Wannan
bayani ne daga Fahimtar Ka'idojin Kimiyya da Nassoshin al’qur’ani Maigirma
Abin
da muka sani ne wanda duk aka tambaya “daga ina ruwa ke samuwa?”, amsar shit a farko
da zarar ya bude bakinsa it ace: "DAGA SAMA NE." ba a yi
musun hakan ba, duk da cewa haka amsar take, amma ba iyakacinta ba kenan. Kai
ba ma wannan ba, abin da mai karatu zai yi mamakin ji shi ne, ruwan sama wata
hanya ce ko wani tsari ne na maimaituwar samuwan ruwa a wannan duniya. Abin
da zai tabbatar mana da wannan bayani shi ne, idan muka yi nazarin ayoyin alqur'ani
da kyau, za mu ga cewa idan ana maganar asali ne, to ma iya cewa asalin farko
na ruwa shi ne tekuna, da koguna da muke da su a duniya. Bayan Allah ya
tsage wannan duniya a halittar farko aka samu sama da kasa, daga baya sai Allah
Ya kimtsa wannan kasa tamu zuwa yanayin da zai dace da zamantakewar mu.Wannan
kimtsawar kuwa ya samu ta hanyar baje kasar, da sanya ta ta zama mai laushi,
mai saukin mu'amala, da kuma samar mana da tekuna, da koguna, da rafuka, sannan
kuma aka kintsa sama – ta hanyar samar da giragizai da iska – don tabbatar da
tsarin samar da ruwa ko maimaituwarsa a duniya. Wadannan bayanai, idan mai
karatu zai natsu ko ya tambaya, za a samo masa su a cikin Suratun Naazi'aat da
ke Kur'ani mai girma.
Idan
muka fahimci haka a karon farko, sai tambaya ta biyu ta biyo baya: shin, ruwa
da muke samu daga sama, wani sabon ruwa ne ful, ko kuwa ruwan da muka sani ne
yake maimaituwa? Idan muka yi la'akari da sakamakon binciken malaman
kimiyya, za mu ga cewa lallai ruwan da muke samu daga sama, ruwa ne da yake
maimaituwa, a wani sabon yanayi mai cike da nishadi da sabuntawa.Watakila mai
karatu yace: "Shin, da gaske wannan magana haka take cikin
Kur'ani?" Amsar ita ce eh. Domin a cikin Kur'ani Allah ya sanar
da mu ne cewa shi ne yake saukar da ruwa daga sama, don amfaninmu da dabbobinmu
da abin da muke shukawa a kasa. Ba wai yanayin ruwan yake sanar da mu ba, sai
dai saukarsa, da cewa shi ne mai saukarwa. Kuma idan ya ga dama sai ya
kame ruwan, kamar yadda mun sha ganin hakan. Kafin mu yi nisa, a nan nake
ganin dacewan sanar da masu karatu wata ka'idar ilmi tsakanin binciken kimiyyar
zamani, da kuma nassoshin da ke cikin Kur'ani. Wannan zai taimaka mana
matuka wajen fahimtar binciken malaman kimiyya, da kuma fahimtar nassoshin
Kur'ani din.
Duk
ayoyin da ke bayanin yiwuwa ko samuwa ko faruwan wasu abubuwa a duniya masu
alaka ta kai-tsaye da fannin kimiyya, sakon da ayoyin ke kokarin isar mana a
takaice shi ne mu san wanda ke haddasa su, ko yake da ikon sanya su faruwa, ko
yake da ikon kame su don hana su tasiri. Wannan tsarin mulki ne na
Ubangiji, wanda ya taskance yadda komai ke faruwa karkashin ikonsa, da yadda
yake tasarrafin abubuwa cikin mulkinsa. Bayan wannan, har wa yau Allah ya
zayyana yadda komai zai faru, da kuma dalilan da za su sa komai din ya faru.
Samuwar wadannan dalilai ne ke sa mai ganin abin a fili ya ga faruwarsu, har a
karshe, idan ba mai imani bane shi, ya dauka wadannan dalilan zahirin su ne
kadai ke sa wannan abin ya faru. Wannan tsari na haddasa faruwan abubuwa
sanadiyyar dalilai bayyanannu, shi ake kira "Cause and Effect
Theory" a kimiyyance.
