JINJINA TA MUSAMMAN GA BABA BUHARI UBAN TALAKAWA

ZUBAIRU IBRAHIM ASSADA

Maganar gaskiya duk wani mai bibiyar matsalolin Zamfara da Kaduna, Katsina nd Borno musamman a °Yan kwanan nan zai fahimci matakin da gwamnatin Tarayya take dauka akan °Yan Ta°Addan mataki na kare Dangi domin anzo gabar da za°a Ruguzasu sannan Dan Arewa zai yi farin ciki kuma zai kara jajircewa da Addu°a ga Shugabanni da Jami°an tsaro cewa Allah ya basu Nasara akan wadannan Mutane bata gari, matuqar Mutun ba Munafuki bane kuma marar kishin kasa sannan muna kara godiya ga Allah Madaukakin Sarki maji Roqon bayinsa daya fara kawo mana sauqin wannan hali da muke ciki bisa Addu°armu da kuma Nasarar samun Shugabanni masu Tausayinmu Tabbs kamar yadda wani Mawaqin Baba Buhari yake cewa ZABINKA YAZAMO ALKHAIRI BAKA BARMU MUNJI KUNYA BA, SAI BUHARI KO GOBE Wannan magana gaskiya ce haka take Saboda akwai Makiya Allah masu zagon kasa wa Kasa suna nan har sun fara ce mana kun gani ba wannan kashe kashe da ake yi NEXT LEVEL kenan, Yunwar ma NEXT LEVEL kenan, Rashin Kudi a hannun Mutane NEXT LEVEL kenan, hatta zafin nan fa da ake yi wani sai kaji yace maka NEXT LEVEL kenan, saboda tsabar Jahilci kuma abinda Talakawa basu gane ba mafi yawa wallahi Baba Buhari bazai taba sanya hannu ga wani aikin Rashin gaskiya ba, Saboda Mutun ne mai tsayayyen Ra°ayi sai abinda yafi karfinsa muna kara masa Addu°a mafi tsada Yaa Ubangijin Sammai da Kassai ka kara karfafa karfin wannan Shugaba namu kuma ka bashi Mashawarta na kwarai kuma ka Ruguza Daular duk wasu Azzalumai masu kiyayya dashi da kasa baki daya Ameeen Yaa Allah.


             ZUBAIRU IBRAHIM ASSADA