"Kun raba mini hankali" wai an ce wa rago ya sha fura ya
kama hanyar gona.Domin shi abin da yafi so, a matsayinsa na rago wanda ba ya
son ko kadan ya motsa gabobin jikinsa, shi ne, ya sha furan, sannan ya kwanta
ko ya zauna ya kama hira da jama'a. To ta yaya aka yi hankalinsa ya rabu kashi
biyu, alhalin ayyukan da ake nemansa da yi ba a lokaci daya aka ce ya yi su
ba? An ce ya sha fura. Aikin farko kenan. Sannan aka ce masa ya kama
hanyar gona, watau bayan ya sha furan kenan. Wannan shi ne aiki na biyu.
Kuma kowanne a lokaci daban-daban zai aiwatar da shi. Watakila mai karatu
bai taba damuwa da sanin dalilin da yasa rago yace an raba masa hankali ba.
Masu karatu, a yau shafin Kimiyya da Kere-kere zai kutsa wani fanni
mai matukar muhimmanci a rayuwar dan adam da sauran kayayyakin sadarwa na
zamani. Wannan fanni kuwa shi ne bangaren da ke lura da tsarin gudanarwar
kwakwalwar dan adam wajen aiwatar da ayyuka fiye da daya, a kuma lokaci daya,
cikin yanayi daya. A turancin malaman kimiyyar bangaren kwakwalwa da
tunanin dan adam, wannan fanni shi ake kira "Human Brain
Multitasking." Ba za mu tsaya da bayani kan yadda dan adam ke
fuskantar kalubale wajen aiwatar da ayyuka fiye da daya a lokaci daya kadai ba,
za mu gwama kwarewarsa (in har ya kware kenan) da yadda masarrafar sarrafa
bayanai ta kwamfuta (Computer Processor) ke aiwatar da nata
ayyukan cikin lokaci daya. A karshe za mu fahimci dalilin da ya kai rago ga
cewa: "Kun raba mini hankali," sa'adda aka ce masa ya sha fura,
sannan ya kama hanyar gona.
Kwakwalwar Dan Adam
Kwakwalwar dan adam (watau Brain) wata
masana'anta ce, ma'adana ce, sannan kuma masarrafa ce ta musamman. Yadda
aka yi ta kasance masana'anta kuwa shi ne, aikin ta ne sarrafa bayanan
abubuwan da dan adam ke alaka da su – mutane ne, kayayyaki ne, bayanan ilmi ne,
dabbobi ne, ko ma dai mene ne - wajen tantance launinsu, da yanayinsu, da
tsarinsu, da kimarsu, da adadinsu, tare da kawo su a duk lokacin da dan adam ya
neme su ta hanyar tunani. Har wa yau aikin kwakwalwa ne tantancewa
tsakanin abubuwa guda biyuko fiye da haka da ke gabanta. Aikin ta ne auna
kima da yanke hukuncin wanda ya fi wajen girma ko karko ko duk wani abin da aka
bata a matsayin mizani da zabi. Duk bangaren masana'anta ce ke wannan
aikin.
Mun kuma ce kwakwalwa ma'adana ce, sosai kuwa. Duk abin da ka
taba gani, da wanda ka taba da hannunka, da abin da ka ji da kunnuwanka na
labari ko sauti, da abin da hancinka ke susnsuno maka, duk aikin kwakwalwa ne
ta taskance maka yadda abin yake. Ita ce za ta adana maka warin da ka ji
ko doyi a yayin da ka wuce wata bola. Da zarar kuma ka zo ba da labari, nan
take za ta tuno maka irin warin da kaji, har ka iya gaya wa mutane. Idan
sauti ne mai firgitarwa, za ta iya tuno maka da yadda yake, sannan ka sifata wa
jama'a cewa sauti iri kaza na ji, mai firgitarwa. Idan labari ne aka baka
na wani abu mai girma, zuciya za ta sifata maka girman, sannan kwakwalwarka
kuma ta adana maka wannan sifa da ka baiwa abin da aka sifata maka ko da kuwa
baka taba ganinsa ba. Ida kuma kai ganau ne a inda wani abu ya taba
faruwa, duk aikin kwakwalwa ce taskance maka labarin baki dayansa, sannan ka
samu saukin watsawa idan bukatar hakan ta taso.
