Lafazin Soyayyah











SHARAHBIL MUHAMMAD SANI
E-mail:sharhamak.info@gmail.com
Tel: 08113777717, 08103139272

Copyright © 2014 Sharahbil Muhammad Sani
Hakkin Mallakar © 2014 Sharahbil Muhammad Sani

Anfitar dashi a Wednesday, 24th Devember, 2014

PUBLISHED IN NIGERIA

By

Signtech Digital Press Limited

COVER DESIGN
Sharahbil Muh’d Sani
(Sharhamak)









GODIYA
Dukkan yabo da godiya sun tabbatarma Allah maɗaukakin Sarki, mai kowa mai komai, wanda Ya sanya soyayya a tsakanin kowane jinsi biyu na hallittarSa. Allah Ya da ɗa tsira ga shugaban halitta, shugaban manzanni, Muhammad Ɗan Abdullahi, tsira da aminci su kara tabbata agare shi, tare da Iyalan gidanSa da SahabbanSa, da kuma mabiya tafarkin sunnarSa har izuwa ranar sakamako.

***   ***   ***
SADAUKARWA
Ga masoya na nakusa da na nesa, ina roƙon Allah Ya kareku daga sharrin masu sharri Ya kuma ƙara ƙulla soyayya a tsakanin mu, amin.

***   ***   ***
DOKA
Ba’a yar da wani ko wata ya yi amfani da wannan littafi ko wani sashe daga cikin sa ba, ta ko wace hanya sai tare da izinin marubuci, Sharahbil Muhammad Sani (Sharhamak) a kiyaye.

***   ***   ***
JINJINA
Gare ku masoya na makaranta littafai na da fatar zaku kasance a tare da ni a koda yaushe.
Ina jinjina miki Yaya ta Sarat M. Sani, Allah ya ƙara miki bashira.
Jinjina ta gare ku abokai na a fannin karatu kamar su : Sa’eed Mas’ud, Mas’ud Ibrahim, Kabir A. S. Maga, Dr. Zee, Sanusi M. Kamba, Hindatu I. Turaki, Rufa’atu, Jamila da dai sauran waɗanda bansamu sanyawa ba, ina muku fatan alkhairi, Allah Ya sanya karatun namu ya zamo mai albarka Ya kuma karemu daga sharrin maƙiya da mahassada baki ɗaya.
Jinjinar bangirma ga ƴar kirki mai kyan hali, Aisha yar gidan mutunci, wacce tasan mutuncin jama’a idan kaga fushin ta to lallai da dalili, ina mai jinjina miki Aisha Bala Kwaifa da irin ƙoƙarinki da kulawa, Allah Ya taimakeki Ya kuma baki nasara a cikin al’amurran rayuwarki, Ya ƙara ɗaukaka darajar Aisha Ya kuma sanya albarka a cikin rayuwarta, amin.   

***   ***   ***



FAƊAKARWA
Ba’a yi wannan littafi don cimma wata biyan buƙata ba, an rubuta shi ne don sauƙaƙawa masoya domin kyautatawa ga masoyansu ta hanyar LAFAZIN SOYAYYA da kuma hakaito hankulansu. Sau da dama soyayya kan roshe dalilin rashin iya lafazi.

Haƙiƙa wannan littafin zai zama jagora wajen jawo hankulan masoya idan har anyi amfani da shi. 

Daga ƙarshe ina roƙon jama’a don Allah wanda ya san shiririta ce manufarsa kada ya yi amfani da littafi na. Allah Ya mana muwafaƙa, Ya kuma tsarkake niyyarmu, amin.
Daga mai ƙaunar ku Sharahbil Muhammad Sani (Sharhamak)


LAFAZIN Soyayya

***   ***   ***
…ZO MASOYIYA
Sa’ida zo masoyiya
Sa’ida ke zamu aminiya
Sa’ida kece sarauniya
In babu ke, babu lafiya

Sa’ida sonki ne a zuciya
Sa’ida ke nasa a zuciya
Ke shige a rai na masoyiya
Karki barni zo yaki gimbiya

