A wasu kasashe na ketare, ilimi suna yi masa hangen wasu al’amari ne mai kyau ga kowace Jama’a kuma kowa ne mutum na da hakken ya nema a bashi. Hakan yasa daliban kasashe daban daban na duniya suke hangensu a matsayin wani jigo na tsarin matakin ilimi na sama da sakandare na kasashensu.
Wadannan kasashen sun bada damar yin karatu a makarantunsu na (Universities) a kyauta ga daliban kasa da kasa (International Students).
Hakan yasa muka zabo wasu daga cikin makarantun (Universities) da ke bada damar karatu ga daliban kasashen duniya daban daban na duniya.
Mun zabi makarantun da ke bada damar karatu kyauta ga (International Students) wadanda sune suka samu matakin daraja mafi koli a duniya ta hanyar QS World University Rankings – topuniversities.com.
ABIN KIYAYEWA
Ku sani cewa wannan bayani da muka saka muku a wannan shafi zai iya canjawa a ko wane lokaci. Makarantun ko Gwamnatin Tarayya kan iya canja tsarin zuwa ga karbar kudin makarantar ga daliban kasashen duniya nan zuwa gaba.