Mu
sani, Kur'ani ba littafin kimiyya bane, duk da cewa akwai bayanai masu alaka da
kimiyya sosai a ciki. Allah ya saukar da shi ne don shiriya, don a bauta
masa, ba wai sinadaran rayuwa ba. Wannan ne ma yasa littafin ya zo a
tsarin sura-sura, ba babi-babi ba kamar yadda littattafan kimiyya suke. Kuma
kasancewar fannin kimiyya ba wani fanni bane da kowa zai iya gudanar da bincike
har ya gano abin da aka fada a Kur'ani, kuma bincike a fannin kan dauki lokaci
mai tsawo, sai wasu ke ganin kamar akwai cin karo tsakanin wannan fanni da abin
da Kur'ani ke tabbatarwa. Ko kadan babu. Matsalar da ke tsakanin masu
gudanar da wannan bincike da Kur'ani, shi ne na rashin imani ko
samuwarsa. Galibinsu ba su yi imani da Allah ba, don haka duk binciken da
suke yi, ba su danganta sakamakon abin da suka gano ga Allah madaukakin sarki,
sai dai ga dalilai na zahiri da suka haddasa abin. Wannan kuwa ba karamin
hadari bane.
To
amma kowane musulmi ya san cewa Allah ne mahallicin komai, kuma shi ne yake
sarrafa duniya baki daya. A matsayinka na makarancin fannin kimiyya ko mai
karanta rubuce-rubucen malaman kimiyya, dole ne ka kiyaye wannan ka'ida a
kwakwalwarka, don kada ka rudu da dalilan da suke bayarwa kan cewa su ne kadai
ke haddasa abin da ke faruwa, ko ke haddasa samuwar wata halitta ko wani yanayi
da ke maimaituwa. Bayan dukkan wannan, yanzu za mu shiga bayani kan yadda
samuwar ruwa ke maimaituwa a duniya, abin da malaman kimiyya ke kira Water
Cycle, ko Hydrologic Cycle. Wannan bayani ne zai
tabbatar mana cewa lallai ruwan sama da muke samu a duk shekaru ko damina, ruwa
ne da ke maimaituwa a wani yanayi.
Tsarin
Maimaituwar Ruwa a Duniya (Hydrological Cycle)
Kamar
yadda bayanai suka gabata a baya, ruwan da ake samu a duniya, daga na cikin
teku, da wanda ke cikin kogi, da na rafi, da na karkashin kasa, da ruwan sama
da muke samu, da tsaunukan kankara na cikin teku, watau Glacier, da
Kankaran da ke saukowa daga sama lokacin ruwan sama, da dusar kankara (Ice
Pellets, ko Snow) da ake samu a kasashe masu sanyi
irin su Rasha da sauran kasashen Turai, duk abu ne guda daya da ke maimaituwa
lokaci-lokaci, cikin wani tsari da Allah ya tanada, mai cike da ban mamaki ko
al'ajabi. Wannan tsari da ke samar da wadannan nau'ukan ruwa a yanayi uku
– narkakken ruwa, da kankara, da tururin iska mai dauke da ruwa – shi ake
kira Water Cycle ko Hydrological Cycle a
kimiyyance. Wannan tsari yana kunshe da matakai hudu ne muhimmai, masu
maimaita shi a duk lokacin da dalilan da ke samar da su suka samu. Bayan
wadannan bayanai ne mai karatu zai fahimci yadda ruwan sama ke samuwa, da
dalilin da ke sa tekuna da kogi suke yin ambaliya, da yadda ruwa ke taskance
kansa a cikin iska cikin yanayin tururi, sannan ya haura zuwa sararin wannan
duniya tamu.
Matakin
Farko
Wannan
shi ne matakin ma'adana, watau lokacin da ruwa ke taskance ko dai a cikin kogi,
ko a cikin teku, ko a cikin rafi; a yanayin narkakken ruwa yake ko a yanayin
kankara narkakke, watau Melting Ice, da ke cikin teku, ko
daskararre. Sai kuma ruwan da ke cikin karkashin kasa mai bubbuga cikin
teku. Dukkan wannan ruwa yana cikin ma'adana ne, wanda Allah ya samar da
shi don amfanin bayi, kuma shi ne matakin farko na samuwan ruwa a duniya, kamar
yadda bayanai suka gabata.