Farinki ya zarce indiya
Tafiya waye baturiya
Fuskarki tafi ta balarabiya
Sa’ida ke sace zuciya

Takunki tamkar Sarauniya
Ke zarce mata na duniya
Sa’ida ke zaga jijiya
In babu ke, ban da lafiya
Ƙaunar ki ce yau a zuciya
Sonki shi ne ya zagaya
Jini na da hanta gaba ɗaya
Tunani na kece gaba ɗaya

Zan shiga ƙunci na rayuwa inji zuciya
In babu ke ya Sarauniya
Idaniya sai rubar ruwa rashin aminiya
Sa’ida karki barni kinjiya

Sahibar rayuwa da zuciya
Ƙaunar ki ce yau gaba ɗaya
Na rasa inda zani kewaya
Abinci na kasa haɗiya
Tausaya kice ni sarauniya








***   ***   ***
INA SON KI…

Ina sonki gimbiyar mata
Amince dani ya sahiba ta
Kiyar da dani ke ce jagoran zuciya ta
Ina sonki jarumar mata

Kaunar ki ce silar jaruntar zuciya ta
Kin ratsa zuciya jini da hanta
Ba zani barki ba sarauniyar mata
Ki na raina kinji ƴan mata

Zanyi kuka idan na rasa ƴar gata
Zuciya ta yi ƙunci ina ta fata
Kasan cewa da ke matsayin miji da mata
Kasance da ni kiyarda da ni kinji autar mata

Tunani na kizamu uwa mai bajinta
Ki kasance dani zaman da babu ƙeta
Zama na har abada suruka ga umma ta
Kasance dani zo kiyar da dani ƴan mata


***   ***   ***
SO SIDANARI…

Sinadarin so, soyayya sinadari mata
Zo Sa’ida soyayya ta shige a zuciya ta

Yaki gimbiya tauraruwa a zuciya ta
Mai haskaka rai na har da zuciya ta

Farko da sunan Allah zani fara
Wanda ya yi dare shi ya yi mira

Duk kanin tunani na dake zani fara
Zan tsinci soyayya ki sam ba dabara

Kalma ta soyayya ya masoyiya ta
Ta ratsa raina har da zuciya ta

Ke zama jagora ta zuciya ta
Ya ki zo muyo soyayya na baki gata

Aminci na baki yar gida na gata
Yaki zo ki zo karki barni na aminta


Ƙaunar ki ta shige zuciya da fata
Ta ratsa jijiya, jini da hanta

***   ***   ***
SILAR SO …
Silar so ƙaurna
A so ke na nuna
Ƙauna ki ce raina
Ambatonki shi ne lazumina
Rayuwa tana ta ƙuna

In babu ke mai so na
Silar son ki ne ke a raina
Ƙauna ki ce zani nuna
Amince dani mai sona
Ki yarda dani muyi ƙauna

Ya sahiba zo muyi ƙauna
Soyayya ce ta sani sauna
Cikin duhun dare ke zani nuna
Idanu na a kallonki basa sauna
Ina sonki mai sona

Na shiga tarko na ƙauna
Ki taimaka ki ceci raina
Da kalaman nan naki ƙauna
Zuciya ta ke ta ƙuna
Rashin ganin ki farin cikina

***   ***   ***
ZUCIYAR SO DA…

Zuciya ta so da ƙauna ta faɗa tarko ba fitowa
Ta faɗa son ki harda ƙuna taimakonki baya gushwa

Tallafin ki na ke buƙata harda ni kai tunawa
Zuciyar ki na riƙe zo kama ni zan fitowa

A cikin barci ko a farke ko yaushe ke nake tunawa
Ko yaushe muradi nake ki karɓi son da babu rowa

Kar ki barni ya ki guna ƙaunarki ce yau tasani kuwa
Sonki bazan bari ba don ki sani zuci kan fashewa

Yayyafi na so da ƙauna ya yi zubar ruwa a kaina
Zuciya ta tana ta ƙuna in ta rasa wanda zai yi sona

Alfarma shi nake ta nema gunka kazamu mijina
Bani son inga damuwarka don ka zarce dukka masu sona

