SiraÉ—in So
Da Lafazin Soyayyah 2
SHARAHBIL MUHAMMAD SANI
(Sharhamak)
Tel: 08103139272
Copyright © 2015-11-02 Sharahbil Muhammad Sani MaÆ™era
Hakkin Mallaka © 2015-11-02 Sharahbil Muhammad Sani
Maƙera
DOKA
An yarda ayi amfani da wannan littafi ko wani sashe
daga cikinsa amma tare da kafa hujja dashi, tako wace hanya.
PUBLISHED IN NIGERIA BY
SIGNTECH DIGITAL PRESS LIMITED
No: 66/67 Beside Nagari Science College
Birnin Kebbi,
Kebbi State, Nigeria
BOOK SETTING/COVER DESIGN BY
SHARAHBIL MUHAMMAD SANI MAKERA
Tel/WhatsApp: 08103139272
GODIYA
Dukkan yabo da godiya sun tabbatarma Allah Madaukaki,
mai kowa mai komai, wanda Ya sanya soyayya a tsakanin jinsi biyu na halittarSa.
Allah Ka yi dadin tsira ga Shugaban Halitta, Shugaban Annabawa da Manzanni,
Muhammad Dan Abdallah (S.A.W) tsira da aminci su kara tabbata a gareshi tare da
Iyalan gidansa da Sahabbansa da kuma masu bin tafarkinsa har izuwa ranar
karshe.
SADAUKARWA
Ga masoya na nakusa da na nesa. Ina rokon Allah da Ya
kareku daga sharrin makiya Ya kuma kara kulla soyayya tare da nasara mai
dorewa, amin.
JINJINA
Gare ku masoya na makaranta littafai na da fatar zaku
kasance a tare dani a koda yaushe.
Ina jinjina muku da irin kokarin da kuke da goyon
bayan da nake samu daga gareku ta hanyar kira da aiko sako na fatan alkhairi da
nake samu daga gareku, na gode. Na ku har kullum Sharahbil Muhammad Sani
Makera (Sharha Mak)
SiraÉ—in So
NA AMINTA DA SOYAYYA
Na aminta da soyayya
Kaunar ki ce nayo niyya
Ke ce wacce nasa zuciya ta
Kaunarki ta zamto sarkakkiya
Rayuwa ta sa tayo farfadiya
Na rasa inda ni zan tsaya da kaunar ta
Rayuwa tamkar darbejiya
Da daci take tafi madacciya
Ya ki zo kice dani kin aminta
Zo kar kice dani kin kiya
In kinyi haka zan sakaya
Hankali zai gushe kanki masoyiya ta
A kaunar ki ni nake yin zabarbiya
Sauri nake yi bani gajjiya
Saboda son gimbiyar mata
Na aminta da soyayya
Kaunarki ni yau nai niyya
Ya ki yan mata
Na shiga rauni da zuciya
Amma na kasa tirjiya
Kaunarki ce ta sa ni gajjiya zo kice kin
aminta
Sahiba ta zo ki bani soyayya
Aminiya ta kan ki bani alkunya
Sarauniya zo kice na aminta
SIRRIN ZUCIYA
Yau zan bayyana sirrin zuciya
Kaunarki ta sani hajijiya
Yaki kiban so kinjiya
Ke zaki barni na tsallake tsiradin
zuciya
Gani gaban ki ina juyayi
Kaunarki ta sa ni nake juyayi
Lallai yau zan bayyana sirrin nadai na boyoyi
yau gani na zo da sirrin zuciya
me sayasa a so na kasa yin tayi
kullum idan na ganki sai nai ta juyayi
kaunarki ta sa ni cikin juyayi
yaki amince da ni masoyiya
kullum idan na zo gidan ku sai na kasa
tayi
kallun idon ki dai nai tsayi
kyakkyawar fuskarki ta sa ni tsayi
ina son ki yan mata amince da soyayya
kullum idaniya ta ke suke gani
sun makanta a mata basu gani
nayi nisa a soyayarki kizo ki gani
amince da ni kar kice baki so na
masoyiya
kunnuwa na sun kurumta
basajin kira bale a furta
idanuwa ko sun azabata
da soyayyarki wata basu gani sai ke
aminiya
kauna na bani kizo ki karba
yafi a ce dake kizo sharba
soyayyarki ce tasa ni nai ta kirba
bani son ace dani zan rasaki a soyayya
sirrin zuciya a yau na shaida
a zuciya ta babu tsida
gun wasu matan tayi tsada