Sannan kwakwalwar dan adam masarrafa ce ko wajen gudanarwa, saboda
muhimmancinta wajen taya dan adam gunadar da ayyukan da yake fuskanta a
rayuwarsa ta yau da gobe. Idan aiki guda kake yi, hankalinka zai koma
kansa ne kacokam. Idan kuma ayyuka biyu ne a gabanka, duk wanda ka fi
bashi muhimmanci shi ne za ka fi yinshi da kyau. Me yasa? Dalilin na
tafe. A takaice dai, duk abin da ka tashi gudanarwa, to kwakwalwa ce za ta
taimaka maka da lokaci, mai dauke da hankalin lura, don aiwatar da wannan aiki.
A takaice dai, wadannan ayyuka da bayaninsu ya gabata, suna samuwa ne ta
bangarorin kwakwalwa daban-daban. Akwai bangaren da aikinsa ne kawai adana
bayanai.Akwai bangaren da aikinsa ne tuna abubuwan da suka gabata. Akwai
bangaren da aikinsa ne gudanar da ayyuka ta hanyar samar da lokacin lura da mai
aikin ke yi, da dai sauransu.
Bincike Cikin Wannan Fanni
Wannan fannin ilmi na tsarin gudanarwa ta kwakwalwar dan adam,
watau Human Brain Multitasking, ya fara shahara ne tun
shekarar 1990. A takaice dai sabon fanni ne da aka bambaro shi daga fannin
ilmin kanikancin kwamfuta, watauComputer Engineering. Wadanda suka
fara gudanar da bincike mai zurfi a kanshi sun hada da Mayer da Moreno, wadanda
kwararru ne a fannin Gwajin Tsarin Tunanin Dan Adam, watau Experimental
Psychology. Sun gudanar da bincikensu ne kan tasirin wannan tsari na
cakuda ayyuka fiye da daya a kwakwalwa a lokaci daya, ga karatun dalibai a
makarantu. Sakamakonsu ya nuna cewa lallai yin hakan na cikin ababen da ke
kashe kuzari da karshashin dalibai, tare da rage musu kokari da kwazonsu cikin
karatu. Sai kuma Juanco da Cotton, wadanda suka dubi tasirin hakan wajen
rayuwar dan adam baki daya.
Bayan su, an samu Richard Hallowell, wanda shahararre ne a fannin
Ilmin Dabi'a. Shi ne ya dada gano cewa, yawan damun kwakwalwa da ayyuka fiye da
daya a lokaci daya kan haifar da kurakurai cikin hukuncin da kwakwalwa za ta rika
bayarwa, ko cikin ayyukan da kwakwalwar ke gudanarwa. A nata bangaren
kuma, Monica Luciana da ke Jami'ar Minnesota a kasar Amurka ta gano cewa, duk
da cewa kwakwalwar dan adam ba za ta iya daukan ayyuka fiye da biyu ba a lokaci
daya, amma idan aka dabi'antar da kwakwalwar ta hanyar maimaci da karantarwa
kafin shekaru 16 zuwa 17 na farkon rayuwa, yara na iya sabawa da irin wannan
tsari. Amma hakan sai ya dauki lokaci mai tsawo kafin kwakwalwa ta
saba. Wannan sakamako har wa yau shi ne sakamakon da Paul E. Dux da ke
Jami'ar Verderbilt ya fitar shi ma; cewa lallai hakan na iya yiwuwa, amma sai
da dan karen tarbiyya na tsawon lokaci. Sai kuma Koechlin da ya gabatar da
nasa binciken cikin 'yan kwanakin da suka gabata, inda shi ma ya gano cewa
kwakwalwa ba za ta iya daukan ayyuka sama da guda biyu ba a lokaci daya.