Idan har ranka ya ɓaci sai naji suka har cikin jikina
Babu abin da zai rabamu ka zamu jarumi a guna

Natsuwar ka da hankalin ka shi ke tada tsiga ta jikina
Harda jiki zanzari yake yi don yaji muryarka sahibi na

Ni ka ɗai ma batu nake yi idan na tuna ka saboda ƙauna
Ya ka masoyi kar ka barni inka barni zan rasa raina

Ga zantuka cike da kamala babu diyar da ta kai ki tsabta
Ko a gari dake a ke kwatance don kin zarcewa mata

Har dangi suna tayani murna nayi dacen sarauniya ta mata
Farin wata mai dusashe harken taurari kece na fahimta

Nai jinjina gareka sadauki kaja gaban manya da ƙanana
Cikin maza ka zamu musu zaki gani gaban ka dole in tsugunna

Tashi ki ganni masoyiya mai sanyaya idona
Murmushi in kiyo gareni sai naji sanyi har cikin jinina
***   ***   ***
DUNIYAR SO…
Ranar mutuwa ce da ke sanya masoya hawaye
Tunani nake yi inbabu ke cikin duniyar so ya zani ƙare

Tunani nake yi mutuwa kaɗai kan rabamu in babu kai cikin duniyar so ya zani ƙare

Yanda ni dai na ke ji  a raina kamar bazaki dawo ba
Duk ilahirin jiki na babu ƙarfi can cikin rai azaba
Ji nake kamar bazan rayuwa ba
Idan baki luraba
Muntadda mararraba
Abin da nake fargaba ƙauna ta ƙare

Bazani ƙika ba komai zafi da ƙuna
In kaga bamu tare sai dai in babu raina
Saboda kai ne dukan jinin jikina
Abin da ke a raina zuciya ta ta nuna
Bawanda zan gani har ya bani so da ƙauna
A rayuwa har ya samu wai ƙarbuwa bani son ka da damuwa daure ka jure

Yazama dole,
Ko kin kulle
Sai na ɓalle
Bazan ƙyale
Soyayyarki ba,

Kishirruwa
Ya zanyi da rayuwa
Son kin a dada ruruwa
Ta dalilin shaƙuwa
In kin tafi zan shiga damuwa
Bani son wani ya yi karo da son ki Allah ya kare

Bani son zubar hawayen ka
Ni ma duba cikin idanuna
Kwantar da hankalinka
Ba abin da zai kawar da gani na
Kai kake bani haske duk inda na tsinci rayuwa na
Jigo na rayuwa na, mai kare lafiya ta, walla ka share


Haka yake in anyi sabo
Wata rana sai ai rabo
In da rai a she da rabo
Allah sa haka bamu rabo
Tunda munce tunanin mu ɗaya
Haka ne kuma zuciyar mu ɗaya
Ruhinmu ɗaya
Fuskukin mu ɗaya

Wajen zaman mu ɗaya
Anan cikin duniya
Har ma a can muna tare






 

  





MAKAUNIYA

Allah gwani kai ne ka ƙagi samaniya,
Kai yo maza mata cikin su halitta.

Ka ce mu so Manzo Rasulu abin biya,
Ɗa gun Aminatu Sidi ya cancanta.

Na san akwai so gaskiya ne ƴan uwa,
Domin ko Rabbi ya sa shi nan ga halitta.

Me sa mutum ya zamo kamar wani jarumi,
Me ji kamar zai doke dukka halitta.

Da can ina zargi a kan mai so ku ji,
Na mai da shi wawa cikinsu halitta.

Yau ga shi na faɗa a tarko har wuya,
Bege a kan wata ƴa cikinsu halitta.

Kullum na zo barci in ta tararradi,
Domin tunanina yana a gare ta.

In don mafarki na yi sau zambar dubu,
Domin yawan shauƙin in sami ganinta.

A cikin mafarki mun haɗe mun daddale,
Amma a fili babu wanda ya furta.

Kwayar idonta kawai tana rikitar da ni,
Balle ta yo farfar da na dube ta.