An
kiyasta cewa akwai ruwa a yanayin gundarin kankara wanda kauri da fadinsa ya
kai nisan murabba'in kilomita 17 (17km2) a nahiyar Antaktika (Antarctica), da
nahiyar Greeland. Wadannan su ne wurare masu matukar sanyi a
duniya. Malaman kimiyya sun ce ba a samun idaniyar ruwa ko ruwan karkashin kasa
a wadannan nahiyoyi, saboda daskarewan ruwan a karkashin kasa. Shekaru
dubu 22 da suka wuce ne aka yi mummunar sanyi a wadannan wurare, inda har
kankara ta mamaye ilahirin kasar Kanada, da Arewarin Amurka, da Arewacin Turai,
da kuma Saiberiya. Wannan kankara ta mamaye wuraren da aka kiyaska sun yi
fadi da nisan murabba'in kilomita miliyan 20 (20m km2).
Daga
cikin ruwan da ke karkashin kasa akwai wadanda suke cikin duwatsu. Wadanda suke
cikin duwatsu masu taushi, watau Sedimentary Rocks, wadanda
kuma aka kiyasta cewa sun mamaye kusan kashi 20 zuwa 40 na duwatsun da suke
cikinsu. Samuwar ruwa a wadannan ma'adanai – na kogi, da teku, da rafi, da
kankara, da karkashin kasa – shi ne matakin farko da ke sawwake samuwar mataki
na biyu, don haddasa tsarin maimaituwar ruwa a duniya.
Mataki
Na Biyu
A
yayin da ruwa ke taskance cikin wadancan ma'adanai na teku ko kogi ko rafi da
dai sauransu, a kullun ruwan na raguwa, yana bin iska a yanayin tururi, har ya
haura zuwa cikin wata ma'adana da ke cikin sararin wannan duniyar ta mu.Wannan
ma'adana ita ake kira Water Vapour, kamar yadda bayani ya zo a
makon baya. Haka ma kankaran da ke narkewa a cikin teku, duk wannan tsari yake
bi.Wannan tsari na bacewar ruwa ta hanyar bin iska a yanayin tururi, shi ake
kiraEvaporation a turancin kimiyya. Haka ruwan zai ta taruwa
zuwa cikin wancan ma'adana ta sararin duniya. Bayan wannan tururin iska da
ke samuwa daga teku ko kogi, akwai wani tururin da ke fitowa daga ramukan jikin
ganyayyaki da ciyayi da kuma kasa mai danshi (ko duk inda aka zubar da ruwa a
kasa), yana haurawa zuwa sama shi ma. Wannan tsari na bacewar ruwa daga
jikin ganyayyaki da ciyayi don bin iska a yanayin tururi, shi ake kira Transpiration a
turancin kimiyya.Dukkan wannan tururi na ruwa da ke bin iska zuwa sama, asalin
ruwa ne da ke ma'adanar da muke da su a wannan duniya – ko dai teku ko kogi ko
kankara ko wanda ke jikin sauran halittu.
Malaman
kimiyya suka ce a kullum ana samun adadin ruwa da yawansa ya kai 1,200 a
ma'aunin kimar ruwa, watau 1,200 cubit km. A kullum sai wannan
adadi na yawan ruwa a yanayin tururi ya bi iska zuwa ma'adanar ruwa da ke
sararin duniyarmu. Don haka malaman kimiyya suka ce, da a ce za a samu
tangarda har wannan adadi ya daina haurawa sama, nan da kwanaki 10 ma'adanar da
ke sararin duniyarmu za ta kafe, a rasa ruwa a cikinta. Wannan ke nuna mana a
fili karara cewa, Allah ya tanada wa bayinsa dukkan abin da za su dogara da shi
na arziki, tare da tsarin samuwarsa. Wannan zance yana nan cikin Suratul Hijri
– inda Allah ya ce dukkan wata arziki taskarta na wajensa ne, kuma ba ya saukar
ta da ita ga bayinsa sai iya gwargwadon yadda zai zama maslaha a gare su.
