KASHEDIN KU
MASHAYA!!!
SHARAHBIL MUHAMMAD SANI MAƘERA
Tel:
08113777717
Hakim Mallaka © 2014 Sharahbil Muhammad Sani Maƙera
Copyright © 2014 Sharahbil Muhammad Sani Maƙera
ISBN
978 – 32004 – 9 – 6
Published in Nigeria
By
SIGNTECH
DIGITAL PRESS LIMITED
No: 66/67 Opposite Nagari Science
College, Birnin Kebbi, Kebbi State
Book
Setting/Cover Design
Sharahbil Muhammad Sani Maƙera
Tel: 08113777717
ABUBUWAN DA KE CIKI
Shafin Farko: - - - - - - - - 1
Hakkin Mallaka: - - - - - - - - 2
Abubuwan da ke
ciki: - - - - - - - 3
Godiya: - - - - - - - - - - 4
Ta’aliƙi: - - - - - - - - - - 7
Gabatarwa: - - - - - - - - - 9
Menene Shaye – Shaye?: - - - - - - 11
Kashe – Kashen Kayansa Maye: - - - - 11
Abubuwan da ake amfani da su a matsayin kayansa maye
da illolinsu: - - - - - - - - - 12
Illar shaye shaye ga matasa: - - - - - 17
Harkar shaye – shaye ga matasa: - - - - 19
Me ke jefa matasa cikin halin shaye – shaye?: - 22
Shaye – shaye babban laifi ne: - - - - - 25
Wake da laifi?: - - - - - - - - 25
Hanyoyin magance shaye – shaye ga matasa: - 29
Hotona masu ɗauke da saƙwanni: - - - - 35
Manazarta: - - - - - - - - - 39
Littaban Marubuci: - - - - - - - 40
GODIYA
Godiya ta tabbata
ga Allah maɗaukakin
Sarki kuma aminci ya tabbata a bisa zaɓaɓɓen jakada Shugaban Annabawa Muhammad ɗan
Abdullah wanda aka saukarma fiyayyen littafi (Al-ƙur’ani) domin ya zamo shiriya da kuma
waraka ga muminai.
Yarda da aminci su
ƙara tabbata a bisa
iyalan gidansa, da Sahabbansa, da kuma Muminai har ya zuwa ranar ƙarshe.
Bayan haka; lalle
Allah Mauɗaukaki
ya kimtsa mini kuma ya taimake ni akan na tarawa kaina da ƴan uwana wani abu
na daga faɗakarwa
kan matsalar da ta addabi al’ummar mu ta yau na shaye – shayen da matasa maza
da mata suka sami kansu a cikin sa.
Haƙiƙa na cirato wasu
bayanai daga waɗansu
ƙasidai da bayanai
da kuma faɗakarwa
daga wurare daban daban don ganin na ci nasarar tsara wannan littafi ta hanyar
fahimtar mutane daban daban, ina yiwa duk kan waɗan da nayi amfani da ƙasIdansu
da kuma faɗakarwar su godiya da kuma fatar Allah Ya biyasu, Ya amfanar da su da
ni da kuma al’umma daga wannan littafi, amin.
Bayan haka kuma nayi
ƙoƙarin inganta
littafin da kuma tace shi tare da shugabanni. Ina roƙon Allah Ya
taimake su Ya kuma ɗaukaka
darajojin su baki ɗaya,
Ya sanya albarka a cikin rayuwar su, amin.
Ina miƙa godiya ta ga
iyaye na waɗanda sune suka bani tarbiyya har zuwa ga wannan hali da na tsinci
kai na a cikin sa, ina roƙon Allah Ya raya mu tare da ku, ya kuma kyautata
rayuwar ku da mu, Ya yiwa rayuwar Albarka, amin.
Godiya ta bazata
ƙare ba har sai na miƙata ga shugabanni da mabiya ƙungiyar Staff School
Old Boy’s Association (Staff – SOBA) da irin ƙoƙari da jajircewa da suka
nunamin naganin ansamu nasara ga wannan tafiya ta alkhairi da cigaba, ina muku
fatan alkhairi, Allah Ya ƙara haɗa kanmu Ya amfanar da mu daga amfani mai yawa gareshi,
amin.
Ina miƙa godiya ta
ga duk wanda ya taimaka ta hanyar bada shawari ko ɗawainiya da hidindimu ko
kuma nuna farin ciki ga wannan aiki na cigaba, ina kuma miƙa godiya ga ƴan uwa
da abukan arziƙi masu fatan cigaba da ɗorewar nasara a dukkan al’amurran na,
Allah Ya taimakeku Ya amintar da ku daga tsoro, Ya kuma sanya alkhairi a cikin
rayuwar ku ta har abada, amin.
