Sanin kowa ne kungiyar Sahihiyar Rayuwa kungiya ce mai zaman kanta da take kokari wajen ganin cewa an samu nagartattun matasa a wannan kasa ta Nigeria.
Kungiyar Sahihiyar Rayuwa Youth Community Development Association wacce shugabanta kuma wanda ya kafa ta Sharahbil Muhammad Sani Makera ya tabbatar mana da cewa sun tallafawa sama da matasa 4000 a cikin shekara uku (3) Ya kuma tabbatar mana da cewa matasan da suka taimakawa sun taimaka musu ne da Sana'o'in Hannu iri daban daban da suka hada da:
1. Aikin Walda da kere-kere: Inda aka samu wasu matasa da suka kware sosai har suka kera injimin Bugun shinkafa, alkama, gero, dawa, masara, wake da injimin dashen shinkafa kai ba a nan kadai suka tsaya ba sun kera injimin tace kullu wanda mata suke amfani dashi wajen jin girki ko kunu.
2. Cosmetics da Catering: An samu kaso mai tsoka na mata da suka koyi wannan sana'a wanda daga cikin matasan da suka koyi sanar da Cosmetics da Catering da yawa daga cikinsu sun yi nasarar zama kwararru a cikin sana'arsu har sun samu dogaro gakai a dalilin sana'ar. Sun dauki sana'ar yin mayukan shafawa, turare, sabulu, omo, man wankin kai, wasu kuma sun dauki sana'ar yin Cakes, Donut da sauran girke girke, inda a makon da ya gabata ma tashar DW Radio suka tattauna da wasu daga cikin dalibai da suka yi nasara a cikinsu.
3. Barbing/Saloon: Da dama daga cikin matasa maza da mata sun dauki sana'ar babin mata kuma sun koyi sana'ar saloon irin nasu da kitso da sauransu inda yanzu haka akwai da dama da suka yi nasarar bude wurarensu.
4. Computer/Engineering: Kaso mai yawa na daga cikin matasan da suka koyi sana'ar hannu daga kungiyar sun koyi computer da kuma koyon gyaranta, a yanzu haka an samu da yawa daga cikinsu suna amfani da wannan dama don cin abinci.
5. Driving: Sana'ar tuki sana'a ce da ke da matukar amfani ga rayuwar matasa, hakan yasa sahihiya ta tabbatar cewa ta samar da sana'ar a cikin jerin sana'o'in da take koyarwa, matasa masu yawa sun koyi sana'ar tuki kuma mun tabbatar sun bi hanyar da ya dace ana kuma samar musu takardar sheda da hukumar kiyaye hadurra ta kasa ta yarda da ita.
6. Dinkin Tela, Takalma, Jakunkuna, Zannuwan Gado, Kayan Yara da sauransu: anan ma kungiyar ta yi bajinta wajen ganin cewa ta samar da kwararrun masara wadannan ilmomin don amfanar al'umma.
Akwai sana'a sama da 25 da kungiyar ke koyar da matasa don magance matsalar zaman banza.
Yanzu haka dai kungiyar ta shirya tsaf don ganin cewa ta fito da wasu sababbin hanyoyin kawar da zaman banza a cikin al'umma.
Mun samu wasu bayanai daga Sakataren kungiyar inda muka tambiyeshi cewa ko akwai masu tallafawa kungiyar. Amsar da ya bamu ita ce "ba za a ce ba a samu ba"
Mun tambiye shi ko wane irin kalu bale ne kuke fuskanta
Ya ce
Kalu balen mu bai wuce rashin samun dama ba gada wajen gwamnatin Jihar Kebbi duk da cewar sun sammu sun kuma san irin aikin da muke iyawa, idan ban mantasa aikin da akayi KARDA na gyaran injinan bugun shinkafa da aka yi ta wahala ba a samu wadanga zasu iya gyaransu ba, a cikin kankanin lokaci yaranmu suka yi aikin kuma cikin nasara.
Ya kuma tabbatar mana da cewa a shirye suke da su kawo cigaba mai amfani a tafiyar wannan gwamnati idan sun samu damar hakan.
Babu shakka da zamu samu ire iren wadannan kungiyoyin da kasar mu ta samu cigakken cigaba mai amfani.
Kofar kungiyar a bude take ga duk mai bukatar tallafawa don ganin cewa an samu cigaba mai amfani a rayuwar al'ummar mu da kasa baki daya.
0 Comments
Post a Comment