Manyan
dalilai na fili da ke sawwake wannan tsari na bacewar ruwa cikin iska a yanayin
tururi da ke haurawa zuwa ma'adanar sararin duniyarmu kuwa, su ne tsananin
zafin rana da haskenta, da iskar da ke bugawa – a tudu ko a saman teku – da
inuwar da ke saman shuke-shuke ko ciyayi, da kuma danshin kasa ko duk inda aka
zubar da wani ruwa a nan duniya inda muke rayuwa. Wadannan dalilai ne ke
haddasa samuwar wadannan yanayi guda biyu na Evaporation da
kumaTranspiration. Kuma wannan mataki ne ke haifar da matakin
samuwar ruwa na uku, watau abin da ake kira Precipitation.
Mataki
Na Uku
Wannan
mataki kuwa shi ne matakin saukar ruwa daga sama, ko Precipitationkamar
yadda malaman kimiyya ke ambatonsa. Kafin mu ci gaba, na san da yawa daga
cikinmu mun sha jin cewa, a kimiyyance abin da ke haddasa ruwan sama shi ne
tururin teku ko kogi da ke haurawa sama, sannan ya zubo. Sai dai da yawa daga
cikinmu muna karyata wannan ka'ida ta kimiyya, amma kuma hakan shi ne abin da
yake kusa da daidai. Babban kuskuren da muke yi kuwa shi ne, muna dauka
cewa ruwan da ke zubowa daga sama, yana zuba ne daga asali ko jikin bangon
saman da muke gani. Wannan kuskuren fahimta ne babba. Domin hatta a
cikin Kur'ani mai girma Allah ya ambaci jihohi guda biyu ne wajen zuban ruwan
sama. Amma kuma dukkan malaman tafsiri sun yarda cewa jihohin nan guda
biyu da Allah ya ambata, abu ne guda daya, ko jiha daya ne yake nufi. Allah
ya ambaci cewa shi ne yake saukar da ruwa "daga sama". A wasu
wuraren kuma ya ambaci cewa, shi ne ya ke saukar da ruwa "daga
giragizai." Malaman tafsiri suka ce ya ambaci sama ne don nufin alaka
da nasaba, dangane da inda dan adam ke zaune. Amma asali ruwa na zuba ne
daga jikin giragizai ba daga can asalin sama ba. Amma an ambaci sama ne
saboda a can giragizai suke; ma'ana a saman dan adam. Bayan nan, da yake zamani
ya kawo samuwar jirgin sama, duk wanda ya taba hawa jirgin sama yayi doguwar
tafiya, zai ga cewa sai jirgin ya "keta hazo" ko
"giragizai" kafin ya daidaita a sama ya ci gaba da tafiya. Abin
da yin hakan ke nufi kuwa shi ne, da za a yi ruwa a duniya – a kowane bangaren
duniya ne kuwa – wadanda ke cikin jirgin nan ba za su sani ba sai sun
sauka. Domin ruwan daga jikin girgije yake zuba, shi kuma jirgin ya wuce
inda girgijen yake. Idan mun fahimci wannan tsari, sai mu koma kan
bayaninmu.
Yadda
Ruwan Sama ke Samuwa
Da
zarar wannan ma'adana mai dauke da danshin ruwa a yanayin tururi (watauWater
Vapour) ta tumbatsa, sai ruwan ya sake saukowa kasa a yanayi
uku.Yanayin farko shi ne yanayin ruwan sama, kamar yadda muka sani. Yanayi na
biyu kuma shi ne yanayin kankara; ko dai wanda ke zubowa a tare da ruwan sama
(watau Ice Pellets), ko kuma dusar kankara da ke zuba a wasu
kasashe inda sanyi ya kai matuka (watau Snow). Sai yanayi na
uku kuma shi ne yanayin raba; watau danshin ruwa mai sanyi da ke zuba cikin
dare (ko Dew kimiyyance).Wannan ruwa da ke zuba, yana zuba ne
a kullum, kamar yadda wancan tururin danshin ruwa da ke haurawa ma'adanar ruwa
a sama a kullum. Bayan nan, malaman kimiyya suka ce a kowace rana a kan
samu a kalla adadin yawa da fadin ruwa a ma'aunin yawa, wajen 300 (watau 300
Cubic Km). Kuma cikin wannan adadi na ruwa da ke zuba a matsayin ruwan
sama, ko kankara, ko raba, kashi daya cikin uku (⅓) ne kadai ke zuba a gundarin
kasa, sauran kashi biyu bisa ukun (⅔) na zuba cikin teku ne, ko kogi, ko kuma
rafukan da muke da su a duniya – su sake komawa cikin sama a yanayin da
bayaninsa ya gabata. Sai dai kuma, na san mai karatu zai so sanin yadda
ruwan sama ke sauka, a kimiyyance.
