KARSHEN ZANCE!!!
Ashe waiwaye adon tafiya ne
yau ga masoyiya yar mama
Sa’ida ce yar mama nake nunawa
Yaki yar fara agaidake yar manya
Sa’ida ce yar gidan Bala Gwandu karshen zance

Gaisuwa uwar tawaga sahiba ta ke zan yaba a yau yar girma
Na gaisheki sahiba takunki lafiya dai-dai-dai gaisuwa nake yi ta miki yar girma

Bisimilla sarki Allah wanda ya zamo gatana
Rabbana ka kara tsareni ya ubangiji sarki na
Zani na wurin Sa’ida gimbiyar yan mata, takon ki lafiya kin zam sarauniya yar girma

Ga salati gun manzon Allah don fa shi yazam gatana

Alihi, asahabatu na sanya kwarrike su bai koka ba
Tabi’ai waliya na sanya na rikesu ba sanya ba

Yanzu sharha zan dau hanya inje in iske giwar mata

Sha tankade da sabon kwarya!!!
Tasha ruwa da sabon muda..
Sa’ida ta zamo sai gada…
Maki gani ya runtse idanu na furta jinjina ga yar girma

Gimbiya Sa’ida, sannunki Sa’ida giwar mata
Ke alafiya kin tashi kwananki lafiya giwata
Sa’ida sannu hasken mata hasken ki ya wuce infurta
Gani naki Sa’ida tattaka a lafiya yar girma

Dukkaninku sai kunkai a kasa in kunga Sa’ida ta
Sa’ida yar gidan alfarma sannu sarauniyar mata
Akyau kin cire ta tutar nan ko wa biki sai yai rata
Gani sharha daga makera nazo wurin ki, kimin gata

Ke gadi girma kuma kin saba a gidanku ba karya ba
Ke gadi girma yar girma tun gidanku ba sanya ba
Maliya yau ta bamu ruwa tulu aja jiki can baya
In ana bayanin Sa’ida mata kuje kasa kuyi ban girma

Mata suka ce ga sako na jinjinar ban girma
Matan Kebbi sunke ga tasu jinjinar alfarma
Sakwkwato ma sunka ce in gaida sahiba yar girma
Yan yobe sun fada sun gaida yar gidan alfarma

Matan Abuja ma sunke sun gaida sarauniya yar girma
Matan adamawa suna kasa sunce a gaida ke maigirma
Matan Damaturu ma sunce ingaida yar gidan girma
Matan Sa’ida ma sunce sun gaida habibiyar alfarma

Sa'idatu jan karfe sararka anyi wasar banza
Kainuwa dashen Allah ne mai kinki yayi shirmen banza

Sannu sannu manyan haraka taka a lafiya yar girma
Yau muna yabon Sa’ida dole ne muzo muyu ban girma

Ke fa an shedeki kin kara daukaka yar girma
Tunda sharha ya shedeki kin dinga daukaka yar girma
Ruwanki sun cika kofi kingi a barsu bakin kofa
Ta sharha kin gawurta wa zayaja da ke yar girma

Zo ki bashi kyautar zuciya don shi muke jira yar gata
Ni dan Muhammadu na roka zo aminta yar alfarma

Mugaida Zainaba yaya ga Sa’ida yar girma
Ita sarauniya Sa’ida naso na ganki inyi bangirma
Mata ga sharha kece fa shimfidar yan mata
Duk wanda ya ce zaija dake nasheda ba zaisha ba

Ke Sa’ida na gaisheki tunda kin gaida gimbiyar yan mata
Ke Sa’ida ikon Allah wa zayaja dake cikin mata?
Ke wucesu sun lamunta sun jinjina ga reki a girma
Kai a karonga sai na leka inganki sahibar yan mata

A gaida Aisha yar Sokoto na so na gaidake kin hidima
Hajiya Aisha Kano na gaisheki jinjina nake kin sha fama
Amina Yola ke ce jagora dole a gaidake yar girma
Zainab Kaduna a gaisheki ke ma nayo jinjinar girma

Lubabatu Kano na gaisheki kema kinyi kokari yar girma
Ina kike Zainab dole naje kano ban girma
Ina Sa’idar Abuja kinsha fama
Har wayau ina gaisheki Safiya a Abuja kinsha girma

Hakama balki na gaisheki yau har Kaduna zan ban girma
Saratu ma na gaisheki don kinyi hiddima yar girma
Habiba ma na gaisheki don kinyi kokarin bangirma

Go slow a sako a huta na dinga jinjina yan mata
Na gaidake yar girma don na sanki ba sanin banza ba
Amira kin sha hidima dole in hada da sandar girma
Hindatu Turaki a gaisheki dole ingaida ke yar girma 
 
Gaisuwa uwar tawaga sahiba ta ke zan yaba a yau yar girma
Na gaisheki sahiba takunki lafiya dai-dai-dai gaisuwa nake yi ta miki yar girma
Rubutawa 
Dan Muhammad Birnin Kebbi