fada kuwa? Malam ke cewa “A'a bansan me nake fada ba, sai ki sanar dani”. “Idan har ka manta to ka tina da alkawarin daka dauka”. Malam ya ce “Wane Alkawari na dauka?” Ai alkawarin alkhairi ake cikawa ba alkawarin sharri ko zalinci ba.
“Eh naji ko ba wannan ba ka tina da irin alkharin da Alhaji Musa ya mana, kasan da cewa wannan gidan da muke a cikin sa shine ya saya mana, ka duba kaga irin wannan arzikin da muka yi sana diyar Alhaji Musa. Don haka wai kace zaka aurar da Samira ga wani wanda ba Alhaji Musa ba zancen banza ka ke”.
Mal. Manir ya yi sauri kamun ta dauko wani shafin yana mai cewa “ni kuma ina mai sanar dake cewa idan har wannan ne Wallahi daga yau gidan ya karbe abin sa, dama bai sameni acikin talauci ba, kwadayi ne kawai ya jaman wannan kuma ayanzinnan na gane gaskiya ina nan akan matsayina bazan chanja ba, dama hausawa kance KWADAYI MADUBIN WAHALA”. Ya sha wani dogon tsaki ya fita ya bar gidan.
“Ai Wallahi Maganar banza kake sai na gani ni dakai muga wanda zai sake.
***  ***  ***
A nasu bangaren kuma, Alhaji Musa ke zaune tare da yaron sa Gali, Alhaji ke tambayar Gali dacewa menene shawara game da wannan matsalar? kaga shawarar da ka bayar a baya ba ta yi umfani ba, dan haka ayanzin ka bada shawara wacce take da umfani. Gali ya yi shiru na dan lokacin, chan! ya ce “Alhaji gani na ke wannan ba wata matsala bane wacce zaka damar da rayuwar ka akan ta ba”. “Amma Gali akwai ka da maganar banza, a koda yaushe na nemeka shawara zaka ce kada dani ka damu wannan ba wani matsala ba ne, ai wannan rainin hankaline, idan har baka da abin da zaka ce ai sai ka gaya man bakada wata shawara, idan har wannan ba matsala bane me zai sa nane meka har nace meye shawarar ka”.
“Kai tashi ka bani wuri dan rainin hankali kawai”. Alhaji ya tashi a tsaye ya na ko karin kai ga yaron nasa Gali, da shauri Gali ya tashi ya fita don yasan a wannan lokacin komai zai fada Alhaji bazai saurare shi ba.
Alhaji Musa ya yi tsaye ya kasa ya zauna, kan sa a sama yana tafiya ya je gaba ya dawo baya, Alhaji Musa ya tsaya ya dora hannayen sa a kai can! Alhaji ke cewa “Wannan zance banza ne wani ya kunyatanirdani, ai wannan rainin hankali ne, bayan an yaudareni na kwashi kudi nayi umfani da su ta kowa ce irin hanya da hanyar kwarai da ta sharri don kawai na kai ga nasarar auren Samira”. ya cigaba da cewa “Iyayen Samira sun nuna aminci a gareni yanzin kuma naga su suke su nuna man rashin mutinci, wannan bazai yu ba nasan irin matakin da zan dauka akan su, zasu san da cewa lallai bahawshe ya yi gaskiya da ya ce KWADAYI MADUBIN WAHALA, dan haka muzuba ni da su”. Alhaji ya gyada kansa hadi da chiza hannu.
***  ***  ***
Alhaji Musa ya fito acikin falon sa ya zo dai dai inda ake parking motocin gidan, Alhaji ya bode mota da kan sa bai tsaya wani ya bode masa ba, ya ja motar acikin gaugawa maigadin gidan ya bode kofa da sauri, Alhaji ya fita da mota ba saukakawa. Maigadin ke tambayar kansa “lafiya Alhaji ke irin wannan gudun, amma abin da mamaki gaskiya, to Allah sauwaka mana”. Maigadin ya rufe gate yakoma wurin da ya ke a zaune ya zauna da mamakin wannan al'amarin.
Alhaji Musa ya nufi gidan su Samira da isa sa masu gadin gidan suka tasu cikin hanzari suka bude masa gate ya shiga da motar a can ciki sosai, ya fito acikin motar batare da wani tsaiko ba, Alhaji Musa ya buga kofar falon, ganin ya buga kar sau biyu baiji an amsa masa ba, ya bude kofar falon da kansa ya shiga. Hajiya Sakina ce a zaune ta dura hannaye akai tinanin ta taya zata samu ta ciyo kan mijin ta ya aminta da wannan auren. Duk da ya ke Hajiya Sakina sam bata ga shigowar Alhaji Musa ba. Alhaji Musa ya zauna a kujera da ga cikin kananin kujerin da ke falon, alokacin ne Hajiya Sakina ta ga Alhaji Musa zaune.
“Barka da zuwa yaushe aka zo?” “Alhaji Musa ya ce sam ba wannan ba ne ya kawo ni a gidan nan ba”. “Hajiay Sakina ta ce kamar ya ba wannan ya zo da kai gidan nan ba?”, ai wannan bai kai a hakkan ba”. “Saurara kiji, ina mai sheda miki da cewa niba mahaukaci ba ne, ina kyautata zatun ke fahimce ni? Wallahi wannan zance banza ne kuma bazai yu ba sam” Hajiya Sakina ke cewa “wallahi ni ban fahimci maganar ka ba”. Alhaji Musa ya ce “Eh! ia ba sai ke fahimci maganar ba domin maganar tawa ai maganar banza ce”. Ya sake da cewa “Sakina nazo ne domin shaida maku da cewa wallahi ina tausaya maku ne badan komai ba, sai don irin son da nake yiwa Samira, amma da ya ke naga bakwa ganin irin ragowar da nake mako lallai yau ne ranar karshe wacce ta ke… Alhaji Musa mikawa Hajiya notice karbi kiga naba ku nan da (3 hours) Awa uku, gaba daya ku tattara naku da na ku kubar man gida na ko koma agidan nan na ku wanda ku ka baro, domin wannan rainin hankali ne, kuma Wallahi za ku ga abin da ba zaku yi zato kokuma in ce tsammani ba.
Hajiya Sakina hankalinta ya tashi, ta mike a tsaye ta dawo a kusa da Alhaji tana cewa “Wallahi wannan yarinyar ce ta so ta ki ya mana amma Wallahi dole ne za muje a asibiti domin a sallamumana ita, kai wallahi ko da bata sami sauki ba za'a daura auren, ya yu bayan an daura duk lokacin da Allah ya bata sauki sai a kai ta a gidan na ka, kayi hakuri Alhaji”. 
“Hajiya Sakina wannan zance banza kike, don haka Wallahi bazan taba fasawa da abin da nayi niyar aika tawaba”. Alhaji Musa ya tashi ya barta tana faman kuka, bayan ya fita Hajiya Sakina ke cewa “yan zi shikenan wannan arzikin ya goje a garemu?” Tambayar kanta ta ke, ta ci gaba da kukan da ta ke.
***   ***   ***
Mukhtar ne akwance kan kujerar ababban falon gidan, sai tinanin Samira ya ke faman yi tin alokacin da ya fara samun sauki. Amira ce ta shigo a cikin falon, da shigowarta tatsaya ta kalli Mukhtar da kyau kallon da tayi masa taga lallai Mukhtar yana cikin wani yanayi na neman a tausaya mishi, kuma ganin kamar ko yaushe a hakan ta ke ganin shi, Amira ta rutsa tana mai cewa “Mukhtar lafiya naganka a hakan?”. “Lafiya kalau ne Amira me ki ka gani da ki ka tambiye ni?” tambayar da Mukhtar ya yi wa Amira ke nan. Amira ta ce “gani nayi a koda yaushe kamar baka da lafiya”. Mukhtar ke cewa “Amira ke san lamarin rayuwar duniya yanda ya ke, amma ni lafiya kalau na ke ba abin da ke bamu na”. Amira ta ce “amma gaskiya ni gani nake kamar akwai wani abinda yake damuwar ka baka so ne kawai ka sanar da ni”. “Ba haka bane Amira cewar Mukhtar”. Amira ta ce “To naji Allah taimake mu”. Mukhtar ya ce “ameen”, Amira ta juya dominta koma a dakin ta, tafiya ta ke tana waigo baya, ganin hakan yasa Mukhtar ya ce “ko da maganane”? Amira ta ce “a'a ba wani magana” Amira ta fita zowa nata dakin.
***   ***   ***
Mahaifin Samira ne acikin dakin asibitin domin sanar da Samira da cewa lallai shi ya aminta da za ta auri wanda ta ke so, ma'ana Mukhtar. Bayan mahaifin nata ya kammale sanar da ita wannan ne kamun ya fita, alokacin ne Alhaji Musa ya turu wadan su mutane su uku da su dakko masa Samira.
Mutanen nan acikin wata mota ce mai kirar (Judgment day) da shigar su a asibitin, adai-dai lokacin ne Mahaifin Samira ya fito daga dakin da Samira ta ke akwance. Mutanen nan kuma sun isu adai-dai da dakin mai no: 307 wanda ya ke shine dakin da samira ta ke acikin sa.