Tsarin Gudanarwa a Kwakwalwa
Kamar yadda bayani ya gabata a baya, daga cikin ayyukan kwakwalwar
dan adam akwai taimaka masa wajen gudanar da wani aikin da ya sa a gaba, wajen
samar masa da lokacin lura. Misali, idan mutum yana cin abinci, hankalinsa
gaba daya kan koma kan abin da yake ci ne. Daga kwanon abincin, zuwa cokalin,
da abincin da yake dibawa, da kimar lomar da yake yi. Da zarar an bugo
masa waya, ya dauka ya fara amsawa, sai tsarin lura da gudanarwar kwakwalwarsa
ya rabu biyu. Kashi daya na wajen abincin da yake ci, kashi dayan kuma
yana kan wayar da yake yi. Bangaren kwakwalwar da ke lura da wannan aiki
kuwa shi ne bangaren da ake kira "Medial Prefrontal Cortex"
(MPC). Aikin wannan bangare ne ya tsaga ko raba wa dan adam lokacin
lura da wani sabon aikin da ya kama yi, bayan na farko. Idan ya ci gaba da cin
abinci kuma yana hira da abokinsa ta wayar salula, to, wadannan ayyuka guda
biyu da yake yi a lokaci daya za su rika gudanuwa ne iya gwargwadon kimar da ya
baiwa kowannensu. Idan hankalinsa ya fi komawa kan abincin, wanda ake
magana da shi a wayar salular zai iya ganewa, domin tsarin yadda ake amsa masa
tambayoyinsa, ko yadda ake bashi labari ko bayanan da yake nema daga wajen
abokin maganarsa za su canza.
Wannan ya kawo mu ga binciken malaman kimiyya a bangaren kwakwalwa
da tunanin dan adam. An tambaye su: shin, mutum na iya gwama ayyuka biyu a
lokaci daya yana yi, sannan kowanne daga cikin wadannan ayyuka guda biyu su
yiwu ta dadi, kuma daidai? Wannan tambaya ce mai tsauri, kuma amsarta ta
danganci wanda abin ya shafa ne. Amma dai, sakamakon binciken da suka
gudanar na nuna cewa, kowane dan adam, iya gwargwadon karfin tunaninsa, yana
iya gwama ayyuka guda biyu masu bukatar lokaci da lura a lokaci guda, kuma su
yiwu daidai – ba tare da wani bangaren aiki ya samu matsala ba.Wannan tsari shi
ake kira "Hyperthreading on Single Core." Amma da
zarar wani aiki na uku mai bukatar lokaci da lura ya shigo, sauran ayyukan duk
za su rushe, a kasa gudanar da su yadda ya kamata.
Wannan shi ne sakamakon binciken da wani kwararre kan kwakwalwa da
tsarin tunanin dan adam dan asalin kasar Faransa mai suna Etienne Koechlin ya
fitar, bayan binciken da ya gudanar. Ya ce hakan na yiwuwa ba tare da an
samu tasgaro a kowane bangare ba. Amma da zarar an hada ayyuka guda uku
masu bukatar lokaci da lura a lokaci daya, nan take kowane aiki zai samu
matsala. Ya ce domin bangaren Medial Prefrontal Cortex da
ke sarrafa wa dan adam lokaci ko raba masa hankali kan aikin da yake yi na iya
yin hakan ne kawai kan ayyuka guda biyu. Amma da zarar an samu wani aiki na uku
ya shigo, to, rabuwar hankalin zai yi yawa, har ayyukan gaba daya su kasa
gudanuwa yadda ake so.