Kamar
yadda bayani ya gabata, ruwan da ke zuba daga sama shi ne ruwan da ke makare
cikin ma'adanar danshin ruwa da ke yanayin tururi a sararin wannan duniyar
tamu, watau Water Vapour kenan. Daga nan sai su zubo,
amma ba kai tsaye suke zubowa ba. Domin ruwa, kamar yadda yake, yana
zubowa ne daga jikin giragizai, watau Clouds a
turance. Su wadannan giragizai a sama suke, haka ma wannan ma'adana ta
sararin duniyarmu. Sai dai kuma, sabanin giragizai da dan adam ke iya
ganinsu da ido, ita wannan ma'adana a yanayin iska take, a makare da ruwa cikin
yanayin tururi mai danshi.
Tsakanin
sararin samaniyar wannan duniyar ta mu da saman tekuna, akwai iska nau'uka
daban-daban. Akwai iskar da ke kada ruwan teku har a samu taguwar ruwa,
sanadiyyar juyawar bigiren rana da wata. Wannan iskar kan yi sanadiyyar
ambaliyar ruwa. Akwai iskar da ke kintsa kasar da muke takawa kafin zuwan
ruwan sama. Akwai iskar da Allah ke kado ta zuwa duniya a matsayin bushara
gare mu don samuwar ruwan sama. Akwai iskar da ke taskance ruwa a yanayin
danshi kamar yadda bayanai suka gabata. Akwai iskar da ke hado kan
giragizai waje daya. Akwai iskar da ke yin barbaran giragizai, har su cika da
ruwa, sannan ruwan ya zubo kasa. Akwai iskar da ke rarraba giragizan da ke
shake da ruwa zuwa jihohin duniya daban-daban, iya yadda Allah ke
so. Sannan kuma akwai nau'in iskar da ke kora giragizai masu dauke da
ruwa. Dukkan wadannan nau'ukan iskoki suna nan, kuma ba iyakansu ba kenan,
sai dai wadanda suka danganci ruwan sama ne wadannan. Kuma wani abin
sha'awa shi ne, dukkansu Allah ya yi bayaninsu, da yanayin aikinsu a cikin
Kur'ani.
Da
zarar Allah ya nufi saukar ruwa, sai ya aiko iskar da za ta kintsa kasa don
karban ruwan da ke tafe. Sannan sai iskar da ke bushara ta biyo
baya. Ita ce iskar da ke zuwa da karfi, cike da kura ko tarkacen da take
dibowa. Sakon da take aiko mana shi ne, "kowa ya kintsa kayansa, ga
ni'ima nan tafe." Wannan iska ce ta bushara, musamman ga al'ummar da
aka de ba a musu ruwa ba, ko suke fama da fari. Daga nan kuma sai wannan iska
mai makare da ruwa a yanayin danshi ta kada, sannan ta yi barbarar giragizai,
ta cika su da ruwa. Nan take sai ka ga giragizai sun yi baki kirin, sai
kaji rugugi, sai cida; ga kuma iskar bushara na bugawa. Daga nan sai iskar
da ke kada giragizan su fara nasu aikin, sai ruwan sama ya fara zuba. Daga
nan sai iskar da ke rarraba wannan ruwa ta biyo baya, ta rika warwatsa
giragizan zuwa jiha ko bigiren da aka nufe su da samun wannan ni'ana. Nan take
sai ka ga hadari ya fara zama fari daga launin bakin da yake a farko. Saboda
ruwa ya fara zuba. Dangane da bayanan da suka shafi nau'ukan iska, da
yadda suke barbarar giragizai, da rarraba su, da kora su, mai karatu na iya
duba wadannan ayoyin Kur'ani: Suratul Hijri, aya ta 22; A'raaf, aya ta
57; Noor, aya ta 43 da 45; Furqaan, aya ta 48 da 49; Room, aya ta 48.
