ADDU°AR KARIYA DAGA CIZON KUNAMA!!!


Watarana daya daga cikin Sahabban Manzon Allah S A W. ya zauna  karkashin wata bishiya sai Kunama ta ci jeshi sai aka zo dashi wajen Manzon Allah S A W domin ya masa magani, bayan ya gama masa magani sai Annabi yace dashi shin safiyar yau kayi Addu°ar safiya? sai Sahabin yace A A Yaa Rasulullah sai Annabi S A W yace da ace ka karanta 

بسم الله اللذی لا يضر مع اسمه شيء فی الارض ولا فی السماء وهو السميع العليم
To da ba abinda zai sameka a wannan yini na chutarwa.

bisa wannan Dalili ne Malamai suka ce wannan itace Addu°ar da bawa zai yi Allah ya kareshi daga sharrin mai Sharrin a ko wace Rana mai buqatar ganin wannan ya duba a littafin DU°A°UL MUSTAJABH