Daga ƙarshe kuma
ina roƙon Allah Ubanginmu Maigirma da Ya sanyawa littafin nan “KASHEDIN KU MASHAYA!!!” karɓuwa da
amfani da albarka ga wanda zai ƙarbe shi ya yi aiki da shi da kuma al’umma baki
ɗaya. Kuma ya sanya mu daga waɗanda Ya yarda da su a wajen faɗi da aiki, lalle Shi
ne managarcin Maijin ƙai.
Mai ƙaunar Rahamar UbangijinSa,
Mai yawan kyauta
Sharahbil Muhammad Sani Maƙera
TA’ALIƘI
Da
sunan Allah Mai Rahama da Jinƙai ya zuwa ga bayinSa. Ina mai godiya ga
Subhanahu Wata’ala (S.W.T) da Ya bani ikon ƙarfafawa marubucin wannan littafi
mai tarin amfani ga dukkan ɗan Adam.
Akwai
babi – babi dake lalata rayuwar ɗan Adam maza da mata da suka ƙunshi caca, sata
zina, da yake Malamai na kan Wa’azi ga al’umma akan illolin da kowannen su ke
jawowa a tarbiyyar ɗan Adam. Wannan littafi, ya baiwa nau’in Shaye – Shaye muhimmanci
don yafi zama ruwan dare game duniya har dai a ƙasashe masu tasowa kamar
Najeriya.
Marubucin
wannan littafe ya aurar da zamanin da aka fito ya zuwa wannan lokaci ta hanyoyi
daban – daban da zamunna ke haɗa ababen sa maye ga ɗan Adam da jinsi mai amfani
da jini kamar dabbobi da tsuntsaye. Ataƙaice, ya nuna mana abinda ilimin kimiya
ya kawo a wannan zamani na ingantawa ko lalata al’umma ta hanyar ƙwayoyi ko ruwan
da ke bugarwa watau su kawar da hankali.
“KASHEDIN KU MASHAYA!!!”
faɗakarwa ce ga uwaye da ƴaƴa maza da mata da yakamata ya zama abin karantawa
akowane lokaci.
Ina
mai ba hukumomi shawara da gabatar da wannan littafi a Makarantu da kuma kira
kan a sake tsarashi da ajami don yawaita amfaninsa ga al’umma. Na gode.
HON.
NURA USMAN
16/11/1434AH/11/09/2014CE
GABATARWA
Bashakka
al’amarin amfani da kaƴansa maye ya zama ruwan dare game duniya, domin babu
wata ƙasa ko Jiha da ba a shaye – shaye, sai dai a sami bambance – bambance
saboda yanayin wayewa ko tattalin arziki ko kuma ƙoƙarin shugabanni wajen daƙile
harkar ta shaye – shaye.
A
halin da muke a ciki mun samu kammu a cikin wani matsananciyar fitina ta shigar
Mata da Ƙananan Yara da kuma Matasa a harkar shaye – shaye.
Babushakka
wannan kan iya janyo fitintinu kamar haka:
vTaɓarɓarewar
tarbiyya da kulawar da iyaye mata suke bayarwa a matsayin gudummawa.
vSamuwar
rashe rashen lafiya da zai iya ɓullowa wanda bawanda ya san inda zai tsaya.
vTaɓarɓarewar
samun kwanciyar hankali da yawan fitintinu kamar su kisan kai, zinace – zinace,
sace – sace, da dai sauran aikin alfasha da munkari (abunƙi). Allah Ya mana
mafita Ya kuma taimake mu, Ya kuma yaye mana wannan fitinar data addabemu a
wannan ƙasar da duniya baki ɗaya.
Ganin
ire – iren waɗan nan matsalolin sai naga ya dace da na rubuta wannan littafi ta
hanyar samu bayanai wurare daban – daban da kuma bincike kan harkar mashaya,
ina fatar Allah Ya sa wannan littafi ya zama mai amfani ga duk wanda ya
karantashi ko ya duba wani sashe daga cikin sa.
SHARAHBIL MUHAMMAD SANI MAƘERA
08/12/1435AH/02/10/2014CE
Bismillahir
Rahmanir Rahim
Wasallallahu Ala Nabiy-al Karim
MENENE SHAYE – SHAYE?
