AKWAI WANI KUSKURE DA MUKE YI A SALLAH, TO DUK WANDA YAKE YI BASHI DA SALLAH. 
(Sai mukaranta domin mu gyara). Wato 'yan uwana akwai wani kuskure da muke yawan aiwatarwa yayin ganawa da Ubangijinmu shi ne kamar haka:
Zaku ga mutum idan anyi ruku'u saboda yana gaggawar samun wannan raka'ar, ba ya tsayawa yayi kabbarar harama, sai kawai ya zarce shi ma da ruku'un. Mun manta da cewa duk wanda ya manta bai yi kabbarar harama ba bashi da Sallah.
Ka fara yin kabbarar harama tukunna sai kayi kabbarar wannan ruku'u da kazo ka tarar. Kuma nasha ganin manya da yara suna yin wannan dabi'a, don haka Manzo (S.A.W) ya umarce mu da cewa kada mu yi gudu ko gaggawa a yayin da aka tayar da Sallah, mu tafi a cikin nutsuwa muje mu sallaci raka'ar da muka samu, mu kawo wadanda suka wuce mu.
Domin koda zaman tahiyar karshe ka samu to kana da ladan jam'i amma katashika kawo raka'o'in da suka wuceka.
Dan Allah 'yan uwa duk wanda yaga wannan sako ya aikawa yan uwa Musulmi ta hanyar share da Comment don mu samu ladan tunatarwa baki daya. Allah ya kara fahimtar damu addininsa.
Ameenn