Kash mai karatu sai ka biyo ni a kashi na biyu domin sanin yanda wannan al'amarin zai kasance.
·       Shin zasu samu damar guduwa da Samira?
·       Ya iyayen Samira zasu kasance?
·       Mahaifiyar ta zata cimma biyan bukatun ta?
·       Tsakanin Samira da Amira wa Mukhtar zai aura?  
·       Ya Mukhtar zai tarar da gidan su?
Don haka, wannan tsaka mai wuya ku biyu ni a littafi na biyu domin sanin yanda zata warware, da kuma sanin mai nasara daga ciki. 

Taamat bihamdillah, Masoyin ku har kullum
Sharabhil Muhammad Sani (Sharhamak)
08103139272
E-mail:sharhamak@yahoo.com
sharha089@gmail.com
***   ***   ***
Godiya ta musamman ga Kamfanin Sane Tech Nig. Ents. (Sanetech publishers) wanda a yanzu ake kira da Signtech Digital Press Limited dake Birnin Kebbi Allah ya kara daukaka ku ya kuma haskaka lamurran ku, ameen.

Ina mai jinjina miki babbar 'Yaya Saratu M. Sani Allah ya kara daukakaki, ameen.

Godiya agareku Mahaifana Allah raya mu a tare da ku baki daya, ameen.

Jinjina a gareki Kaka ta Aishat Allah ka jikan mijin Alhaji Yaqub ya kuma sa aljanna ce makomar sa, ameen.

Jinjina ta a gareku Kanne na da abokai 'yan uwa da masoya na SRM bazam manta da ku ba har abada. Sharha Ms. Ke maku fatan Alkhairi Allah ya sadamu  a wani karon,  ameen.

LITTAFAI MASU FITOWA
Ku nemi littafin Farin masoyi,
Amini nane, Rudani, Sanadi, Bulaye dukkan wadannan littafan suna nan fitowa bada dadewaba. 
Sharhamak Hijri Dhq, 1431/27 Nov, 2010/4 week 44