RAHOTO.
22/3/2019
Jumu'a

Daga fadar Mai Martaba Sarkin Gwandu, Alh Muhammad Iliyasu Bashar (Shugaban Majalisar Sarakunan Jahar Kebbi)


A yau ne shuwagabannin wannan kungiya mai albarka, kamar yanda sunka saba a ko wa ne mako ranar jumu'a suna dauko rahoto daga fadar masarautar Gwandu.
Maimartaba Sarkin Gwandu *** Shugaban NTA Birnin Kebbi

Kamar yanda aka saba a ko wa ne mako mai martaba sarkin Gwandu yana zama da 'yan malisarsa domin sauraren koke-koke ko korafe-korafe acikin al'umar kasar Gwandu.



Bisa zamanda ya gudana  a wannan fada mai albarka,an tattauna muhimman ababe wadanda suka shafi magance matsalar shaye-shaye atsakanin al'ummar musulmi da ke cikin kasar Gwandu,da magance matsalar wata dabi'ar caca da ke cima mutan birnin kebbi tuwo a kwarya.
Haka zalika masarautar Gwandu zata jawo hankalin Gwamnatin jaha don kara inganta wutar lantarki ga sauran yankunan kasar Gwandu suma su sami isasshiya wutar lantarki.


Duk acikin zaman malisa ne da yagudana a yau ne mai martaba sarkinkin Gwandu yakarbi vakuncin  sabon manajan NTA. Manajan ya jinjinama wannan masarauta bisa ga yanda ta ke basu goyon baya ga ayukkansu tun kamin yasamu wannan matsayi na manaja.Daga karshe dai mai martaba yayi mishi babbar kyauta tareda bashi shawara yaji tsoron Allah aduk inda yasami kanshi,manajan yaji dadi matuka har ya nemi albarma awurin mai martaba da yabasu dama suturo wani yarika zuwa yana daukar rahoto kuma masarauta tabasu mutum daya wanda zai dinga kaimusu rahoton wannan masarauta,mai martaba dai ya aminta da wannan alfarma.

Gwandu Emirate Social Media Team

Daga karshe mai martaba yakara jawo hankalin iyayen yara da su sa idanu ga al'amurransu da huldarsu da wasu miyagun muta ne da ba'a sani ba,yayi kuma adu'a akan Allah ya zaunarda kasarmu lafiya inda za'ayi zabe gobe Allah yasa ayi lafiya akare lafiya.Yana kuma yima kowa barka da jumu'a Allah ya amshi ibadarmu amin.


Karshen rahoton kenan.




Abubakar Aliyu Gwandu.
(Justice Gwandu)
Sakataren watsa labarai na masarautar Gwandu.