S
|
haye
– Shaye, shi ne haɗiyar ko shan wasu ƙwayoyi masu sa maye ko ganyayyakin da shaƙarsu
ko cinsu kan fitar da ɗan Adam cikin hankalin sa, ko tunaninsa ya koma irin na
dabba
KASHE – KASHAN KAYANSA MAYE
Su
kayansa maye, sun kasu kashi daban – daban, gwargwadon yadda yanayin jama’a
yake da yanayin mazauni da ilimi da tarbiyya da yanayin tattalin arzikin yankin
yake. Amma masana wannan fannin sun raba kaƴansa maye zuwa rukuni – rukuni,
kuma daga cikinsu akwai masu sa maye kai tsaye, akwai waɗanda sai anyi amfani
da su fiye da kima, sannan zasu sa maye, akwai kuma waɗanda ɗaukar lokaci wajen
amfani da su ke sa su dinga sanya maye.
Haka
kuma akwai kayanmayen da ke iya dakatar da harkar jiki, akwai kuma masu tasiri
ga hankali da jiki kamar: -
Ø Sanya
buguwa
Ø Sanya
ruɗewa
Ø Shiga
halin matsanancin maye
Ø Sanya
matsanancin barci
Ø Da
kuma hana barci
ABUBUWAN DA AKE AMFANI DA SU A
MATSAYIN KAYANSA MAYE DA ILLOLINSU
1. Giya:
Shan giya na tasiri wajen gushewar hankali ɗan adam kuma idan hankali yagushe
komai ma za’a iya aikatawa, shan giya na kawo ciwon hanta, bugawar zuciya, ya na
kuma sanadiyyar cansa, shan giya na sa mashayinta lalacewa jiki ya samu nakasa,
da dai sauran illolin da giya take zama sanadiyya ga mashayinta, za’a kuma iya rasa
rayuwa kai tsaye.
2. Koken
(Hodar Iblis): Ya na da illoli sosai ga ɗan Adam, idan ɗan shaye shaye na
amfani da hodar iblis haƙiƙa zai iya samun kansa a cikin waɗan nan illolin kamar
su cansa, bugawar zuciya, raunin ƙashi da kuma saurin bugewa ma’ana saurin
tsufa, hodar iblis na tasiri a ƙwaƙwalwar ɗan Adam, yana kuma iya zama
sanadiyar rasa rayuwa.
3. Totolin,
Emzolin da Benelin: Shan waɗan nan magunguna batare da ka’ida ba yana da
illolin da yake haifarwa ɗan Adam ya na kuma tasiri wajen lalacewar siffar
jikin ɗan Adam, harma idan ka duba a dokokin amfani da shi a sashen illolinsa
zakaga an rubuta kada kayi tuƙi lokacin da kasha shi, domin yana sanya buguwa.
4. Taba
Wiwi: Tana ɗaya daga cikin mafi girman ababen da mashaya suke amfani da su
wajen shaye shaye alhali tana da illolin da take haifarwa kamar haka: Sanya
tabuwar hankali (hauka), Bugawar zuciya, Hawan jini da kuma samun haɗurra ya
yin tuƙin abin hawa, ƙarshema tana iya zama sanadiyyar rasa rai.
5. Taba
Sigari: Taba Sigari kusan ince shanta ya zamo ruwan dare, mafiyawan matasa da
magidanta suna amfani da ita, shan taba sigari yana haifar da illoli ga
garkuwar jikin ɗan Adam kamar haka: - lalacewar wasu sassa na jikin mutum,
Sanya ciwon nimoniya (Pneumonia) da kuma Bronchitis, Cancer, lalacewar zuciya
ta na kuma taɓa ƙwaƙwalwa da dai sauran miyagun curutan da take haifarwa (a ƙarshe
yana iya zama sanadiyar rasa rai) a taƙaice dai hukumar lafiya ta duniya ta
tilasta dukkan kanfanonin ta su tabbatar da sun rubuta ƙarara cewa “Taba
Sigari yana zama sanadiyar salwantar da rayuwa da wuri ga mai shanta”.
6. Turirin
Masai: Shaƙen Salanga wasu daga cikin ababen da matasa maza da mata ke amfani
da su wurin gusar da hankalin su, shaƙen warin yana tattare da illar da yake
haifarwa lafiyar ɗan Adam, ga kaɗan daga ciki: Ɗaukewar numfashi, ciwon hanta,
yawan curuta barkatai, yana kuma zamowa sanadiyar rasa rayuwa.
7.
Sholusho: Kan iya
sanadiyar waɗan nan matsalolin kamar haka: rukurkucewar jiki, ruɗewa, ciwon cancer,
zai iya sanadiyar samun matsalar huhu, taɓuwar hankali, da dai sauran illolin
da shaye shaye kan iya sanya mashayi aikatawa.