ke kadaice zaki taya aminiya
SIRADIN KAUNA
Siradin kaunarki zan tsallaka
Masoyiya ta zo ki taimaka
Ke kadai ce zan kusanta
Ina tunani a zuciya ta
Kaunarki lallai ta samu gata
Ke kadaice kauna na furta
Zo ki yarda dani aminiya
Kauna muyu da ke zo sarauniya
Tunani na bani da tamka ni na furta
Sanadin kaunarki na zama jarumi kauye da
birni
A sonki na yi suna duniya anka sanni
Na samu masoya masu fata da alkhairi ni
na furta
Amma gani yau siradin na kasa tsallakawa
Sai na fada don gazawa
Shin laifi na ne ko kuwa al’adar so tambaya
ta
Nayi bincike kanki kuma na gane
Cewa ke ce wacce ta dace kuma na gane
Koda najje nai magana iyaye miji sunka
mata
Nayi kuka idaniya sun gajarta
Zuciya ta sai faman bugawa kamar ta
busta
Na kasa hakuri amma can sai sunka furta
Sun bani kauwar ta don ita an rigani
Nace zanyi shawara zaku jini
Da naje gida na bacci yaki zowa gareni,
aminiya so zoki furta
Idan ka duba hannu na sunanta shine
Kullun itace abin tunawa, tunaninta
shine
Abinyi gareni don na yi nisa a so ne zo
na baki gata
Ina neman shawarar yan dandalina
Me zance gun mahaifanta don na nuna
Karfin soyayya ta gareta ko zasu gane
zan bata gata
Wannan shawara ce ni na nema naji ta
babba
Gunku masoya ni bani zamba
Ina sonta amma basu banba, aminiya zo na
baki zuciya ta
Siradin kaunarki zan tsallaka
Masoyiya ta zo ki taimaka
Ke kadai ce zan kusanta
Ina tunani a zuciya ta
Kaunarki lallai ta samu gata
Ke kadaice kauna na furta
…BURINA
Bani sake soyayya
Bani sakara lobayya
Yau na juya baya
Na rasa farin ciki na
Mai haskaka ruhina
Mai tausayi ga kalbi na
Na zasa mai so na
Mun dade da son juna
Gashi yau iyaye sun raba mu da juna
Ni fa kece burina
Ke naso ace zan nuna
Surruka ga ummana
Meyasa kuke jifa na
Kuka nake kan kauna
Na rasa zabin kalbina
Masoyayi kizo zo guna
Zo kice kina burina
Aure muyoshi da juna
Zan rike amanar kauna
Zan tsare hakken mai sona
Ke ce muradin raina
Kaunarki ce burina
Kaunarki ta ratsan raina
In babu ke an barna
Farin ciki babu araina
Ya ke abin alfahari na
Zo nan kizo muyi kauna
…MANUFATA
Sadiyya ke nake ta fata
Rayuwa ta duniya ke ce manuffata
Ina ta son su gane suna ta tsarguwa ta
Yaki zo mu zauna ki zam garkuwa gareni
Me yasa suka ce bazasu bani
Kudi, ilimi, nasaba duk suna gareni
Rikon da addini kuma dole gareni
Cikin masu hikkima dole ne a aganni
Na fahimta
Na aminta
Na karimta
Duniya ta sanni
Zainab ki ce ni
Zo muje ki bini
Muyi aure a birni
Na zo ki ganni
OYOYO MASOYIYA TA
Oyoyo masoyiya ta
Oyoyo zan baki gata
Oyoyo kaunar ki jata
Kaunar ki ta zama tsarin zuciya ta
Ke ce wacce na baiwa raggamata
Zo gani ki bani gata
Oyoyo sai na yaba ta
Kaunarki ce abin fadata
Sa’ida kin basu rata
Yau gani ina ta fata
Na so ace kudduri da fata
Sun cika yau na bata gata
Me yasa so yake da sata
Nan take zuciya ya sata
Yabi jini da jijiya ta
Gaki fara kuma kina da tsafta
Doguwa ce ga ido an bata
Tafiyar ta tafi ta, ai ta tsere mata
Ina sonki ya masoyiya ta
Kaunarki tana a zuciya ta
Zo gani ki bani gata
Sa’ida ce masoyiya ta
Kaunarki ina fadarta
A zuci kuma baki ya furta
Na aminta da son tauraruwa ta
Mai tsari irin na mata
Kizo gani ki bani gata
Soyayya!
