SHAKAR WARIN TUSA YANA KARIYA DAGA KAMUWA DA CUTUTTUKA - Dakta Mark Wu



Jaridar Dimokuradiya: A sakamakon binciken da wasu masana da suka gabatar a Jami’ar Delta Zeta dake kasar Britaniya, sakamakon nasu ya bayyana cewa shakar warin tusa na da matukar amfani a jikin dan Adam.

A cewar su "shakar warin tusa na kare dan Adam da kamuwa daga cututtuka kamar su Sanyin Kashi, Ciwon Daji (Cancer) ko kuma Sankara da wasu cututtukan daban.

Jagoran binciken Dakta Mark Wu ya bayyana  cewa warin tusa na dauke da Sinadarin (AP30) wanda ke kare bil Adama daga kamuwa da cututtuka daban daban.

DAGA CIKIN AMFANIN TUSA DA SUKA BAYYANA AKWAI:

1. Kariyar dan Adam daga kamiwa daga Cututtuka dake kama zuciya. 


2. Yana kariyar mutum daga kamuwa daga cutar shanyewar bangaren jiki.

3. Warin tusa na kariya daga kamuwa daga yawan Mantuwa.

4. Yana kuma kariya daga kamuwa da cutar Dajin dake kama Dubura.

5. Warin tusa na kariyar Bil adama daga kamuwa daga cutar Sanyin kashi.


Mark Wu ya kuma ce, bankawa juna musamman Ma’aurata kuma tusar a hanci ba abu ne da za a rika jin kunya a kai ba, domin ya na da wani sinadarin da ke kara dankon soyayya a tsakanin su.

A dalilin haka Dakta Mark yake kara yin kira ga masoya da Ma’aurata da su rika yi wa junansu tusa mai doyin gaske saboda sabonta soyayya a tsakanin su, sannan kuma da samun lafiya mai nagarta.