8.
Babba Juji: Tun
bamuje ko’ina ba kaji sunansa “Babba Juji”
shi Babba Juji yana sanadiyyar waɗan nan matsaloli kamar haka: Haukacewa kai
tsaye da kuma salwantar rayuwa, Allah ya mana kariya, amin.
Waɗan
nan su ne kaɗan daga cikin abubuwan da matasan mu suke amfani da su a matsayin
kayansa maye da marisa da kuma kaɗan daga cikin illolin da suke haifarwar wanda
ke mu’amalantar su.
Da
fari naso na lissafa kayan da kesa maye aƙalla guda ɗari da ƴan kai amma sai
nayi tunanin wasu basu sansu ba, kuma yin haka zai iya zama sanadiyyar wasu su
gwada su don basu taɓa jinsuba ko basu taɓa ganin anyi amfani dasuba, adalin
wannan na fasa aiwatar da hakan.
Ya
kamata matasa mu kula da lafiyar mu, mu guji abin da zai kawo mana illa ga
rayuwa, daga ƙarshema ya kan iya zama sanadiyyar mutuwa, kuma addini ma ya
haramta mana da cewa “Kada mu sanya hannayen mu a cikin hallaka”. Allah ya mana mafita, amin.
ILLAR SHAYE SHAYE GA MATASA
Hankali
babbar ni’ima ne, da wadata da kuma jari da ya kamata a kiyaye shi, a aiwatar
dashi, inda ya dace, shan kayan maye, da buguwa, wanda yake yaduwa tsakanin
matasa maza da mata, wanda hakan yake barazana ga taɓarɓarewar tarbiyya, da
rugujewar al’umma ta gari, abune na takaici da Allah wadai, a cikin shan kayan shaye
– shaye akwai matsaloli da suka shafi yawan rigima, tashin hankali, daru,
tarzoma, fitintinu, kashe – kashen rayuka, kuma akwai barazanar da kayan maye
suke yi ta ɓangarori kamar haka:
vAddini
ya haramta shaye – shaye haka kuma yaja kunne kansa
vHankali
kan gushe, sakamakon shan kayanmaye kuma Idanhakali ya gushe komaima mashayi
zai iya aikatawa.
vƳan
uwa da dangi da mashayi yake cutarwa shima wani nauyi ne babba da mai shaye –
shaye ya kamata ya lura da shi.
vFuskantar
matsalar tattalin arziki a wajen mai shaye – shaye sakamakon shan kayan maye.
vRashin
samun cikakkiyar lafiyar jiki da mashayi ya ke rasawa
vRashin
samun zaman lafiya da kwanciyar hankali da tsaro.
vRushewar
tarbiyya saboda suke ɗaukar ciki, shayarwa, reno da tarbiyya in suka zama ƴan
maye akwai matsala mai munin gaske.
vRashin
bin doka da aikata miyagun lafuka
vKawo
cikas ga ayyukan raya ƙasa da lalacewar nasaba, ta fuskar haihuwar ƴaƴa marasa
cikakkun iyaye.
vYara
daga primary, zuwa sakandare, Idansuna shaye shaye, da wuya suke iya dainawa,
ko da sun tafi jami’o’I, kuma su a ke sa ransu zama shugabanni nan gaba, ko
kuma su zama jami’an tsaro, idan ya zama tsaron lafiya da dukiyar masu hankali
ya koma hannun Yara ko Matasan da ke shaye – shaye, masu rushashshen hankali,
babushakka akwai tashin hankali, Allah ya kiyaye, amin.
HARKAR SHAYE – SHAYE GA MATASA
Matsalar
shaye – shayen miyagun ƙwayoyi yana ɗaya daga cikin matsalar da ta fitini
mutanen wannan zamani, kuma ta zama babban ƙalubalen da yake fuskantar
gwamnatoci a ƙasar nan. Haƙiƙa ɗabi’ar
shaye – shaye mummunar ɗabi’a ce musamman tsakanin matasa waɗan da ake ganin su
ne manyan gobe, matasan da idan lokaci yayi ko hali ya kama su ne zasu
jagoranci wannan ƙasa, wannan babbar matsalace da ta ke barazana ga zaman
lafiyar kowace irin al’umma, domin wajibin hukumomi ne tsarewa al’ummarsu
hankalinsu da lafiyarsu, musamman a cikin wannan rayuwar da muke cikin.