Wannan Malami ya ba da misalin ayyuka biyu. Na farko shi ne
mutumin da ke tukin mota, sannan ya kama hira a wayar salularsa. Na biyu
kuma wanda ke halin tafiya a kasa, sannan ya kama hira da wani a wayar
salularsa. Ya ce duk da cewa wadannan ayyuka guda biyu ne, amma kamar
tukin mota yana amfani da bangaren lura a kwakwalwa sosai, don haka idan wani
aiki ya shigo, ana iya samun matsala wajen tuki. Shi yasa ma a dokar
tuki ba a yarda direba ya rika buga waya a halin tukin mota ko babur
ba. Amma kuma, a daya bangaren, mace na iya buga wayar salula a halin dafa
abinci. Wannan ba matsala. Amma ga mutumin da ke tafiya a kasa,
sannan yana magana a wayar salula, wannan akwai hadari. Domin hankalinsa
zai rabu matuka, ya koma kan wayar da yake yi har ya fada cikin
hadari. Haka ya taba faruwa ga wata baiwar Allah a daya daga cikin biranen
Amurka, inda take buga waya a yayin da take tafiya, a karshe ta rifta cikin
wata lambatu, ta guggurje jikinta.
Malam Koechlin ya nuna cewa, abin da yasa hada tukin mota tare da
buga wayar salula a lokaci daya ke da hadari mai girman gaske shi ne, tsarin
gudanar da aiki fiye da daya (watau Multitasking) a kwakwalwa
na bukatar lokacin lura ko kulawa(Attention) mai girman gaske a
yayin da ake gudanar da ayyukan tukin mota. Don haka, idan aka hada tukin
mota da wani aiki mai bukatar lura da kulawa irin (kamar hira a wayar salula),
to, za a samu matsala da ayyukan tukin mota nan take. Domin a tukin mota
akwai tunani mai zurfin gaske, da kallo mai cike da lura, da aiki da ma'aunin
kimanta tazara (misali ga direban da ke son cinma motar da ke gabansa don wuce
ta, alhali ga wata mota a gefen hagunsa mai zuwa).Sannan kuma ga ayyukan kafafu
da hannu (wajen taka birki, ko kara gudu, ko matsa kuloc, ko sanya giya)
wadanda su ma suna bukatar shiriya daga kwakwalwa don sanin lokacin da yafi
dacewa a yi su. A karshe kuma ga aikin ji; sauraron odar motocin da ke
tafe, ko wacce ke kokarin wuce shi, ko kuma wani kara na matsala da motarsa ka
iya bayarwa a halin tafiyarsa. Dukkan wadannan ayyuka suna samuwa ne daga
kwakwalwa. In kuwa haka ne, ashe direba mai tuki ba karamin aiki yake yi
ba a lokaci guda. Dakta Koechlin yace idan direba ya kama buga waya a halin
tafiya da yake yi, hankalinsa zai rabu biyu. Idan mota ta bukaci
hankalinsa (misali wajen taka birki, ko sanya giya, ko matsa kuloc), kafin
hankalinsa ya dawo kan tukin, komai na iya faruwa.
Domin tsarin da ke juyo hankalin mutum a kwakwalwar dan adam daga
wani aiki zuwa wani, watau Context Switch, ba ya yin hakan
farat daya, sai ya dan dauki wani lokaci. Kuma kafin har ya juyo hankalin
zuwa aikin da ke bukatarsa, komai na iya faruwa. Shi yasa ake samun hadari
mafi muni ga direbobin da ke buga waya a halin tuki. Da za ka tambayeshi
bayan faruwar abin, zai ce maka: "…kafin in canza giya ne..ko kafin in
taka birki ne…ko kafin in kawar da kan motar ne…"Waya yake yi, hankalinsa
ba ya tare da shi wajen tukin, dari-bisa-dari. Shi yasa a kasashen turai
ma, laifin direban da aka kama shi yana tuka mota sannan yana buga waya, ya fi
na direban da aka kama shi a buge da barasa ko giya girma.Wannan tsari na Context
Switch ya fi inganci a masarrafar gudanarwa ta kwamfuta fiye da na
kwakwalwar dan adam. Domin a tsarin kwamfuta, da zarar ka bukaci
komawa kan wani aikin daga wanda kake kai, cikin kasa da dakika guda
(watau 1 second) ta koma da kai nan take.