In tai fishi sannan take dada kyan gani,
Balle harara ta fi kyau a wurin ta.

Tsari da suffa ba batunsu a nan wurin,
Ta zarce duk wani kyau da za a musalta.

Haƙuri damo ya sallama mata kun jiya,
A cikinsu mata ban ga wadda ta kai ta.

Ni na zamo sarki a harkar so ku san,
Amma a yau na zam mariri gun ta.

Ya zan yi ne na zamo gwani a wajen ta ni?
Har ma ta san ni ta san ina ƙaunarta.

Ni ba ni so na faɗa da baki ta san ina,
Mutukar masifar so yana a gare ta.

Babbar buƙatata a ce ta san da ni,
Ta gane lallai ni ina begenta.

Ko da ko ba ta so gare ni ku tabbata,
Na cim ma burina a kan ƙaunarta.

Ya ƴan uwa ku taho da tanyon agaji,
Ko na ji sauƙi kan batun matsayinta.

Ya zan yi ne in warke ciwon nan kuwa,
In sami yarjewa cikin
ƙalbinta.

Ciwo kaɗan da kaɗan yake daɗa ƙaruwa,
Wata ran a wayi gari ya kai ka ka kwanta.

Ni shawara na bida gare ku makaranta,
In bayyana ne ko ko kadda na furta.

Ƴan Dandali ku fito da amsar tambaya,
Ku malamai ne kan sa so ku fahimta.

In kun gaza kun ba mu kunya bai ɗaya,
Sai dai na ce kaico a harkar son ta










Wasiƙun SOYAYYA (6)

INA TUNANIN BAKI FAHIMCI INDA NA DOSA BA (1)
Aminci a gareki,

Ummul-Khair! Kamar yanda na sanar da ke, ina tunanin baki fahimci inda na dosa ba, don haka sai na sake shawara da cewa abu mafi sauƙi shi ne in rubuta miki wannan takardar kamar yanda zai biyo baya.

Haƙiƙanin gaskiya yau ne ranar da zan bayyana miki da abin da yake a cikin zuciya ta, banyi zato ko tsammani ba zaki iya gujewa gareni, ko ki kyamace ni, sanin kowane Ummul-Khair yarinya ce kyakkyawa, wacce Allah ya baiwa farin jini, ga kuma kyan fuska, gashi har gadon baya, a duk lokacin da Ummul-Khair ta ke tafiya, ni kan ƙure mata kallu, Ummul-Khair kin zarce duk kanin ƴan mata, dayawan mata su ke fata ace sun taka sawun ki, amma ina ba dama.
Kyan ki waye ba’indiya, jiki mai kyau kuma inaga balarabiya, tsayinki kuma dai dai kin tsayo matukar tsayowa, Allah Ya miki kyan da bazan iya misaltawa ba.
Ummul-Khair idaniya sun hango farin cikinsu, sun hangu sanyi su, ranar da na aika miki saƙo na farko, tunani na ya yi rauni saboda tsoro da fargaba sai naga ba mafita idan har ba na fito fili na sanar da ke sirrin zuciya ba.

Tsananin sonki ya tsanan ta a cikin zuciya ta, har ma ya keta ƙirjina ya fito fili, duk wanda ya ganni yasan ina cikin wani hali na daban kuma abin tausayawa, halayena da tunani na duk sun canja saboda ke.

Ummul-Khair ki amince da ni domin inyi alfahari da ke a wata rana da zamu tare a matsayin ma’aurata.

Ina Sonki Ummul-Khair
MUHAMMAD ISHAQ





NA SHIGA TSAKA MAI WUYA (2)
Salam, barka da wara haka ina fatan aminin zuciya a mafi ribatuwar rayuwa, bayan haka: Ya kai sanyi idanu, nasami kai na a mafi munin safiya, yau ne ranar da bazan taɓa mantawa da ita ba, kuma yau na ɗauki biro na rubuta a kundin tarihin rayuwa ta.

Aminin zuciya ina baka haƙuri dangane da abin da ya faru, nasan nayi kuskure, kuma abin da nayi ban kyautaba, haƙiƙa sheɗan ne sanadiyar afkuwar wannan al’amari.