A
halin da muka sami kammu a yau, harkar shaye – shaye ta sauya ba kamar yadda
aka santa a shekarun baya ba. Yanzu kusan komai yana tafiya ne da zamani, da, a
yadda muka sani, daga mashaya taba sigari, sai masu zukar tabar wiwi waɗan da
sune muke kallo da cewa mutanen banza ne, mai shan shalisho kuwa dama wannan ƙazami
ne, ko su kansu wasu daga cikin ƴan shaye – shayen suna ƙyamar ɗan sholi, idan
har aka ce wane yana shan giya, shakka babu, lamari ya lalace, wannan mutumin
babu wanda zai kalleshi da kima ko daraja. Idan aka ce wane ɗan kwaya ne to
wata kila yana shan Ajigarau ne, ko wani magani da ake kira da suna buta ko
alabukum duk waɗan nan magungunan aji garau ne.
Amma
yanzu wannan batu bahaka yake ba, shaye – shaye ya ɗauki wani sabon salo ta
yadda bawai ga maza ya tsaya ba abin har da mata da ƙananan yara, ta yadda suke
shan ƙwayoyi masu yawa domin su bugu, akwai magungunan da aka sani na tari ko
mura sai mutum yayi ta a za su yana korawa da ruwa tun yana gane mutane har sai ya zo yana gani garaye garaye,
zaka yi mamaki idan kaji yadda matasa suke baiwa wannan mummunan aiki
muhimmanci, kuma wani ƙarin abin baƙin ciki da takaici har da manyan mutane da
kuma ɗimbin yara sababbin balaga a wannan mummunar rayuwa.
Magungunan
da ake amfani da su domin bugarwa sun haɗa da Benelin da Totalin da Emzolin da
Rocci da sauran dangogin maganin tarin mura, irin maganin da ake zubawa a cikin
ƴar ƙaramar kwalba idan za’a sha sai a sami ƙaramin cokali sai kaga yaro ko
yarinya sun shanye shi a lokaci ɗaya, wanda wannan ya wuce over dose sai dai a
kira shi da hauka, domin maganin da likita zai rubuta da za’a yi a kalla mako
biyu anasha, amma mutum ɗaya ya shanyeshi a lokaci guda, wannan hauka ne ko
hankali?, wannan yasaɓawa duk wani lafiyayyen hankali, galibima yanzu masu irin
wannan shan magani domin buguwa mata sukafi yawa, wasu sukance idan aka haɗa
shi da lemo yafi tafiya dai – dai; Allah ya kiyaye, amin.
ME KE JEFA MATASA CIKIN HALIN SHAYE –
SHAYE?
vBabban
dalili shine talauci da rashin tarbiyya tagari. Adalilin wannan bari mu ɗantsakalo
aibin talauci kamar yadda mukaji malamai nafaɗa cewa “Talauci fitina ce mai matukar
munin gaske har Annabi (S.A.W) da kansa ya na yawaita adu’ar neman kariya daga
talauci”. Wannan ya nuna tsananin muni da talauci ke tashi, domin mafi
yawan kaba’irorin na kafirci na fakewane a ƙarƙashin talauci. Allah Ya karemu
daga talauci, amin.
vRashin
tarbiyyar ƴaƴa sau dayawa yakan saka yaro a irin wannan halin shaye – shaye.
Sau dayawa iyaye da kan su suke jefa ƴaƴansu a irin wannan mummunan halin na
maye ta hanyar rashin kula da abonkan da ƴaƴansu suke hulɗa da su.
vMata
kan faɗa irin wannan halin sau da dama dalilin auren da ake yi musu na dule,
hakamma yakan jefa matasammu mata a irin wannan sha’ani na ƙwalewa.
vKwaikwayon
miyagun ɗabi’u ta hanyar kallon fina – finai ko tashoshin ƙetare ta hanyar
yanar gizo da sauran hanyoyin sadarwa. A halin da muke a ciki har finafinan mu
na cikin gida suna taimakawa matasa wayen gurɓacewar tarbiyya da kuma cusa musu
sha’awar irin wannan miyagun ɗabi’u.
vKarance – karancen mujallun batsa marassa amfani da kuma
watsi da tarbiyyar ƴaƴa.
vYawon almajiranci da tallace – tallace da aikatau na ƙananan
yara daga karkara zuwa birane, sau dayawa shi ne ummul haba’isin lalacewar
matasa da faɗawarsu a irin wannan matsala. Sau da dama wasu daga mata masu
talla sukan faɗa hatsarin karuwanci da kuma shaye – shaye, yawon almajiranci
kuma yakan haddasa matsalar faɗawa irin wannan matsala ta shaye – shaye da kuma
zamowa ɗanta’adda a cikin al’umma.
vNunawa
yaro gata don iyayensa nada wadata shima illace babba ga yaro kuma a mafi yawan
faruwar wannan al’amarin ƴaƴan da ake nunawa gata su sukafi lalacewa, matsalar
ba’a nan kaɗai ta tsaya ba, sai su zama sanadiyyar lalacewar waɗansu ƴaƴan.