Soyayyah! Soyayyah!
Har
yanzo ban dainaba
Kaunar
ki ban fasa ba
Ni
ke nasanya a rai duba
Ko
zaki ce kina so na
Eh!
Nayi tunani na duba
Kaunarki
ta samin haiba
Kwarjini
a cikin hubba
Har
wayau ni ban daina ba
Har
yanzo ban daina ba
Wayyo
raina kaunarki ban daina ba
Tunanin
ki shine abin yi duba
Hatsari
na shiga kan soyayyar yar baba
Zuciya
sai faman bugawa take zo duba
Na
rasa sukuni kan sonki akwana ban
runtsaba
Safiya
da rana duk daya ne guna basa gaba
Me
yasa suke tunanin da ba’a karba
Sirrin
Zuciya
Ke
na baiwa sirrin zuciya
Kaunarki
ta sani hajijiya
Tunaninki
abinyi aminiya
Zo
yaki yan mata zo Sa’ida
Kaunarki
nai fata muje saudiya
Aure
da ke nai fata masoyiya
Dare
da rana kece tunanin zuciya
Har
abada kece a zuciya
Idaniya
na kuka kan masoyiya
Rabuwa
ni da ke ban fata sarauniya
Ni
bani zaton wai zamu rabu da taurariya
Tunani
na ke nai duba a zuciya
Kina
da kyan siffa ko ba kwalliya
Gaki
fara, a sura sililiya
Iya
tafiya kuma waye ba indiya
Tattausan
lafazi
FIYA
– FIYA
Sako
daga Dan Kebbi
Agaida
fiya fiya ka gama arna - kurungus angama da arna
Wa ye taure ya
fada giwa - kurungus angama
da arna
Sun razana naga
basu ima - kurungus angama da arna
Kai har sun
hankura sunga basu suna kurungus
angama da arna
Watturo taure ya
fada giwa - kurungus angama da arna
Kanata hawa kana
da girma - kurungus angama da arna
Kai ka kara hawa
kana da girma - kurungus angama da arna
Sai dai gangara
gwani na - kurungus angama
da arna
Kai dai sai dai
gangara ubana - kurungus angama da arna
Gwarzo na Sa’ida
basu cimma - kurungus angama da arna
Sharha Muhammad a
gaida giwa - kurungus angama da arna
Dan bubawanga
bashi ima - kurungus
angama da arna
kurungus mungama
da arna - kurungus angama da arna
Sharha Muhammad
kana da girma - kurungus angama da arna
Kai ga dan kasuwa
tsayayye - kurungus angama da arna
Rana ta karo a
baiwa giwa - kurungus
angama da arna
Wa yaro ya farma
giwa - kurungus angama da arna
Yanzu karonga basu
ima - kurungus angama
da arna
Sharha Muhammad
Allah daukaka ka kurungus angama da
arna
Sai dai Sharha na Makera ka gama da arna kurungus angama da arna
Sannu fiya fiya ka
gama da arna
Gaba dai Sharha
Muhammad dan kasuwa ka darasu suna
Tafi dai tafi dai
giwa haryanzu da kai mukai gwani na
Sannu fiya fiya ka
gama da arna
Gaba dai Sharha
Muhammad dan kasuwa ka darasu suna
Gaba dai gaba dai giwa haryanzu da kai mukai gwani
na
Bisimilla gwani ahadun sarki na mai dare
da rana - Eh lallai
Shi yanda yaso yakai Allah na kar ka sani
kuna - Eh lallai
DK mai waka a jahar Kebbi zan buga tambari
na - Eh lallai
A wajen gwarzon
namiji Sharha Muhammad ubangidana
Sannu fiya fiya ka
gama da arna
Muje Sharha
Muhammad dan kasuwa ka darasu suna
Gaba dai gaba dai giwa haryanzu da kai mukai gwani
na
Salati dubu jimla zanyo gun annabi manzo
na - Eh lallai
Manzon Allah kunsan ya daukaka girma da
suna - Eh lallai
Alihi da sahabai munsa suma sun daukaka da
suna - Eh lallai
Ni dai manzon
Allah kai dai ka kwanta zuciya na
Sannu fiya fiya ka
gama da arna
Muje Sharha