A daya bangaren kuma, wannan Malami yace mai tukin mota na iya hada
tuki da sauraro a lokaci daya, babu laifi kan wannan. Domin, a cewar
Malaman Kimiyya, hada aikin sauraro da ayyukan tuki ba zai raba hankalin direba
ta yadda zai zama da matsala ba. Domin sauraro abu ne guda daya. Amma
magana a wayar salula kuwa, abubuwa ne da dama. Akwai sauraro a
ciki. Akwai magana a ciki. Sannan akwai bukatar hankali don fadin
abin da ake bukatar ya fada, ko yanke wata shawara, ko kuma abin da ake gaya
masa na iya mummunar tasiri a kan tunaninsa, wanda idan haka ta kasance kuma
sai ya yi mummunar tasiri kan ayyukan tuki, daga nan kuma sai komai ya lalace.
A yayin da kuma yayi gwaji kan samuwar aiki na uku a kwakwalwa
kuma, Malam Koechlin yace sakamakon bincikensa ya nuna cewa, duk wani aiki na
uku da ya samu a kwakwalwa, wanda ke bukatar lura da gudanarwa bayan wasu
ayyuka biyu da ake da su a farko, aiki daya daga cikin ukun zai rasa gurbin
lura daga kwakwalwa baki daya. Wannan zai sa hankali ba zai koma kan aikin
ba, balle har a samu wata fa'ida mai kyau daga gare shi. Misali, mutum ne
ke cin abinci, sai aka bugo masa waya, ya dauka ya kama magana, sannan a cikin
wayan ya bukaci yayi rubutu, aka miko masa takarda da biro ya kama
rubutu. Wadannan ayyuka guda uku duk aikin gudanar da su na cikin
kwakwalwa ne baki daya.Kowanne daga cikinsu kuma an tanada masa lokacin lura da
mai aikin zai ba aikin. A farko dai lokacin lura guda daya ne aka tanada
masa, shi ne aikin cin abinci. Da ya dauki waya ya fara magana kuma, sai
nan take kwakwalwarsa ta tanada masa lokacin lura kan wannan aiki; ma'ana aka
raba wancan lokacin nasa na cin abinci zuwa kashi biyu. Da ya bukaci fara
rubutu kuma, sai nan take kwakwalwa ta tsuke lokacin lura na daya daga cikin
ayyukan da yake yi, don bashi damar aiwatar da wannan aiki na uku. Duk da
cewa zai iya ci gaba da yin waya, yana rubutu, sannan yana daukan laumar tuwo
yana jefawa a bakinsa, amma ayyukan ba za su tafi daidai ba. Ko dai ya
samu matsala cikin wayar da yake yi. Ko ya samu matsala wajen rubutu. Ko
kuma ya samu matsala wajen abincin da yake ci. Wannan ke nuna mana cewa
tsarin gudanarwa na kwakwalwar dan adam, watau Human Brain
Multitasking, ba zai iya daukan ayyuka fiye da biyu ba a lokaci guda.