Waɗannan
hanyoyi kowanne daga cikinsu na iya jefa yara a cikin mummunan ɗabi’ar da zata
iya gurbata tarbiyyar su.
SHAYE – SHAYE BABBAN LAIFI NE
Shaye
– shaye babban laifi ne da ya saɓawa kowane irin addini, haka kuma ya saɓawa
dokokin kowace irin ƙasa, ya saɓawa al’ada da tarbiyyarmu da zamantakewarmu,
lallai wannan babban laifi ne da ya shafi ɓangarori da dama, kama daga su kansu
masu shaye – shaye da iyaye da al’umma da kuma gwamnati.
WAKE DA LAIFI?
Iyaye
suna da laifi babba akan wannan batu, domin wasu da yawa suna sane da cewa ƴaƴansu
na shaye – shaye amma kuma basa ɗaukar wani mataki na magance hakan, misali,
zaka samu galibin yara sukan fara koyon shaye – shaye ne a lokacin bukubuwan
Sallah, inda zakaga ƙananan yara na koyar zuƙar taba sigari, wanda daga nan ake
cigaba zuwa busa tabar wiwi idankuma akayi rashin nasara abin ya ɗore sai kaji
yaro ya iya shan komai. Kaga wannan iyaye ne suka yi sakaci sosai akan ƴaƴansu,
domin zaka samu ba’a cika lura da zirga – zirgar yara ba a lokacin bukukuwan
sallah, kowane uba yabar ƴaƴansa su shana yadda suke so batare da damuwa da
al’amurransu ba ko bibiyar inda suke zuwa, da abinda suke yi ba.
Wannan dolen iyaye ne wajen samarwa
ƴaƴansu abukai nagari domin da yawan matasan da ke shaye shaye, su na faɗawa
tafarkin ne saboda dalilai daban daban. Waɗansu kan ɗauki ɗabi’ar a makaranta,
suna kwaikwaya ne a wurin abokan da su ke hulɗa da su. Don haka yazama wajibi
ga iyayen yara su dinga bibiyar ƴaƴansu a makarantu da kuma kula da kalar
abukan da suke mu’amalanta ko hulɗa dasu.
Lallai
wajibin iyayene su tashi tsaye haiƙan wajen ganin sun yaƙi wannan mugunyar ɗabi’ar
ta shaye – shaye. Dole iyaye da dattawa da masu unguwanni su tashi domin yaƙi
da wannan mugunyar ɗabi’ar, wani abin takaici shine wasu masu mulkin sukansu ƴan
ƙwaya ne.
Wajibin
hukumomi ne su tashi tsaye domin yaƙi da sha da fataucin waɗan nan miyagun ƙwayoyi,
ta hanyar yi hukunci mai tsanani ga duk wanda aka kama yana harkar safarar waɗan
nan miyagun ƙwayoyi da kuma masu sha, lallai dole gwamnati ta takawa ƴan siyasa
birki domin suna taka muhimmiyar rawa wajen jefa ƴan uwanmu matasa cikin wannan
mummunan yanayi, da yawansu su ne suke sayamusu waɗan nan kayan maye, da basu
makamai domin su faɗawa abokan hamayya.
Buɗe kemis birjik, ba tare da bin
ƙa’idoji ba shi ne ya fara kawo cikas ga kula da kiyaye harkar magunguna. Kamar
yadda mutum zai bushi iska ya bude shagon kayan ci da sha, ko kayan sayar da
bulawus da kayan kwalliya. Haka nan yanzu a ke busar iska a buɗe kemis. da ma
buɗe Kemis ɗin ne kawai, da sai ace da ɗan sauƙi, abun haushinma, wanda zai
kula da shagon sayar da kayan bulawus ko kayan kwalliya, shi ne zai kula da
Kemis za ka ga wani bai taba shiga makaranta ba, ballantana ya san wanne magani
ne ake sha idan ciwon kai ya addabi mutum.
Don haka, idan ma da gaske ne hukumomin
yaƙi da shaye shayen miyagun ƙwayoyi na aikinsu, na ganin an daƙile ko an kawo
cikas ga shan abubuwan da ke sa maye. To wajibi ne su fara da tsafta ce
kemis – kemis ɗin da a ka buɗe su ba tare da bin ƙa’ida ba. Duk da yake a ko
ina za’a iya samun mutanen kirki da kuma miyagu.