Muhammad dan kasuwa ka darasu suna
Gaba dai gaba dai giwa haryanzu da kai mukai gwani
na
Muna maganar Sharha Muhammad munsan kana
da girma - Eh lallai
Kai ke bida maza Sharha Muh’d kanen Saratu
uwa ta girma - Eh lallai
Karya yaro yashsha ya dangana don yaga
bashi ima - Eh lallai
Dan kasuwa mai
kima ka zama fiya fiya na arna
Sannu fiya fiya ka
gama da arna
Muje Sharha Muhammad
dan kasuwa ka darasu suna
Gaba dai gaba dai giwa haryanzu da kai mukai gwani
na
Abin mamaki ga dan
taure na fada da kura - Eh lallai
Yaja damara ya
nade hannu ku kyale saura - Eh lallai
Kare a cikin jeji
ku kunsan bai fada da kura - Eh lallai
Ga Sharhabilu
Muhammadu ya kira su sauna
Sannu fiya fiya ka
gama da arna
Muje Sharha
Muhammad dan kasuwa ka darasu suna
Gaba dai gaba dai giwa haryanzu da kai mukai gwani
na
Gaba gwarzo mai Allah magauta ka sakasu
kuka gwani na - Eh lallai
To yaya zasuyi ne ka gagara ka hanasu suna
- Eh lallai
Jirgi uban tafiya gwarzo na Sa’ida bashi
sanya gwani na - Eh lallai
Sharha Muhammad ka
daukaka ba’aja da maigidana
Sannu fiya fiya ka
gama da arna
Muje Sharha
Muhammad dan kasuwa ka darasu suna
Gaba dai gaba dai giwa haryanzu da kai mukai gwani
na
Ango ga Sa’ida gwani giwa kake masu kalle
taru - Eh lallai
Gona mai taki can naffi zuwa na dinga lura
- Eh lallai
Ganda duk yayi noma fatan da yakai ga
kwara - Eh lallai
Har ya kai ga
girbi gonar wani bata gaba nai
Sannu fiya fiya ka
gama da arna
Muje Sharha
Muhammad dan kasuwa ka darasu suna
Gaba dai gaba dai giwa haryanzu da kai mukai gwani
na
Gaba dai sharha jan zaki ka hana suna - Eh lallai
Dotse mai nauyi kowaddauka shina da fama - Eh lallai
Ya maliya tayi ruwa kai kogi saika ja da
baya - Eh lallai
Na Sa’ida ruwan
malka kai muke so muke ta kauna
Sannu fiya fiya ka gama da arna
Muje Sharha
Muhammad dan kasuwa ka darasu suna
Gaba dai gaba dai giwa haryanzu da kai mukai gwani
na
Kwaro yaja baya ya
hangi fiya fiya makashi nai - Eh lallai
Shi ke karya maza
ciwon ciki ka gama da irna - Eh lallai
Masaki ke karya
kada kasu surazana ubana - Eh lallai
Kai nakawa waka
banwa wawan da baida suna
Mai ilimin boko ga
arbiya ina gwani na girma - Eh lallai
Ka fisu ado ka
girmama naga basu cimma - Eh lallai
Kafisu gida ka
girmama naga basu ima - Eh lallai
Dan kasuwa sharha
kai munkafi so kai muka kauna
KARSHEN ZANCE!!!
Ashe waiwaye adon tafiya ne
yau ga masoyiya yar mama
Sa’ida ce yar mama nake nunawa
Yaki yar fara agaidake yar manya
Sa’ida ce yar Muhammad Usmanu karshen
zance
Gaisuwa uwar tawaga sahiba ta ke zan yaba
a yau yar girma
Na gaisheki sahiba takunki lafiya
dai-dai-dai gaisuwa nake yi ta miki yar girma
Bisimilla sarki Allah wanda ya zamo gatana
Rabbana ka kara tsareni ya ubangiji sarki
na
Zani na wurin Sa’ida gimbiyar yan mata,
takon ki lafiya kin zam sarauniya yar girma
Ga salati gun manzon Allah don fa shi
yazam gatana
Alihi, asahabatu na sanya kwarrike su bai
koka ba
Tabi’ai waliya na sanya na rikesu ba sanya
ba
Yanzu sharha zan dau hanya inje in iske
giwar mata
Sha tankade da sabon kwarya!!!
Tasha ruwa da sabon muda..