Ta
yiwu mai karatu ya ce me yasa ruwan sama ke zuwa da kankara, kuma ruwan da
sanyi yake zuwa, haka ma kankaran? Kuma hatta raba da ke sauka cikin dare,
da sanyi yake zuwa. Me yasa? Fahimtar haka abu ne mai sauki. Domin idan ba
a mance ba, a kasidar farko na sanar da mu cewa wannan duniya ta mu Allah ya
ajiye ta ne a wani bigire matsakaici, wanda ke dauke da yanayin zafi ko sanyin
da suka yi daidai da yanayin dabi'a da rayuwar halittu. Wannan yanayin
zafi da sanyi su ne suke sa duk wani ruwa da ya bi iska ya haura sama a yanayin
tururi, ya zama mai sanyi, a wasu lokuta ma har ya daskare. A wasu
duniyoyin, musamman duniyar Satun, babu ruwa narkakke, saboda yanayin wurin ya
wuce kimar da za a samu ruwa narkakke kamar yadda muke da shi a
duniyarmu. Don haka duk ruwan da ke makare a sararin duniyar Satun,
gundarin kankara ne, wanda ba a tunanin ranar fashewa balle narkewarsa. Dangane
da duniyarmu kuwa, tunda akwai sabanin yanayi madaidaici, don haka muke samun
ruwa narkakke da wanda ke yanayin kanka, da kuma raba, da ma ruwan da ke
yanayin danshin tururi da ke bin iska.
Har
wa yau, mai karatu na iya tambayar dalilan da suka sa ake samun canjin yanayin
damina tsakanin kasashe, ko nahiyoyin duniya. Shi ma amsar wannan ba nesa take
ba. Babban dalilin da ke haddasa hakan shi ne jujjuyawan lokutan dare da
yini, da samun canji a yanayin bigiren rana da wata. Da kuma tsarin
juyawan duniya a kwanakin shekara. Wadannan, na tabbata, suna cikin
bayanan da muka karanta cikin littafin Dakta Adnan, na Gwagwarmaya kan Ilmin
Sararin Samaniya. To, bayan saukar ruwan sama, sai me?
Mataki
na Hudu
Kashi
biyu cikin uku (⅔) na ruwan da ke saukowa daga sama – a yanayin narkakken ruwa,
ko kankara, ko raba - yan zarcewa ne cikin tekuna, da koguna, da kuma
rafuka. Kashi daya cikin ukun (⅓) ne kawai ke zuba a saman kasa.Wannan kaso kan
gangara cikin tekuna shi ma daga inda ya zuba, kasa tasa iya shanta. Wadannan
rafuka sukan cika su batse, daga nan su antayar da raran ruwan zuwa cikin
teku. Kamar yadda muka sani, dukkan tekunan duniya a jone suke da juna ta
wasu hanyoyi. Sannan dukkan kogunan da ke cikin kasashenmu, da rafukan da
ke ciki, duk karshensu yana hadewa ne da wadannan manyan tekuna da ke tsakani
ko bayan kasashen duniya. Dukkan kankaran dake fadowa a kasa, sukan narke,
kuma ruwan kan gangara zuwa cikin rafuka ko kogunan da muke da su. Da
zarar sun antayo cikin tekuna, sai a sake samun maimaituwan wannan tsari kamar
yadda bayanai suka gabata a baya. Wannan shi ne mataki na karshe.
Daga
bayanan da suka gabata, mai karatu zai ga cewa lallai ruwan sama da ake samu,
da sauran hanyoyin samun ruwa a duniya, duk abu ne guda daya, wanda ke
maimaituwa, cikin kudura da iradar Ubangiji. A mako mai zuwa za mu ci
gaba, inda bayanai za su zo kan nau'ukan sinadaran da ke dauke cikin ruwa;
narkakke ne, ko daskararre a yanayin kankara, ko kuma wanda ke yanayin tururi a
cikin iska.
Source: Click here
2 Comments
Aiki yayi kyau nazari nada matuqar faida
ReplyDeleteMun gode sosai a cigaba da ziyartar shafin mu domin samun fa'idoji daban daban kuma yi sharing wa abokai da yan uwa
DeletePost a Comment