Sannan su kansu al’umma su sani waɗan nan matasa ƴan uwanmu
ne daga cikinmu suke, lallai ne ya zama wajibi a garemu wajen janyo su tare da
nuna musu muhimmanci rayuwa, da kuma illar wannan harka ta shaye – shaye, da
yawa wasu suna ɗaukar shawara, matsalar kwai itace wanɗa zai kirasu yayi musu
nasiha ne babu, kowa ya kame hannu tunda babu Ɗansa to ɗankowama ya mutu. Babu
shakka sai mun tsaya tsayin daka wajen ganin munbi hanyoyin da suka kamata
wajen ganin an shawo kan wannan matsala ta shaye shaye wadda barazanarta tana
da yawan gaske.
HANYOYIN MAGANCE SHAYE – SHAYE GA
MATASA
Babban
burin kowace ƙasa ko jiha shi ne, so take taga ƴan ƙasar ta ko jihar ta sun
zauna lafiya, tare da cikken hankali da bin doka, wannan shi zai sa a sami zaman
lafiya da ayyukan cigaba a kowace ƙasa ko jiha.
Haka
kuma matasa su ne ƙashin baƴancigaba idan har sun gyaru, ƙasa ta gyaru, idan kuma
suka lalace, sun zama haɗarin rayuwar kowace ƙasa, kuma babbar hanyar lalcewar
matasa ita ce shaye – shaye, idan har matasan gari suna shaye shaye to za a iya
samun kowanne irin nau’i na matsala a wannan garin, misali: -
vRashin
bin doka
vAikata
miyagun laifuka
vKawo
cikas ga ayukkan raya ƙasa
vRashin
tarbiyya
vLalacewar
nasaba, ta fuskar haihuwar ƴaƴa marasa cikakkun iyaye.
Ko
shakka babu ya zama wajibin kowace ƙasa ko jiha, ko gari, kauye ne ko birni, ya
tashi tsaye domin nemo hanyoyin magance matsalar shaye – shaye ko amfani da kayansa
maye, wannan ita ce maslaha da kuma zaman lafiya.
Hanyoyin
magance matsalar shaye – shaye ga matasa sun haɗa da: -
ü Wa’azi daga
Malamai: - Malamai wata babbar hanya ce da zasu taimaka wajen
magance matsalar shaye – shaye ta hanyar wa’azi da bayyana hukuncin kaƴansa
maye a musulunci.
ü Gudummawar Iyaye:
- Iyaye su kula da tarbiyyar ƴaƴansu tun daga neman Aure, da goyon ciki, da
reno, da lura da abokansu Idansun fara tasowa.
ü Gudummawar Ƙungiyoyinsa
kai:
- kowace ƙungiya ta fito da wata hikima ta hana shaye – shaye a gari.
ü Ilimin sanin
illolin kaƴansa maye ya ƙasance a cikin tsarin karatun Sakandare:
- Ya kamata ya zama cikin tsarin karatun sakandare, a sanya ilimin sanin
illolin kayansa maye a ciki, yin haka zai sa a shawo kan wannan matsala.
ü Samar da ayukkanyi
ga matasa: - akwai buƙatar gwamnati ta samar da ayyukanyi ga
matasa maza da mata, ta fuskar kafa masana’antu, masu kudi da ƙungiyoyi da
sauran ɓangarorin jama’a, su baiwa gwamnati goyon baya, ta wajen samar da aikin
yi ga matasa da koya musu sana’o’in hannu.
ü Kakkafa ƙananan
masanantu a birane da ƙauyuka: - wannan ma zai sa kowane
matashi ya sami abin yi domin ya zamu masa shamaki ga zaman banza balle har ya
fara tunanin aiwatar sana’ar yin shaye shaye.
ü Baiwa hukumar hana
sha da fataucin miyagun ƙwayoyi haɗin kai wajen gudanar da aikin ta: - sau
da dama idan hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi suka shiga unguwa ko
gari domin kama wani mai laifi sai kaga ƴan unguwa sukan taru su hana a tafi da
mai laifin ko su je suyi belinsa ko su hana hukunta shi ko kuma a ɓoye mai
laifi a ƙi nuna shi. Ya kamata a daina yin haka, domin abune mai illa sosai ga
al’umma.