Sa’ida ta zamo sai gada…
Maki gani ya runtse idanu na furta jinjina
ga yar girma
Gimbiya Sa’ida, sannunki Sa’ida giwar mata
Ke alafiya kin tashi kwananki lafiya
giwata
Sa’ida sannu hasken mata hasken ki ya wuce
infurta
Gani naki Sa’ida tattaka a lafiya yar
girma
Dukkaninku sai kunkai a kasa in kunga Sa’ida
ta
Sa’ida yar gidan alfarma sannu sarauniyar
mata
Akyau kin cire ta tutar nan ko wa biki sai
yai rata
Gani sharha daga makera nazo wurin ki,
kimin gata
Ke gadi girma kuma kin saba a gidanku ba
karya ba
Ke gadi girma yar girma tun gidanku ba
sanya ba
Maliya yau ta bamu ruwa tulu aja jiki can
baya
In ana bayanin Sa’ida mata kuje kasa kuyi
ban girma
Mata suka ce ga sako na jinjinar ban girma
Matan Kebbi sunke ga tasu jinjinar alfarma
Sakwkwato ma sunka ce in gaida sahiba yar
girma
Yan yobe sun fada sun gaida yar gidan
alfarma
Matan Abuja ma sunke sun gaida sarauniya
yar girma
Matan adamawa suna kasa sunce a gaida ke
maigirma
Matan Damaturu ma sunce ingaida yar gidan
girma
Matan Sa’ida ma sunce sun gaida habibiyar
alfarma
Sharahbilu jan karfe sararka anyi wasar
banza
Kainuwa dashen Allah ne mai kinsa yayi
shirmen banza
Sannu sannu manyan haraka taka a lafiya
dan girma
Yau muna yabon Sa’ida dole ne muzo muyu
ban girma
Ke fa sharha ya shedeki kin kara daukaka
yar girma
Tunda sharha ya shedeki kin dinga daukaka
yar girma
Ruwanki sun cika kofi kingi a barsu bakin
kofa
Ta sharha kin gawurta wa zayaja da ke yar
girma
Zo ki bashi kyautar zuciya don shi muke
jira yar gata
Ni dan Muhammadu na roka zo aminta yar
alfarma
Mugaida Zainaba yaya ga Sa’ida yar girma
Ita sarauniya Sa’ida naso na ganki inyi
bangirma
Mata ga sharha kece fa shimfidar yan mata
Duk wanda ya ce zaija dake nasheda ba
zaisha ba
Ke Sa’ida na gaisheki tunda kin gaida
gimbiyar yan mata
Ke Sa’ida ikon Allah wa zayaja dake cikin
mata?
Ke wucesu sun lamunta sun jinjina ga reki
a girma
Kai a karonga sai na leka inganki sahibar
yan mata
A gaida Aisha yar Sokoto na so na gaidake
kin hidima
Hajiya Aisha Kano na gaisheki jinjina nake
kin sha fama
Amina Yola ke ce jagora dole a gaidake yar
girma
Zainab Kaduna a gaisheki ke ma nayo jinjinar
girma
Lubabatu Kano na gaisheki kema kinyi
kokari yar girma
Ina kike Zainab dole naje kano ban girma
Ina Sa’idar Abuja kinsha fama
Har wayau ina gaisheki Safiya a Abuja
kinsha girma
Hakama balki na gaisheki yau har Kaduna
zan ban girma
Saratu ma na gaisheki don kinyi hiddima
yar girma
Habiba ma na gaisheki don kinyi kokarin
bangirma
Go slow a sako a huta na dinga jinjina yan
mata
Na gaidake yar girma don na sanki ba sanin
banza ba
Amira kin sha hidima dole in hada da
sandar girma
Hindatu Turaki a gaisheki dole ingaida ke
yar girma
Gaisuwa uwar tawaga sahiba ta ke zan yaba
a yau yar girma
Na gaisheki sahiba takunki lafiya
dai-dai-dai gaisuwa nake yi ta miki yar girma
Rubutawa Dan Muhammad
Birnin Kebbi
KO
KA/Ki NA JiNDADIN AYUKAN DA MUKE GUDANARWA?
Ga duk mai Sha’awar aiko da wani sako/abu da yake
bukatar a saka masa a wannan shafi a matsayin nashi gudunmawa kai tsayi sai ya
aiko mana sako ta wannan adireshin i-mel sharha089@gmail.com ko ya aiko sakonsa ta wannan lamba 08103139272, 0811377717.
0 Comments
Post a Comment