YABO GUN JALLA DAI DAINA - Wakar Wazirin Gwwndu



Yabo gun Jalla daidai na
Garan kuma wajibina na
Na jin kai nai da yan nuna
Garan ya amshi roko na

Tutur! Na zam shukura
Ga sarkin nan da naiyi kira
Da sunayensa naiyi bara
Zuwa ga biyan bukatuna

Da farko duk abinda ni kai
Da fari dai salati ni kai
Ga Annabi duk abinda ni kai
Da shi nika fara wake na

Sahabbai nai da Alu duka
Gama sun taimake shi duka
Ina ko daulaminsu duka
Da aikina da horo na

Abokina taho ka jiya
Ina rokonka kar ka kiya
Ka samu guri guda ka tsaya
Idan ka amshi roko na

Tsaya gun Jalla dai ka fake
Da imaninka kar ka fake
Ka bishi ka togi inda shike
Mu dogara nan masoyi na

Biyar Allahu ta wajaba
Sana'a ta mafi riba
Tutur! Batu na bai da tambaba
Tsaya in baka shaiduna

Ruwa bana sun ka kai ga wuya
Har na rasa inda zani tsaya
Balle juyi, balle tafiya
Ganin am fara zunde na

Rawata an suke ta duka
Gama an dungushe ni haka
Ganin ta kai ni ag ga haka
Dada nir raina wayo na

Dada sai nik kirai Ahadun
Guda, wannan da as-Samadun
Da nim matsu ni nufai da gudun
Gama shi am maceci na

Da nat tasamma inda shike
Cikin huruminsa ni iske
Aminci nan gare shi shike
Dada nid debe tsoro na

Da dai nig gane Sarkina
Da ba a bida garai shi hana
Ga kofofinsa niz zauna
Dada ni buda baki na

Dana roka da ya bani
Dani dauko ga Qur'ani
Ashe ma anyi min izini
In tai in kara koke na

Da najji hakanga nish shirya
Bido Zababbiya ka jiya
Cikinta kana ganin hanya
Da zam bi ta zam mahorina

Taho sa hankali ka kula
Kabar gajiya, kabar shagala
Tutur! mu tsare yabon Allah
Cikin zarafin zamowa na

La'in mun zo ga Qur'ani
Bisa horonka don ka sani
Ina tsaya ran dare da wuni
Ina shukuri da Bege na

Tabara yabonka jalli na
Gareni abin tsimina na
Sahihin maganina na
Da shi nika warke rauni na

Da lotto duk yabonka ni kai
Dana matsu duk kiranka ni kai
Bida bisa agajinka ni kai
Ka warwatse aduwai na

Kana nan inda nis sanka
Tutur! Ka amsa sunanka
Mujibun kow kireka haka
Kana ji baka yin kwana

Da kyau nas soka nab bika
Da kowa baiyi ma shirka
Ilahul Arshi baicinka
Wane ka biyan bukatu na

Ina wani banda kai Rabbu
Da ba a bida shice babu
Ina wani mai kade aibu
Gareni shi karbi rokona

Ku kawo wanda kun ka sani
Da komi za ayi shi sani
Da an roke shi bashi hani
Fada mini shi, ka ban suna

Kace Allahu sarki na
Wani nai dug gazajje na
Abi nai duk kadan dai na
Ina shika jure roko na

Bida ga waninka mik kai ni
Dadai duk wanda yas sanni
Cikin ni'imarka yag ganni
Kana da kula da raino na

Ka cetan kar a kaushe ni
Ga duk hanyar da shaidani
Rajimi kar shi rudeni
Shi hau kan yan dibaru na

Ta'ala kai da ka hora
Mu zan koko mu zan ta bara
Gareka mu zam bidan Nasara
Dashi ni kayo umurni na

Ta'ala Jallah mai iko
Ina nan dai ina dako
Ina ta kiranka kullum ko
Ina kuma kara kwazo na

Da farin na kiraye ka
Da sauri nig ga jinkanka
Ina gode ma baiwarka
Dashi ni ka rera wake na

Ta'ala bani fasa bara
Tutur! Ni ke duk cikin zakara
Ginarka gareka ga sutura
Wadarka, ka kore bakakina

Bukatu na matso ni su kai
Dana matsu ko kiranka ni kai
Tutur! Sonka bani ni kai
Ina nika kama bakina

Bukatu gasu sun gilma
Ilahi gani na soma
Kiran nan wanda nif fara
Da farko nigga dace na

Da farin gafara zambu
Nike roko wurin Rabbu
Da aikina nayin aibu
Da son raina da wayo na

Ka hori ga zuciya ta tsaya
Bida ga waninka duk ta kiya
Balle inyo haraminya
Garai in banna baki na

Isheni ga duk abinda nik kai
Biya min duk bukin da ni kai
Gama kasan nufar da ni kai
Ya Rabbi ka amshi rokona