ü Shirya tarukan
ƙarawa juna ilimi ga matasa: - a dinga shirya taron
ƙarawa juna sani, ga Limaman Juma’a da ƙungiyoyin ɗalibai, da kuma malamai masu
koyar da darasin addini a makarantu, da sauran muhimman mutane, su kuma su cigaba
da karantar da jama’arsu a koda yaushe domin wannan illace babba ga al’ummar
duniya baki ɗaya.
ü Hukunci mai
tsanani ga masu shan miyagun ƙwayoyi: - Idan muka duba ƙasar Saudi
Arabiya tana zartar da hukuncin kisa ga masu shigar musu da ƙwaya ko a jikin bizar
shiga ƙasarsu ana rubuta cewa duk wanda aka kama shi ya shiga da miyagun ƙwayoyi
hukuncin sa kisa ne, don haka a tsananta wajen hana shigowa da kayansa maye
daga waje sannan kuma daga ƙarshe dole ne a raba matasa da bangar siyasa.
Don
haka ina bawa matasa shawara muguji cutar da kanmu da kanmu, wannan shaye shaye
da muka saka kawunanmu a cikin sa ba al’adar mu bace, yahudawa ne suka ɓullo da
waɗan nan al’adun domin su shagaltar damu daga addininmu, su rabamu da
lafiyarmu, su kuma cimma nasara wajen ganin munci gaba da ci baya a ƙasarmu, wannan
al’amarin shaye shaye ya shafi roshewar ilimin al’umma da kuma roshewar ƙasa
baki ɗaya. Ina mana rokon Allah Ya taimake mu Ya bamu nasarar gane gaskiya da
kuma aiki da ita, Ya sanya nasara a cikin dukkan al’amarinmu, Ya kuma karemu
tare da ƙasarmu, Ya tsare mana rayukan u, Allah Ya sanya albarka a cikin
rayuwar mu, Ya amfanar da al’umma daga wannan littafi ya zama sanadiyyar
shiriya ga matasan mu, kuma ya zama sanadiyyar tsirar mu baki ɗaya. Allah Ya
amfanar da Jiha ta Kebbi, Ya tsare mana ita, Ya ɗaukaka Jihar Kebbi, da
al’ummar Jihar Kebbi da kuma matasan Jihar Kebbi da kewaye, Ya Allah Ka shiryar
damu bisa tafarki na gaskiya Kai ne ma’ishinmu, kuma gatanmu, Ka taimaki
musulunci da musulmi baki ɗaya. Ya Mai Gafarar zunubai Ka gafartawa matasanmu,
kuma Ka tilastasu gane illolin da ke cikin harkar shaye shayen da suke su
daina. Ina rokon Allah Ya ɗaukaka Arewa da kuma ƙasa ta Nigeria, amin.
Tsarki
ya tabbatar ma Allah ina kuma gode masa, Na sheda babu abin bautawa bisa can
canta sai Allah, Shi Kaɗai yake bashi da abokin tarayya, muna neman yafiyar Ka,
kuma Ka kauda kai daga laifuffukanmu, Kayi mana afuwa, amin.
Mai Kaunar Rahamar Allah
SHARAHBIL MUHAMMAD SANI MAƘERA
Tel:
08113777717
HOTUNA MASU ƊAUKE DA SAƘWANNI
MANAZARTA
(Dr) Yakubu
Maigida Kacako (2013) “Kayansa Maye na Gargajiya, da Ilolinsu”
DCG/OPS Hisbah Kano ya gabatar a Africa House a ranar 13th April,
2013.
I.S.B Daurawa (2014) “Illolin Shaye Shaye Ga Matasanmu” Submitted
by ISB Duarawa on Fri, 04/25/2014 - 08:54
Lubana Mukhtar
Umar (ND) “Shaye – Shaye Tsakanin Matasa Maza da Mata”
Malam Aminu
Ibrahim Daurawa, (ND) “Illar Kayan maye ga Matasa”
Yasir Ramaɗan Gwale
(ND) “Shaye
Shaye Tsakanin Matasa: Suwa ke da Laifi?”
Littafan Marubucin sun haɗa da:
ü …Mabuɗin
Wahala 1,2
ü Du’a
from the Qur’an & Sunnah
ü Du’a
for Studies & Exams!!!
ü Raudhatudh-Dhullab
Fi’ahadisis-Sayyidil Mursalin
ü Manufar
Rayuwa 1,2
ü Kashedin
Ku Mashaya!!!
Za’a
iya tuntuɓar Signtech Digital Press Limited da ke Opposite Nagari
Science College Birnin Kebbi, Kebbi State Layi na 7 Shago Mai Lamba 66/67.
Tel:
08054918787, 08032054591
0 Comments
Post a Comment