Tsarin Gudanarwar Masarrafar Kwamfuta
A daya bangaren kuma, Masana masu bincike sun yi kokarin kwatanta
tsarin gudanarwar kwakwalwar dan adam (Human Brain Multitasking) da
tsarin gudanarwar masarrafar kwamfuta (Computer System
Multitasking), don gano bambancin da ke tsakanin tsare-tsaren biyu, da
kuma sanin wanne ya fi inganci.A takaice dai sakamakon da aka fitar ya nuna
cewa lallai tsarin gudanarwar masarrafar kwamfuta ya fi saurin gudanarwa, da
inganci wajen tsarin juyawa daga wani aiki zuwa wani (watau Context
Switch). Wannan ba ya nuna cewa kwakwalwar kwamfuta ta fi ta dan
adam. Ko kadan ba abin da ake nufi ba kenan.Kwakwalwar dan adam ta kasance
mai saibi ne wajen juyawa daga wani aiki zuwa wani saboda asalin yanayinta
kenan. Da kuma cewa, sabanin masarrafar kwamfuta wacce kera ta ake yi kan
wani tsari guda daya tilo, kwakwalwar dan adam wani irin muhalli ne mai karbar
sauyi a kowane lokaci. Kamar yadda ba a iya haifar mutum da tarin ilmi a
kwakwalwarsa sai a hankali yake tara su, ko tsarin tunaninsa ya danganci iya
gwagwarmayarsa da jama'a ne, ko irin tsarin rayuwar da yake yi ko kasancewa
cikinta, to haka kwakwalwarsa ke kasancewa. Amma tsarin gudanarwar
masarrafar kwamfuta ba haka take ba. Tsarinta guda daya ne, shi ne a duk
sa'adda ka bukaci ta juya daga wannan aiki zuwa wani, nan take za ta iya
juyawa.
Bayan haka, masarrafar gudanarwar kwamfuta, watau Computer
Processor, kala-kala ne. Akwai kwamfutar da ke zuwa da masarrafar
gudanarwa guda daya, watau Single Core Processor. Sai kuma
kwamfuta mai zuwa da masarrafar gudanarwa guda biyu, watau Dual Core
Processor. A wannan zamani akwai wasu nau'ukan kwamfutoci na musamman
har wa yau wadanda ke zuwa da masarrafar gudanarwar kwamfuta guda
hudu. Wadannan ake kira Multicore Processors. Idan ka
kebe kwamfuta mai zuwa da masarrafar gudanarwa guda daya – watau Single
Core Processor – sauran nau'ukan suna da ingancin da dan adam ba zai
taba tunaninsu ba wajen aiwatar da ayyuka, da juyawa tsakanin wani aiki zuwa
wani. Masarrafar gudanarwar kwamfuta mai tsarin gudanarwa daya ce ta dace
da tsarin tunanin dan adam, musamman wajen hada ayyuka guda biyu a lokaci guda
– watau Multitasking.
Don haka Malaman kimiyya a fannin kwakwalwa da tunanin dan adam sun
nuna cewa kwakwlwar dan adam ba za ta iya daukan ayyuka fiye da biyu ba a
lokaci guda. Domin tsarin gudanarwarsu ba zai taba samuwa yadda ake so
ba.Samuwar hakan ga dan adam kuwa ba aibu bane ko kadan. Domin
kasancewarsa a yadda yake haka ne zai bashi kariya wajen yin abubuwa a cikin
tsari da kamala. Domin kwakwalwarsa wata irin muhalli ce da ba ta son
cakude-cakuden abubuwa a lokaci daya, muddin ana son ta gudanar da su cikin
tsari da inganci da kuma kamala. Malaman Kimiyya sun nuna cewa idan aka
tilasta wa kwakwalwar dan adam yin abubuwa da yawa a lokaci daya, hakan zai sa
ta rika tafka kurakurai wajen bayar da hukunci, sannan da tilasta mata juya
akala daga aikin da take yi zuwa wani, ba tare da tsari ba. A karshe ma dai,
wani sakamakon bincike da wata Jami'a ta yi makonni biyu da suka gabata ya nuna
cewa, yawan cakuda wa kwakwalwa ayyuka fiye da biyu a lokaci daya na daga cikin
dalilan da ke sa mutum ya samu kiba mara misali ko yayi teba (Obesity).
Dangane da bayanan da suka gabata, a tabbatace yake cewa yin
abubuwa fiye da biyu masu bukatar aiwatarwa a lokaci daya, ba abu bane mai yiwuwa. Don
haka Rago ya yi wa kansa adalci, lokacin da aka bukaci ya sha fura sannan ya
kama hanyar gona, sai ya ce: "Kun raba mini hankali."
Source:
http://kimiyyah.blogspot.com/2011/11/tsarin-gudanarwar-kwakwalwar-dan-adam.html
0 Comments
Post a Comment