Masoyina! Idan har baka haƙura ba, shinwa zan nemi afuwa gunsa? Kada ka manta kai kaɗai ne farin cikin rayuwa ta, kuma kai ne wanda nake fata ya zame man sanyi idanu mai ɗorewa. Ina sahibin zuciya? Ahmad ina sanar da kai cewa na ɗauki alƙawari ba wani abin da zai sa ni in daina ƙaunar ka, Ƙaunar ka ce kaɗai a zuciya ta, kuma kai ne Insha Allahu wanda zan zamo mata a gareshi.

Ina Son ka Ahmad
Daga Sahibar ka
SA’IDA ISMA’ILA
AMINCE DANI YA KE SILAR JIN
DAƊI NA (3)

Aminci a gareki,
Ya ke sanyin idaniya

Bayan gaisuwa irin ta masoya, tare da fatar rayuwa mai inganci, ina miki fatan ka sancewa da lafiya mai ɗorewa.

Sararin zuciya ta, abar ƙauna, hasken zuciya haƙiƙa kece zuciya take ta bege, kece wacce zuciya ta ke tsantsar ƙauna. Na rubuto miki wannan saƙo ne badon komai ba sai don na sanar da ke gaskiyar al’amarin abin da ke cikin zuciya ta. Na kamu da ƙaunar ki. Son ki ya gama zagaye ko ina a sassan jikina, bani da wani abu da zan iya aiwatarwa face tunanin ki. Amince da ni, ya  ke silar jin daɗi na.

Ya ke mai haskaka zuciya ta, haƙiƙa a sonki na yi matuƙar ɗimauta, ki aminci da ni ya ke sanyin idaniya.

Masoyin ki
SADIQ MUSA
SO TASKAR ZUCIYA (4)
Salam,
Ki karanta wannan saƙo a cikin farin ciki da nishadi ya ke masoyiya, haƙiƙa so ya canja tunani na, Sa’ida ki kula dani, ki man lamuni da ƙaunar ki, ki amince dani, ke ce ki ka zamu muradin zuciya. Soyayyar ki ce ta zamo abu mafi raɗaɗi da azabtarwar zuciya, na rasa yanda zan yi na samu sauƙi a ciwon da zuciya ta kamu da shina ƙaunar ki, ina sonki Sa’ida, ki yo tallafi a soyayya ta kada ki gujeni, muradi na shine ki kasance a matsayin sanyin idanuna na har abada.

Kasance dani kuma kiyar da dani ya ke haske mai haskaka zuciya ta.

Masoyin ki har kullum
KABIR IBRAHIM



FARIN CIKIN ZUCIYA TA (5)

Assalamu Alaikum,
Ya ke farin cikin zuciya, kuma sanyi idaniya, haƙiƙa ke ce mace ta farko wacce na yi gamu da ita akan so, bantaɓa zato ko tsammani ba za’a yi wata ƴa mace wacce zata sace min duk kanin ruhi a mafi ƙanƙanin lokaci ba, amma sai gashi ba tsammani nayi kicibis da kyakkyawar muskar da na kasa ɗaukewa kallo.

Haƙiƙa tun lokacin da idaniya ta kalle ki zuciya ta kamu da ciwon sonki, na aiko miki wannan sako ne ba don komai ba sai don na rasa irin hanyar da ya dace na bi domin sanar da ke, kwana da kwanaki ina tunani da irin hanyar da zan bi ta sanar da ke wannan cutar da Allah ya yi min jarabawa da ita, amma ina, na kasa. Na yi tunanin samun ki a makaranta domin na sanar da ke irin ƙaunar ki da ke ƙunshe a cikin zuciya, sai naga ba mafi sauƙi irin rubutu miki wannan wasiƙar.

Ka da na cikaki da surutu ya ke hasken zuciya ta, kin riga kin zamo ginshiƙin rayuwata, ina sonki, ina kuma ƙaunarki, a kullun ke ce abin tunane na, zan rasa duk kanin farin ciki idan har ban samu amincewar ki ba, haƙiƙa zuciya zata ɗan dani wata irin azaba idan kika ce bakya tare da ni.

Daga ƙarshe ina miki fatan alkhairi, ina kuma sauraru daga gareki, nagode.  

Masoyin ki na har abada
AHMAD MUHAMMAD KABIR




DARE DA RANA KAI NE ABIN
TUNANI NA (6)
Aminci ya tabbata ga farin cikin zuciya

Bayan gaisuwa da fatan alkhairi ina gabatar maka da wannan saƙo ba don komai ba sai don tunatarwa a gareka da irin soyayar mu.  

Masoyi na, kada ka manta, dare da rana kai ne abin tunani na, a duk lokacin da na kwanta idan har ba muryar ka na jiba to faufau ni da bacci munyi ban kwana, yau kimanin shekara biyu da ƴan kwanaki kenan da na kamu da sonka amma na kasa na sanar da kai nayi ƙoƙarin nuna alamu amma sai nake ganin kamar baka san inda na dosa ba. Ibrahim ka sani cewa bazan iya rayuwa ba tare da kai ba, kai ne kaɗai zaka iya zamuwa gata a wuri na.

shin me yasa zuciya bata jin rarrashi ne?, ni da kai na na sani Ibrahim ya san irin zafi da ƙuncin da mai so kan shiga idan har bai samu gata a inda yake nuna soyayyar sa ba. Ibrahim me yasa idan ina nuna maka ƙauna da tausayi da kuma kulawa lokacin kake ƙauracewa a gareni? Ka da ka manta shi so hallittace kuma jarabawace baka sanin lokacin da yake riskuwar ka kamar yanda baka sanin kiskuwar mutuwar ka.

Tunani na ya yanke basira ta ta dallashe, shawarwari na sun ƙare, ɓoyon da na ke yi ya kai ƙarshe yau ne ranar da ta zamo ranar tarihi a wurina.

Ina sonka, ina kaunar ka Ibrahim, bazan taɓa mantawa da kaiba, ka amince da ni.

Kaunar ka nake dare da rana
HINDATU ISMA’IL

Alhamdullillah
1.    Soyayya
2.    Oyoyo Masoyiya ta
3.    Na aminta da ke
4.    Kin kasance farin ciki
5.    Ina kike mai So na
***  ***  ***



***  ***  ***
SANARWA! SANARWA!! SANARWA!!!
Yana da Muhimmanci ka karanta wannan Sanarwa

KU NEMI LITTAFIN
…Mabuɗin Wahala na Sharahbil Muhammad Sani yana nan a kasuwa, kada ku bari a baku labari wannan littafi an yi shi ne don ku, don kuma a nishadan da ka ku, da ingantacciyar soyayyar asali, soyayyar da aka gida ta don ɗorewa ta har abada. Amma kash! Sai tayi rashin sa’ar iyayen da duniya ce manufar su.
…Mabudin Wahala ya nan a kasuwannen ku na Kano, Sokoto, Birnin Kebbi da kuma Zamfara.
Zaku iya kiran daya daga wadannan lambubin domin samun Sharahbil Muh’d Sani Makera (Sharhamak) ta kai tsaye ku kira 08103139272, 08113777717

Website: www.craspost.xyz
Littafai Maso fitowa a ɓangaren saƙwanni
·       100 Love SMS
·       Over 100 Language all around the world to said I love you
Littafai Maso fitowa a ɓangaren Nishadan tarwa
Wadannan littafain zasu biyo baya Insha Allah kuma na rubuta sune don in nishadan tar da makaranta Littafaina 
·       Dariyar – Darara
·       Sharhamak don Nishadi
Littafain Maso fitowa a ɓangaren Hausa Novel
·       …Mabuɗin Wahala 2
·       Farin Masoyi
·       Amini nane
·       Ƙudurina…
·       Tsautsayi
Da sannu zaku sami waɗan nan littafai a kasuwan nen ku da ke garin Sokoto da Birnin Kebbi da kuma sauran kasuwanni da suke kusa da ku.
(Sharhamak Insha Allah)
…With God Everything is Possible